🚨🦅 Raphael Onyedika zai koma Eintracht Frankfurt, an kammala komai!
An cimma yarjejeniya kan ɗan wasan Najeriya domin ya koma Eintracht Frankfurt.
Eintracht za ta biya €10m ga Club Brugge, yayin da Onyedika ya zaɓi Frankfurt duk da tayin da ya samu daga ƙungiyoyin Saudi. 🇳🇬
Atlético Madrid ta fara tattaunawa domin ƙoƙarin ɗaukar Cristian "Cuti" Romero daga Tottenham. Kocin Atlético, Diego Simeone "Cholo" yana matuƙar son ɗan wasan kuma yana ganin Romero shi ne cikakken ɗan bayan tsakiya da ya dace da tsarin ƙungiyar.
⏳ Har yanzu babu cikakkiyar yarjejeniya tsakanin Real Madrid da RB Leipzig kan cinikin Yan Diomande, duk da sabbin tattaunawar da aka yi yau. Dukkan ɓangarorin da abin ya shafa sun tabbatar da hakan
Diomande yayi atisaye ƙarkashin kulawa musamman a Leipzig yau
An cimma yarjejeniya ta farko kan kwantiragi har zuwa shekarar 2028 tsakanin Geronimo Rulli da Manchester City.
Enzo Maresca ne ya zaɓi Rulli domin ya maye gurbin James Trafford, kuma yanzu Manchester City na tattaunawa da Olympique Marseille domin cimma yarjejeniyar cinikin sa
César Palacios na daf da komawa Fulham daga Real Madrid.
Matashin ɗan wasan na Sifaniya ya riga ya nuna amincewarsa da komawa Fulham, yayin da koci Álvaro Arbeloa ke taka muhimmiyar rawa a tattaunawar da ake yi domin kammala cinikin.
#FFC
César Palacios na daf da komawa Fulham daga Real Madrid.
Matashin ɗan wasan na Sifaniya ya riga ya nuna amincewarsa da komawa Fulham, yayin da koci Álvaro Arbeloa ke taka muhimmiyar rawa a tattaunawar da ake yi domin kammala cinikin.
#FFC
🚨 An cire Kristjan Asllani daga tawagar Inter da za ta yi rangadin tunkarar sabuwar kakar wasa, domin kulob din ya ɗauke shi a matsayin wanda ba ya cikin shirinsa.
A halin yanzu ana aiki kan sayar da ɗan wasan tsakiya.
🚨⚪️⚫️ Juventus na ci gaba da tattaunawa kai tsaye da wakilan Kerem Alajbegović da mahaifinsa don kammala cinikin
Kungiyar tana da kwarin gwiwar cimma matsaya ba da jimawa ba, yayin da ake jiran amincewa ta ƙarshe kan kuɗin kwamishina da sauran kuɗaɗen da ke tattare da cinikin.
🔜 An kammala ciniki, kuma an tabbatar! John Stones zai koma Inter a matsayin ɗan wasa kyauta.
Ya amince da kwantiragi har zuwa 2028, inda zai riƙa karɓar albashin €4.5m a shekara. Ana sa ran yau ne zai yi gwajin lafiya tare da sanya hannu kan kwantiragin.
🚨❌ Maganar cewa Gleison Bremer zai koma FC Bayern Munich ƙarya ce.
Kulob ɗin Jamus ɗin bai taɓa saka shi cikin jerin 'yan wasan da yake son ɗauka ba, kuma Bayern ta musanta duk wani shiri na sayen sabon mai tsaron baya.
⚪️⚫️🔥 Komai ya kusa kammala: Juventus FC ta tsara komai domin kammala ɗaukar Kerem Alajbegović.
An riga an shirya takardun yarjejeniyar, kuma ana jiran amincewa ta ƙarshe kan kuɗin kwamishina domin a kammala cinikin a yau.
🚨 Como a shirye take ta miƙa tayin €22m ga Bologna domin ɗaukar Jhon Lucumí.
Mai tsaron bayan a shirye yake ya bar Bologna a wannan kakar wasan, kuma ana ci gaba da tattaunawa kan cinikin. 🇮🇹✍️
🚨✅ Ta Kammala! Randal Kolo Muani ya koma Juventus daga PSG a matsayin aro kan kuɗin €4m.
Yarjejeniyar tilas Juventus ta saya kan €34m tare da ƙarin €12m don gurbin buga gasar Turai. Ya rattaba hannu kan kwantiragi har 2031, inda zai riƙa karɓar €5m a shekara. ⚪️⚫️✍️
��🔴 Gerard Martín kan sabbin 'yan wasan da Real Madrid ke saya:
"Suna da damar su sayi duk wanda suke so, amma hakan bai dame ni ba."
"Mu dai hankalinmu yana kan ƙungiyarmu ne kawai. Za mu ci gaba da fafatawa kamar yadda muka saba yi a kowace shekara." 💪
��🔴🏆 Karim Adeyemi: "Babban burina shi ne lashe gasar zakarun turai."
"Na taɓa zuwa kusa da cimma hakan, amma abin takaici mun sha kashi. Har yanzu wannan ne babban burina, kuma kullum ina aiki domin in cimma shi." 💙🏆
❤️🩹🇪🇸 Fermín López: "Wannan ita ce kakar wasa mafi muni a rayuwata." Dan wasan ya bayyana yadda rauni ya hana shi buga wa Spain, yana mai cewa hakan ya yi masa zafi sosai. Ya kuma ce yanzu ya warke kuma ya shirya dawowa ya ci gaba daga inda ya tsaya a kakar da ta wuce. 🇪🇸💪
🚨 Ayyoub Bouaddi na daf da kammala komawa Manchester City daga Lille.
An riga an cimma yarjejeniya kan sharuɗɗan kwantiragi har 2031, kuma ana sa ran za a kammala cinikin nan ba da jimawa ba. 🔵✍️
🚨🇪🇸 Fermín López: "Kowa yana son lashe Champions League, kuma cikin shekaru biyu da suka wuce mun kusa cimma hakan."
"Ina ganin wannan shekarar na iya zama tamu. Muna shirin fafatawa domin lashe dukkan kofunan da za mu buga, musamman ma Champions League." 🏆💙❤️
🚨🇹🇷 Makomar Rafael Leão har yanzu ba ta kammala ba, yayin da Fenerbahçe da Galatasaray duka suke son ɗaukar ɗan wasan.
Shugaban AC Milan, Gerry Cardinale, ya dage cewa kulob ɗin ba zai saurari kowace tayi da ta gaza €50m ba, kuma babu batun amincewa da aro a matakin farko.