Abigael Kendi, ƴar shekara 19 ce a Kenya da aka haife ta dubura biyu, farji biyu, mafitsara biyu da kuma ƙoda guda ɗaya.
Ta bayyana yadda take rayuwa cikin wannan yanayi da kuma yadda yanayin halittarta ta fara canzawa a lokacin.
Tace hoto - Fatima Othman
A tarihin Gasar Kofin Duniya, akwai wasu wasanni da ba a mantawa da su.
Amma a wannan gasa ta 2026, za a kafa wani babban tarihi mai matuƙar muhimmanci tsakanin Aljeriya da Japan.
Karin bayani - https://t.co/fe6N5H8gpy
Kasancewar ƙasashe kamar Najeriya da Nijar da Kamaru ba su samu gurbi a Gasar Kofin Duniya ba, mutane da yawa na goyon bayan ƙasashen da gwanayensu ke taka wa leda.
Iran ta ce ta rufe mashigar Hormuz bayan zargin Amurka da Isra'ila da saɓa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a makon nan.
Sojojin Iran sun ce sun ɗauki matakin ne bayan sun zargi Isra'ila da ci gaba da kai hare-hare a Lebanon.
Bayan shafe shekaru hudu, al’ummar jihar Ekiti da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun koma rumfunan zabe domin zaɓen sabon gwamnan da zai jagorance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Ƙarin bayani - https://t.co/aRwIUlHtjg
Iran ta ce kuɗaɗen da za a saki za su kasance an tanade su ne domin bunƙasa manyan ayyukan more rayuwa kamar gyara hanyoyi, tituna da filayen jiragen sama domin inganta rayuwar Iraniyawa.
Ƙarin bayani - https://t.co/0cETRzQcAy
A cewarsa, amincewar Iran da kuma matakin da ya ɗauka sun taimaka matuƙa wajen kaucewa abubuwan da za su iya jefa tattalin arzikin duniya cikin hadari.
Ƙarin bayani - https://t.co/im028iVuBa
Tsohuwar ministar albarkatun mai ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, wadda wata kotu ta wanke daga zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi mata ta ɗaura wa gwamnatin Najeriya alhakin yanayin da ta shiga.
🎥 - Fatima Othman
Me za a kira mutumin da kuɗinsa suka kai dala tiriliyan ɗaya?
A baya-bayan nan ne Elon Musk ya samu babban tagomashi, yayin da arziƙinsa ya zarta dala tiriliyan ɗaya, wato ya ninka Aliko Dangote kuɗi sau 33.
🎥 - Fatima Othman
Gwamnatin Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai bai wa ƴan jarida damar yin rakiya ga dakarun sojin ƙasar a lokacin da za su ƙaddamar da wasu farmaki na musamman.
Ƙarin bayani - https://t.co/gAefUF4kaf
Wata mata ta zargi ɗan wasan bayan Paris St-Germain da yi mata fyaɗe a gidansa da ke babban birnin Faransa a shekarar 2023, lokacin tana da shekara 24.
Karin bayani - https://t.co/n95Vy0QWJr
Ga yadda mutane suka garzaya don ceto wasu da hatsarin jirgin sama ya rutsa da su.
Kusan mutum 12 ne suka yi ƙoƙarin ceto mutanen da jirginsu ya faɗi a wani titi a Texas.