Manzon Allah SAW ya kasance yana yawaita wannan addu'ar:
"Ya Allah ka rabani da talauci, ka rabani da karancin arziki, ka rabani da kaskanci da wulakanci.."
Mu yawaita yi muma...👌
Duk irin sabanin da kukai dawani kada ka bayyana sirrin da kukai, sabida kacimai mutunci ko makamancin haka..!!!
Cikakken Yarintane dakuma Rauni da Rashin Aminci, kuyi chatting da Mutum ta sirri dazaran kuma kun samu sabani seka dauko screenshot din Wannan chatting din da kukai ka bayyanawa Duniya, Wannan ya nuna kai ba amintacce bane kuma bai kamata kowa ya aminta dakaiba.
Dan Wani yataba biyoka DM dinka ya nemi taimako ko kuma yanemi wata alfarma wannan ba Gazawa bane rayuwa ce tasashi haka dakuma jarrabawa, idan da Allah yaga dama kai zaisa amatsayin Wanda zaibi Wani DM yanemi alfarman.
Duk dai wasu sunmai da Abun Sana'a, Amma dayawa Babu yadda zasuyine sabida jarrabawan rayuwa dakuma halin yau da kullun. Idan har ka taimaki mutum Dan Allah kuma babu Wani mummunan nufi koko azuciyanka, to kada kai fatan Ranan da Allah zaisa katai maki wani, dagabaya dan kun samu sabani ko kunyi fada dashi kadauko wani screenshot din Abunda kukai a sirri.
Samun sabani ba illa bane, Amma bayyana sirrin wani da Niyyan cin mutunci ko dan huce takaici illa ne, domin yana rage Aminci dakuma zubar da kima, duk Yadda nake ganinka da kima wlh dazarar naga kunsamu sabani da wani, sainaga kadauko Wani screenshot na sirri kanunawa Duniya kwata kwata sai inji karage kima aguna.
Kayi taimako Dan Allah, kamanta da kayi taimakon, inma kaga dama dazaran kungama chatting dinku na sirrin sai kai maza ka goge duka maganganun da kukai.
Kafin Kazo Kana Tallan Kano First, Ya Kamata ka Tuna da Lahira First, Yanxu Dan ALLAH Ranar Lahira wacce hujja Abba yake da ita a wajan Ubangiji na wajan dauko Tallan Tinubu 😭😢. Ba za a ci Amanar Arewa dani ba, Saboda haka Lahira First 💪. Duk cikin Nasiha ce, Muji Tsoron Allah
KA'IDOJI 20 NA RAGE DAMUWA:
1. Ka daina shiga harkan mutanen da babu ruwanka, kuma ka mai da hankali kan al’amuranka.
2. Ka rage magana, ka yawaita sauraro.
3. Ka daina kwatanta rayuwarka da ta wasu.
4. Ka zama mai yafiya, kada ka riƙe ƙiyayya a zuciyarka.
5. Ka girmama iyakokin da mutane suka sanya
6. Ka guji gulma da kuma maganganun banza.
7. Ka koyi rabuwa da mutane masu guba a rayuwarka.
8. Ka yi murna da nasarar wasu.
9. Ka koyi sarrafa fushinka.
10. ka bayar ba tare da tsammanin sakamako a kan ka ba.
11. Ka zama mai wadatar zuci da abin da ka mallaka.
12. Ka cika alkawuranka.
13. Ka koyi zama kai kaɗai ba tare da jin kadaici ba.
14. Ka yi haƙuri a cikin zirga-zirga da kuma al'amuran rayuwa.
15. Ka nisanci rigingimu da maganganu marasa amfani.
16. Kada ka katse maganar wani lokacin da yake magana.
17. Ka taimaka ba tare da sanar da duniya ba.
18. Ka yi magana da nutsuwa koda fushi ya kama ka.
19. Ka yi jinkiri wajen yanke hukunci a kan wasu.
20. Ka so kanka, amma kada ka zama mai son kai.
A cikin wannan duniya mai cike da hayaniya da kalubale, koyon rayuwa cikin salama da kanka da kuma mutane kyauta ce mai ƙarfi. Waɗannan ƙananan ɗabi’u za su taimaka maka ka gina kyakkyawar dangantaka, rage damuwa, da kuma samun farin ciki a rayuwarka ta yau da kullum in sha Allah.
Allah Yadda Ka Shayar Damu Ni'imomimka. Ka Wadata Mu. Baka Barmu Cikin Talauci Ko Rashin Lafiya Ba.
Allah Muna Roƙonka Albarkar Wannan Watan Na Ramadan Ka Ninka Mana Duk Wata Ni'ima Ta Rayuwar Duniya Da Lahira.