Daga kusan ganga 900,000 a kowace rana a shekarar 2022, zuwa sama da ganga miliyan 1.6 a kowace rana, tare da cika kason hako mai da OPEC ta ba Najeriya na tsawon watanni 6 a jere a shekarar 2026.
Kafin zuwan Shugaba Tinubu, ana satar manmu. Ana fasa bututun mai. Kuma Najeriya na asarar kudade.
A yau, karkashin Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, an tsaurara matakan tsaro, kuma ana daukar kwararan matakan gyara a fannin mai da iskar gas.
Sakamakon kuwa: ana hako karin mai, kudaden ajiyar kasa sun karu, Naira ta kara daidaita, kuma kowace jiha na samun karin kudaden shiga.
Wannan shi ne aiki da manufa.
#ArewaforAsiwaju #A4A
Albishir ga ’yan fansho!
Hukumar PTAD ta biya basussukan fansho da aka gada na sama da Naira biliyan 91.5.
Ta kuma biya sama da Naira biliyan 60 na bashin ƙarin fansho na Naira 32,000 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi.
’Yan fansho sama da 150,000 na tsohon tsarin fansho ne suka amfana.
Yanzu ma, ɗan fansho zai iya kammala tantancewa ta intanet daga gidansa, ba tare da zuwa ofis ba. Tabbatar da rai da ake yi sau biyu a shekara ma ya zama da sauƙi.
Rage jinkiri. Ingantacciyar hidima. Gaskiya da inganci.
Ritaya cikin mutunci.
#ArewaforAsiwaju #A4A
Hukumar PTAD mai kula da fansho ta biya sama da naira biliyan 91.5 na tsofaffin basussukan fansho da ta gada. Ta kuma biya sama da naira biliyan 60 na bashin karin fansho na naira 32,000. 'Yan fansho sama da 150,000 da suka cancanta a karkashin tsohon tsarin fansho ne suka amfana.
An biya wadannan kudade ne domin a gama da basussukan da ake bi, kuma a inganta rayuwar ma'aikatan gwamnati da suka yi ritaya.
Haka kuma, PTAD na kawo tsarin zamani a harkokin fansho ta hanyar Integrated Automation System. Wannan tsari na ba 'yan fansho damar yin tantancewa ta intanet daga gidajensu, ba sai sun je ofishin hukumar ba.
An kuma inganta shafin intanet na tabbatar da cewa dan fansho yana raye (Aliveness Confirmation Portal). Yanzu, tantancewar da ake yi sau biyu a shekara, wadda wajibi ce, ta kara sauki ga kowa.
Ana sa ran wannan tsarin zamani zai rage jinkiri, ya inganta ayyuka, kuma ya kara gaskiya da inganci a harkokin fansho.
#ArewaforAsiwaju #A4A
The Bala-led ADC group is asking INEC to enforce the court judgment concerning Atiku's nomination as the party's presidential candidate, insisting that the ruling must be respected. They have now formally demanded compliance from the commission.
The ADC’s internal crisis may be heading for another dramatic twist. The Bala-led faction is stepping up its legal battle, seeking to enforce an earlier court judgment that invalidated Atiku Abubakar’s nomination as the party’s presidential candidate.
An gyara cibiyoyin lafiya na matakin farko sama da 3,500 a fadin Najeriya, kuma ana ci gaba da gyaran wasu guda 908. Gwamnatin Tarayya na yin haka ne domin jama'a su samu muhimman ayyukan lafiya cikin sauki.
Wannan ci gaba ya nuna irin kokarin da gwamnati ke ci gaba da yi wajen inganta cibiyoyin lafiya da kuma kyautata ayyukansu a garuruwa da kauyuka.
#ArewaforAsiwaju #A4A