NAMIJI ZAI IYA KAIWA KARFE 2:00 WANIMA 3:00 NA DARE IDONSA BIYU... !!!
Sannan ya tashi karfe 5:30 na Asuban ya fita Sallahn Asuba, karfe 7:00 yafita nema.
*Alhali ana bin sa Bashi.
*Aljihunsa Babu ko sisi.
*Babu mai taimakonsa sai Shi kadai.
Amma duk da haka, zaka ga yana murmushi, yana da Yakini mai karfi a cikin zuciyarsa cewa:
"Watarana komai zai yi daidai, kuma watarana sai labari."
Wannan sam ba hauka bane...
WANNAN SHINE AKE KIRA NAMIJI.
Duk tsananin da kake ciki, kada ka fidda rai. Gobe ta Allah ce.