Top Tweets for #shugaba
Koriya ta Arewa (North Korea) ta taɓa yin odar motocin Volvo sedan guda dubu daya (1,000) daga Sweden, saboda amfanin manyan jami'an ta, amma ta ƙi biyan kuɗin, wannan ita ce almundaha mafi girma a fannin siyar da motoci a Tarihi.
A shekarar 1974, Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Kim Il Sung yasa akayi odar manyan motocin Volvo 144 sedan guda 1,000 tare da kayan gyaransu. Lokacin da jirgin ruwa ya sauke dukkan motoci 1,000 a birnin Pyongyang, kasar ta taki biyan kuɗin motocin, fiye da shekaru 50, gwamnatin Sweden ta na aikawa sau biyu a kowace shekara don a tunatar da gwamnatin Pyongyang kan biyan kuɗin wanda kimarsu yanzu ya kai kusan dala miliyan 300, amma shiru kakeji. Yayin da waɗannan motocin Volvo na shekarun 1970 a ke iya ganin su har yau akan tituna a babban birnin kasar.

Tambaya:
A ganinku, mene ne babban abin da matasa suke bukata a yau domin su samu ci gaba: Ilimi, sana'a, tarbiyya ko shugabanci nagari?
Let's have a meaningful conversation.
Shugaba Tinubu nada cikin manyan Masoyan Arewa. ya Kamata Arewa tasan haka, kuma ta tuna haka. Inji Kashim Shettima.
@Waspapping_
ATIKU ABUBAKAR yayi Martani ga Shugaba Tinubu. Tinubu ne Masar, shiya maida Nigeria Masar shiyasa akeso a Gudu abar kasar.
@ADCVanguard_
Shugaba Tinubu ya sake Nuna Kwarewar shi a Jihar Zamfara, wajen dawo da Yan Majlisu 8 APC. Darasi ga Jam'iyyun Adawa.
@Waspapping_ @Minikothe3rd @The_Umdazz
MATSAYAR ƳAN TMG A MA'AUNIN FALSAFAR LOGIC✍️
"Idan Atiku bai cika alƙawuran da yayi mana ba, za mu kawar da shi mu kawo wani" - Ƴan TMG
TAMBAYA
1. Dama baku da yaƙinin Atiku ya cancanta?
2. Ana sauke shugaba a Najeriya cikin ruwan sanyi?
3. Me yasa kuka yiwa Buhari uzuri amma kuka kasa yiwa Asiwaju?
4. Anya ba ɓangaranci ko ƙabilanci ne matsalar ku ba?
5. Idan Atiku ya ba ku muƙami shin za ku yaƙe shi idan ya gaza ko?
6. Tun da mun gane iyayen gidan ƴansiyasar Najeriya duk ɗaya ne (turawa), me yasa kuke tunanin sauyi?
7. Bisa la'akari da matsalar tsaro ce kan gaba a Arewa, me yasa babu wani tsari da Atiku yake dashi wajen magance zubar da jinin bayin Allah?
NB: Muna son tattaunawar ilmi ba zage zage ba.
@TeeVee76 If I were to give them titles
Shugabush would be the "Original Legendary"
The Shugafam would be the "x" Edition Legendaries, so for example Shugabass is "Bass Edition"
bbli$zard would be the "Spitfire Legendary"
Su fa wasu sunce ba'a fito na fito da shugaba
Breaking 💯
If you feel overwhelmed then resign immediately.......
Monsignor (professor) Obiora Francis Ike.
He is a Roman Catholic priest, a scholar and human rights activist.
Professor Obiora is the founder of the Switzerland based Catholic institute for development justice and peace
https://t.co/9guVyLSLHg
Ba'a fito na fito da shugaba. A sirri a ke masa gyra
When the country is bleeding, there is no room for sugarcoating, mincing words, or decorum. You say things as they are. This is what we expected of our clerical class. And it's not a simple expectation, it is an obligation, a duty.
Bayan Surutan Shugaban Kasar Burkina Faso.
- Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo.
-@el_uthmaan
SANARWAR FADAR SHUGABAN ƘASA
Shugaba Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Kan Ceto Ɗalibai da Malamai da Aka Yi Garkuwa da Su a Orire, Ya Yaba wa Jami'an Tsaro
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matuƙar farin cikinsa kan nasarar da jami'an tsaro suka samu wajen ceto ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su daga yankin Orire a Ogbomoso, Jihar Oyo.
Shugaban ya yabawa jajircewar jami'an tsaro, musamman sojoji, Hukumar Tsaro ta DSS da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, saboda aikin da suka yi ba dare ba rana cikin kwanaki 56 domin tabbatar da ceto waɗanda aka sace ba tare da wata illa ta samu ba. Haka kuma, ya yabawa jami'an kan kama mutum takwas daga cikin masu garkuwa da mutanen tare da kashe wasu daga cikinsu.
Shugaba Tinubu ya bayyana alhininsa kan irin wahala da damuwar da ɗaliban, malamansu, iyalansu da kuma ’yan Najeriya baki ɗaya suka sha tun bayan faruwar wannan lamari.
Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Oyo bisa haɗin kai da ta ba Gwamnatin Tarayya wajen gudanar da aikin ceton, tare da umartar gwamnatin jihar da ta ƙara ƙarfafa tsaro a makarantun jihar.
Shugaban ya ce:
> "Ina matuƙar farin ciki cewa jami'an tsaronmu sun yi nasarar ceto ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su daga Orire da ke Ogbomoso a Jihar Oyo, bayan wani samame da sojoji, ’yan sanda da jami'an leƙen asiri suka gudanar, wanda ya kai ga kashe wasu daga cikin ’yan ta'addar da suka aikata wannan mummunan laifi tare da kama mutum takwas daga cikinsu."
> "Wannan nasarar ta kawo ƙarshen fiye da kwanaki 50 na fargaba da tashin hankali, tare da kawo sauƙi ga al’ummar Najeriya baki ɗaya, musamman iyalan waɗanda abin ya shafa. A madadin ƙasa, ina miƙa godiyata ga jami'ai da dakarun rundunar soji, hukumomin leƙen asiri da Rundunar ’Yan Sanda saboda ceto ɗaliban da malamansu cikin koshin lafiya."
> "Gwamnatina za ta tabbatar an yi adalci ga waɗannan ɗalibai da malamansu, da kuma iyalan Mista Oyedokun, wanda ’yan ta'addar suka kashe cikin mugunta."
> "Ina kuma yabawa Gwamnatin Jihar Oyo saboda haɗin kan da ta ba mu wajen kawo ƙarshen wannan mummunan lamari cikin nasara."
Shugaba Tinubu ya kuma umarci hukumomin agaji na gaggawa da su yi aiki tare da Gwamnatin Jihar Oyo domin samar wa ɗaliban da malamansu dukkan kulawar lafiya da tallafin da suke buƙata.
Bayo Onanuga
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru
10 ga Yuli, 2026

Gwamna Bala Mohammed ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da malamai wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Bauchi, yayin da ya karɓi shugabannin JIBWIS ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir a Fadar Gwamnati. Ya yaba da gudummawar malamai tare da tabbatar da ci gaba da aiki tare domin ci gaban al'umma.
@shamsudeen_bala @LawalMuazBauchi #Bauchi #JIBWIS

Kotu Ta Yanke Wa Mahaifiyar Kachalla Battujo Hukuncin Shekaru 20 A Gidan Yari Kan Taimaka Wa 'Yan Ta'adda
Wata kotu mai hurumin sauraron laifuka ta yanke wa mahaifiyar fitaccen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Battujo, hukuncin shekaru 20 a gidan yari bayan samunta da laifin tallafa wa ayyukan ta'addanci.
An same ta da laifin tura kuɗaɗe da kuma bayar da bayanan sirri da suka taimaka wa ɗanta da sauran masu aikata laifukan ta'addanci wajen gudanar da ayyukansu. Bayan nazarin hujjoji da shaidu da aka gabatar a gaban kotu, alkalin ya tabbatar da cewa an gamsar da kotun kan zarge-zargen da ake mata.
Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ci gaba da ƙara matsa kaimi wajen dakile hanyoyin tallafi da goyon bayan da ke bai wa kungiyoyin masu aikata laifuka damar ci gaba da ayyukansu.
Masana harkokin shari'a na kallon hukuncin a matsayin wani muhimmin mataki wajen tabbatar da cewa duk wanda aka samu yana taimakawa masu aikata laifuka, kai tsaye ko a kaikaice, zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Shugaban cin City Boy Movement na Kaduna. Sun halarci ziyarar gani da ito zuwa HQ din CBM.
@CBMKadunaState @CityBoyMedia @_hafsat_paki @realYangaB @sirr_fk
ABIN TAMBAYA: WAYE AINIHIN “YARO” A SIYASAR BAUCHI?
Abin mamaki ne yadda wasu ke cewa “Yaro ba zai yi Gwamna ba”, alhali ana cewa Sen Shehu Buba Umar da Hon. Dr. Yakubu Adamu sun yi karatu tare ko kuma aji ɗaya.
Idan Dr. Yakubu Adamu yana da shekaru 46, Sanata Shehu Buba Umar yana da 48, sannan honourable Nura Manu soro ma yana cikin irin wannan rukuni na gogaggun masu neman shugabanci, to wa ake kira “yaro” a cikinsu?
A zahiri, siyasa ba ta ta’allaka da shekaru kaɗai ba. Tarihi ya nuna shugabanni da dama sun jagoranci jihohi tun suna ƙasa da waɗannan shekarun, ciki har da Ahmadu Adamu Mu'azu.
Saboda haka, abin da ya kamata jama’a su duba shi ne cancanta, ilimi, ƙwarewa da hangen nesa, ba kiraye-kirayen siyasa da ba su da hujja ba.
Daga ƙarshe, ina kira ga magoya bayan Dr. Yakubu Adamu PhD da su yi watsi da irin waɗannan kalamai marasa amfani, su mayar da hankali wajen yaɗa alkhairi, kyawawan manufofi da hangen nesansa na ci gaban Jihar Bauchi.
Muna da yaƙinin cewa idan ya samu damar jagoranci, zai kawo ci gaba mai ma’ana, musamman ga mata, matasa da sauran al’ummar jihar baki ɗaya. Siyasa ta gari tana ginuwa ne a kan hujja, cancanta da kyakkyawan tsari, ba a kan zage-zage ko lakabi ba.
@shamsudeen_bala

Na koyi wani abu da ya girgiza zuciyata. 💔
Wata budurwa mai shekara 23 kacal, cike da burika da mafarkai, ta fada hannun ‘yan bindiga. Sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 50. Iyalanta sun roka, sun yi kuka, sun nemi rangwame, amma suka ki rage ko sisi.
Tsawon makonni biyu mahaifinta ya yi gwagwarmaya kamar zaki. Ya ci bashi, ya sayar da kadarori, ya tattara komai har ya samu miliyan 50 din. Da ya kira su domin jin muryar diyarsa kafin ya biya kudin, aka ba ta waya.
Amma maimakon ta roki a cece ta, sai ta ce:
“Kada ku biya kudin. Idan suka sake ni, zan kashe kaina.”
Dalili kuwa shi ne, tsawon kwanaki 14 suna cin zarafinta da fyade ba kakkautawa, suna wulakanta rayuwarta da mutuncinta.
Da ‘yan bindigar suka ji abin da ta fada, sai suka harbe ta. Daga baya kuma suka aika wa iyalanta bidiyo da hotunan lokacin da aka kashe ta.
Ba mutuwa ta yi ba. An kashe ta ne bayan an azabtar da ita ta hanyar da babu wani dan Adam da ya cancanci fuskanta.
Yau wani yana ce min in goyi bayan gwamnati.
Wallahi zuciyata tana ciwo.
Wannan ya wuce siyasa. Wannan magana ce ta rayukan mutane. Magana ce ta iyaye da suka rasa ‘ya’yansu, da iyalan da suke tara kudin fansa amma a karshe su karbi gawa.
Mu ba wai muna neman shugaba ne kawai ba. Muna rokon a ceci rayukanmu.
Idan irin wannan labari bai sa ka nemi sauyi ba, to lallai akwai matsala.
Kasarmu tana zubar da jini, kuma lokaci ya yi da za mu farka.
#Copied

🚨🚨 LABARII MAI DADI: Dan wasa Dumfries ya amince zai koma kungiyar Real Madrid, kuma shugaban kungiyar Florentino Perez zai kammala sayen dan wasan bayan an gama zabuka,
kamar yadda jaridar OKDiario ta tabbatar.
• Real Madrid ta gano wanda zai maye gurbin Carvajal
#Amk

-Dafa Idan Ka Hada Irin Wannan Kayan Kallon A Dakinka A Unguwarku Kaine Shugaban Kasa.

SHUGABA TINUBU YA BA DA TABBACIN CETO WAƊANDA AKA SACE A JIHAR OYO, YA KUMA YI ALLAH-WADARAI DA RAHOTON KISAN MALAMIN DA AKA YI GARKUWA DA SHI
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadarai da rahoton kisan ɗaya daga cikin malaman da aka sace daga al’ummar Esiele da ke Jihar Oyo, yayin da ake ci gaba da aikin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
‘Yan bindiga sun kai hari al’ummar Esiele da ke ƙaramar hukumar Oriire a Jihar Oyo a ranar Juma’ar da ta gabata. Sun sace ma’aikata, ɗalibai da yara na makarantar Community Grammar School, Baptist Nursery and Primary School da kuma L.A. Primary School.
Jami’an tsaro na aiki dare da rana domin ceto waɗanda aka sace tare da kamo ‘yan bindigar da masu haɗin gwiwarsu a cikin al’umma.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, da gwamnati da al’ummar jihar bisa wannan mummunan lamari, tare da ba su tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta haɗa kai da gwamnatin jihar domin ceto waɗanda aka sace.
“Na yi matuƙar baƙin ciki da rahoton kisan ɗaya daga cikin malaman da ‘yan bindigar da suka kai hari al’ummar suka sace. Ina jajanta wa Gwamna Seyi Makinde kuma ina yaba matakan da ya ɗauka kan lamarin. Ina kuma jajanta wa iyalan waɗanda aka sace.
“Gwamnatin Tarayya na aiki tare da gwamnatin Jihar Oyo domin ceto dukkan waɗanda aka sace. Ina yaba wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da Kwamishinonin ‘Yan Sanda na Jihohin Oyo da Kwara bisa gaggawar shiga tsakani da kuma tura tawagar musamman ta dabarun yaƙi da kuma tawagar tattara bayanan sirri (IRT) domin ceto waɗanda aka sace.
“Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, bisa umarnina, shi da kansa yake jagorantar wannan aiki na zamani da ake amfani da fasaha wajen gudanarwa. Muna sa ran samun gagarumar nasara nan ba da jimawa ba. Za a kamo ‘yan bindigar da duk masu taimaka musu a cikin gida kuma a hukunta su bisa doka.
“Yawaitar sace mutane na ƙara nuna muhimmancin kafa ‘yan sandan jihohi domin kula da wasu yankuna da ba sa samun isasshen tsaro. Ya kamata Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta gaggauta kafa dokar samar da ‘yan sandan jihohi,” in ji Shugaban ƙasar.
Bayo Onanuga
Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman
(Kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare)
18 ga Mayu, 2026

BREAKING:
City Boy Movement Kaduna Appoints New State Officers, Mobilises for Tinubu, Uba Sani’s 2027 Re-election
Kaduna, Nigeria – The Kaduna State chapter of the City Boy Movement (CBM), a leading grassroots political support platform for President Bola Ahmed Tinubu, has approved the appointment of new state officers with immediate effect as part of strategic efforts to strengthen its operational structure ahead of the 2027 general elections.
The announcement was contained in an official statement made available to newsmen and jointly endorsed by the Kaduna State Director of the movement, Hon. Gambo Ibrahim Gujungu, and the State Coordinator, Comrade Ibrahim Musa.
According to the statement, the appointments are part of ongoing restructuring and expansion aimed at deepening political mobilization, grassroots engagement, and inclusive participation across Kaduna State.
Speaking on the development, Hon. Gambo Ibrahim Gujungu charged the newly appointed state executives to justify the confidence reposed in them by working tirelessly to consolidate the achievements of President Bola Ahmed Tinubu and Governor Uba Sani while ensuring their overwhelming re-election victory in 2027.
He said the movement remains committed to building a broad-based political structure that accommodates all demographics, faith communities, students, business stakeholders, support groups, and vulnerable citizens.
The newly approved officers are:
- Engr. Dauda Mbaya John – Head, Christian Affairs
- Hon. Jessy Ajeson Luka – Secretary, Christian Affairs
- Hon. Sadiqa Isiyaka Rabiu – State Welfare Officer
- Hon. Auwal Musa Shugaba – Head, Security and Safety
- Hon. Abba Nuhu Bashir – Deputy Director, Strategy and Implementation
- Hon. Auwal Shuaibu – State Social Events Coordinator
- Hon. Yusuf Badamasi – Director, Community Engagement
- Hon. Mahmud Sadis Buba – Director, Special Needs
- Hon. Muhammad Abubakar – Director, Student Affairs
- Hassan Shuaibu Shuaibu – Director, Logistics and Transportation
- Ahmed Mohammed Zagi – Director, Support Groups
- Ismail Usman Jibril – Head, Islamic Affairs
- Ahmad Idris Usman – Secretary, Islamic Affairs
- Hon. Isiya Anka – Head, Business Community
The statement emphasized that the appointments take immediate effect, urging all members of the movement across the 23 local government areas of Kaduna State to cooperate fully with the new officers in advancing the movement’s objectives.
Political observers see the latest appointments as part of intensified grassroots political realignment ahead of the 2027 electoral cycle, particularly in strengthening support for the Renewed Hope agenda in Kaduna State.

🚨 ABIN AL'AJABI A AZARE 🚨
Rahotanni masu tayar da hankali sun fito daga garin Azare, Jihar Bauchi, inda wasu mutane ake zargi da kafa wata sabuwar gungiya mai ɗauke da akida mai matuƙar ban mamaki da tayar da kura.
A cewar majiyoyi, shugaban wannan gungiya ya yi iƙirarin cewa ya samu wani “wahayi” a mafarki, wanda ya umurce su da wata dabi’a da ta saba da al’ada da addini — inda ake zargin mambobin kungiyar na musayar matansu a tsakanin juna, har ma da shigar da mata marasa aure cikin wannan tsari.
Sun ce manufar hakan, a cewarsu, ita ce ƙara “soyayya da tausayi” a tsakanin su — ra’ayi da ya janyo cece-kuce mai zafi a cikin al’umma.
👉 Abin da ya fi ɗaga hankali shi ne: jami’an tsaro sun riga sun kama mutane 7 da ake zargi da hannu a cikin wannan lamari, kuma ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma yiwuwar akwai karin masu hannu a ciki.
Al’ummar yankin sun nuna matuƙar damuwa tare da kira ga hukumomi da su ɗauki mataki mai tsauri domin kare tarbiyya da mutuncin al’umma.
⚠️ Wannan lamari ya buɗe sabon babi na muhawara a kan yadda ake fassara “yanci” da kuma iyakokin da al’ada da addini suka shimfiɗa.
Me kuke tunani akan wannan? Shin ya kamata a tsaurara hukunci ko a mai da hankali kan wayar da kai?
@bbchausa @DCLHausa
#Azare #Bauchi #LabariMaiZafi #Nigeria
A gaskiya, ya kamata mu jinjina wa Atiku Abubakar game da dabarun da yake bi kwanan nan.
Kowa ya sa rai cewa jam’iyyar ADC za ta tsayar da dan takara daga kudancin kasar a shekarar 2027 don cika wa’adin mulkin kudancin. Sai dai kuma, kusancin da ke kara kulluwa tsakanin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ya canja salon wasan. Wannan kawancen yana karfafa damar Kwankwaso a shekarar 2031, sannan yana dusashe burin Atiku na dogon lokaci.
Bangaren Atiku sun yi kokarin ramawa sun gudanar da taron Ibadan domin neman goyon baya da kuma kokarin tallata shi a matsayin wanda kowa ya amince da shi. Sai dai kuma, Obi ya hango abin da ke zuwa, shi ya sa ya yi hanzari wajen daukar mataki.
A takaice dai Burin shugabancin Atiku ya kara wahala sosai a yanzu.
Yan ADC yanzu duk sun karkata zuwa NDC da kuma tafiyar #OKMovement.

Most Popular Users

Elon Musk 
@elonmusk
240M followers

Barack Obama 
@barackobama
118.6M followers

Cristiano Ronaldo 
@cristiano
114.4M followers

Donald J. Trump 
@realdonaldtrump
111.7M followers

Narendra Modi 
@narendramodi
106.9M followers

Rihanna 
@rihanna
98.6M followers

NASA 
@nasa
92.1M followers

Justin Bieber 
@justinbieber
91.7M followers

KATY PERRY 
@katyperry
89.9M followers

Taylor Swift 
@taylorswift13
83.9M followers

Lady Gaga 
@ladygaga
75.4M followers

Virat Kohli 
@imvkohli
73.3M followers

Kim Kardashian 
@kimkardashian
70.8M followers

YouTube 
@youtube
68.6M followers

Neymar Jr 
@neymarjr
66.3M followers

Bill Gates 
@billgates
65.2M followers

Selena Gomez 
@selenagomez
63M followers

The Ellen Show
@theellenshow
62.1M followers

CNN 
@cnn
61.7M followers

X 
@x
60.6M followers












