Don Allah, don Annabinsa mai girma Gwamna @Kyusufabba a hakura da gina sabbin estates dinnan, ka mayar da hankali kan manya da kananan tituna.
Wallahi Kano ta fi bukatar tituna a kan estates dinnan. Na hadaka da Allah da Annabinsa. 🙏
Labari: Hukumomi a Nigeria sun janye haramcin amfani da shafin sadarwa na Twitter a yau.
Hakan na kunshe cikin takardar da Shugaban Kasa @MBuhari ya rattabawa hannu, ta hannun Shugaban Hukumar Habbaka Kimiyyar Bayanai ta Kasa, @KashifuInuwa.
Yau ne a ke sa ran dawowar shafin. https://t.co/b1agrSDTxD
LABARAI: ASUU Ta Janye Yajin-Aiki.
Biyo bayan doguwar tattaunawa da kudure-kudure tsakanin Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Kasa da Gwamnatin Tarayya, Kungiyar ta janye yajin aikin da ta dauki tsawon wata 9 ta na yi.
Daliban jami'o'i a Najeriya za su koma zaurukan karatun su.
Labarai: Allah ya yiwa Sam Nda Isaiah rasuwa bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Marigayi Sam dai shi ne ya samar da jaridar Leadership kuma tsohon dan takarar Shugaban Kasa a shekarar 2015.
Ya rasu a gidansa da ke Abuja a daren jiya.
John Mahama ya yi watsi da zaɓen Ghana.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a Ghana ƙarƙashin Jam'iyyar NDC, John Dramani Mahama, ya bayyana cewa ba zai karɓi sakamakon zaɓen ƙasar ba, duk da cewa hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shugaba mai ci Nana Akufo-Addo a matsayin wanda ya lashe zaɓen
IS ta ce ita ta sace ma’aikatan Red Cross a Borno.
Ƙungiyar IS da ke da’awar jihadi a duniya ta yi iƙirarin cewa ita ta sace ma’aikatan ƙungiyar agaji ta Red Cross a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Labarai: Gwamnatin Jihar Kano ta sanya hannu a kan wata doka da ta tanadi hukuncin ɗauri a gidan yari, ko kuma tara ga duk iyayen da aka samu da laifin ƙin sanya ƴaƴansu a makarantar boko.
Hakan ya biyo yunkurin gwamnatin na ganin ta kara yawan yara ma su zuwa makaranta a jihar.
Labarai: Jami'ar East Carolina University (ECU), ta yi watsi da batun cewa ta nada Gwamnan Kano, Umar Ganduje, a matsayin Farfesa kuma Malami Mai Ziyara.
A kwanan baya dai an yi ta rade-radin Jami'ar ta Amurka ta karrama Gwamnan da mukamin farfesa, wanda su ka musanta yanzu.
Labarai: Jarumin Kannywood Ibrahim Maishunku ya sha da kyar a hanyar Kaduna zuwa Abuja, lokacin da masu satar mutane su ka kusa kama shi.
Maishunku ya ce ɓarayin sun shafe minti 30 su na ɓarin wuta inda suka kashe mutum 10, kuma su ka yi awon gaba da mutum 15.
Labarai: Rundunar Sojin Najeriya ta fitar da wasu sabbin sunayen ‘yan ta’adda guda 86 da ta ke nema ruwa-a-jallo.
Kadan daga cikin su sun hadar da Abubakar Shekau da wasu daga kwamandojin Bokoharam da ISWAP.
Labarai: Tsohon Shugaban Ghana, JJ Rawlings ya rasu a yau sakamakon cutar Corona.
Ya rasu ya na da shekaru 73. Kuma ya yi mulkin kasar Ghana na tsawon shekaru 10 cif.
Labarai: 'Yan ta'adda su na sanyawa manoma haraji a jihar Zamfara.
A cewar waɗannan manoma, 'yan bindigar su na raba su da kayan amfanin gonakin su na miliyoyin nairori, sannan ba sa cika alkawarin da suka ɗauka na sakin kayan da kuma dakatar da garkuwa da su.
Labarai: Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu a birnin Kaduna, a yau.
Ya rasu ya na da shekaru 84 a duniya, bayan gajeriyar rashin lafiya. Za a yi jana'izarsa da misalin karfe hudu a agogon Najeriya a masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna.
Rahoto: An yi jana'izar fitaccen mafaraucin nan kuma mai kama barayi, Alhaji Ali Kwara a garin Azare a ranar Asabar.
Ya rasu ne a wani asibiti a Abuja ranar Juma'a bayan ya sha fama da rashin lafiya. Manyan mutane daga sassan Najeriya daban-daban ne suka halarci jana'izar ta sa.
Labarai: Sojin Najeriya sun halaka ‘yan Boko Haram kimanin 75, a wani karon-batta da su ka yi.
Fafatawar ta lakume rayuwar zaratan soji guda 3, a tsawon kwanaki 3 da suka dauka su ba-ta-kashi.
Labarai: Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya bayar da umurnin sake gina Masallatai biyu da aka kone a jihar, biyo bayan rikicin kabilanci da ya afku makonnin da su ka wuce.