"Mawaƙa kuwa, batattu ne suke binsu..." Allah bai koyawa Annabinsa ﷺ waƙa ba. Wannan Abu Bai Taɓa Zama Al'ada A Arewarmu Ba.
Abin da ya faru ya tayar da hankalina matuƙa. Musulunci bai hana a yi wa malami nasiha ko a bayyana rashin yarda da ra'ayinsa ba. Amma cin mutunci, zagi da wulaƙanta malamai ba hanyar gyara ba ce, kuma ba ɗabi'ar Musulmi ba ce.
Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne yadda wasu daga cikin Musulmai suke tafa wa irin wannan ɗabi'a, maimakon su yi kira zuwa ga ladabi da girmama masu ilimi.
Malamai ba ma'asumai ba ne. Idan sun yi kuskure, ana gyara su da hujja, ilimi da kyawawan ɗabi'u. Amma buɗe ƙofar zagi da raina su zai iya jawo mutane su daina girmama ilimi da masu ɗauke da shi.
Wai akan siyasa irin ta Nigeria ne mutum zai zagi malami, wanda ya dade yana yada sunnar Manzon Allah, Tun Ana Matasa har aka tsufa ake koyar da Islam. Tir!
Mu ji tsoron Allah game da harshenmu. Kalmar da mutum ya furta a yau na iya zama hujja a kansa gobe a gaban Allah.
Allah Ya kare mana mutuncin malamai masu gaskiya, Ya shiryi duk wanda ya kauce wa ladabin Musulunci, Ya kuma sanya mu cikin masu girmama ilimi da masu ilimi.
Alhamdulillah bini’matihi tatimmus salihat. Alhamdulillah ’ala kulli hal.
Alhamdulillah for another day. Always be grateful to Allah for giving you another chance, another opportunity, and another blessing. Every new day is a gift. May Allah guide us, protect us, and keep us steadfast. Ameen.