One day, we will all stand before Allah and answer not only for what we did, but for what we exposed, what we shared, what we encouraged, and what we took pleasure in spreading may allah forgive us and protect our hearts from enjoying people secret, downfalls, problems or other challenges may allah make us a faithful servant and make us among people in jannah ameen.🙏
2.6 MILLION A KOWANE WATA… DOMIN MARAYU.
Daga bakin:
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (Hafizahullah)
Yanzu ƙaramin breakdown da mukayi jiya…
duk wata, abunda yaran nan za’a
musu dawainiya tsakanin:
— abincin safe
— abincin rana
— abincin yamma
— albashin malamansu
— albashin security
— kula da bangaren girka abinci
— da sauran abubuwan tafiyar da makarantar…
Atakaice, duk wata za’a kashe kusan naira
million biyu da dubu dari shida (2.6M+)
Kuma fa…
ba wai anyi wannan ne don walwala ko nuna isa ba.
Wannan makaranta…
Makarantar marayu ce.
Duk yaron da zaka gani a wajen,
Maraya ne. Mahaifinsa ya rasu.
Ba gwamnati bace ta gina ba.
Ba jama’ar gari suka hada suka gina ba.
An gina ta ne saboda tausayi…
saboda neman yardar Allah…
saboda a ceci rayuwar marayu.
Shi yasa zaka ga wani idan yazo, sai yace:
Ai larabawa ne suka gina…
Wani kuma sai yace:
ai akwai masu daukar nauyi…
Wallahi…
ba kowa bane Allah yake daura masa irin wannan nauyin.
Ba kowa bane zai iya daukar dawainiyar rayuwar
marayu haka ba tare da gajiya ba.
Gaskiya Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (Hafizahullah)
Ya cancanci yabo da addu’a.
Domin a zamanin da mutane da yawa
Suke tara dukiya don kansu…
Akwai wadanda suke kashe dukiyarsu domin rayuwar marayu ta gyaru.
Allah ya saka masa da mafificin alkhairi.
Allah ya sanya wannan aiki ya zama haske a kabarinsa.
Allah ya albarkaci masu tallafawa wannan gida na marayu.
Allah ya raya zukatan masu hali da son taimakon marayu.
Ameen Ya Rabbal Alameen.
Addinu Annasiha
Why is this not trending after being commissioned 3days ago ?
Sheik Tijjani Guruntum builds a boarding school for orphans known as “DARUL AYTAM ” Ya Allah bless him abundantly for this sadaqatul jariya 🤲🏽