Karamin Ministan tsaron Najeriya Bello Matawalle ya shirya yan sanda da bindigu sunje sun sace Salim Abubakar Musa (@AM_Saleeeem) a Hotel din dayake zaune a Abuja.
Abin takaici ne ace mutumin da al’umma ke zargin yana da hannu dumu-dumu a ta’addanci yan bindiga, shine Ministan Tsaro har yanzu a Najeriya, Mutumin nan yayi Gwamna amma bai kawo cigaba ba a yankin sa domin inganta tsaro, yau shine Ministan tsaro amma kullum matsalar tsaro kara ta’azzara take a jihar sa ta Zamfara.
Jami’an tsaron Najeriya bazasu iya tracking din Bandits ba amma zasu iya tracking wanda yayi rubutu a social media, wannan zalunci ne, tauye hakkin dan adam ne, nunawa gazawar dimokradiyya ne.
Laifin Salim daya ne; Yayi posting video din tsohon mai taimakawa Matawalle wanda yayi video yabada shaida cewa Matawalle nada alaqa da yan ta’adda su Bello Turji. Menene laifi idan Salim yayi posting video din? Meyasa bazasu je su kama Sheikh Asada ba? Meyasa bazasu je suka ma wanda yayi video ba (Musa Kamarawa).
Saboda haka ire iren wannan zaluncin bazamu laminta ba, mun kwammace duka akama mu ko a kashe mu, amma tabbas wannan azzaluman yan siyasar rubabbu, bazamu barsu su cutar da goben yayan mu ba indai muna numfashi a doron kasa.
#JusticeForSalim #FreeSaleem