Official X page of Trust Radio 92.7FM Abuja, Nigeria...The voice you can Trust.
Listen to us live on our website for your up to date news and entertainment. RT
Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta saki wani manomi ɗan asalin Jihar Kaduna, tare da wanke shi daga zargin alaƙa da ƙungiyar Boko Haram, sannan ta biya shi diyyar naira miliyan uku.
https://t.co/07Eq2eZeh6
Dakta Bugaje ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da aka yi da shi cikin shirin A Wata Mahanga, shirin da wasu masana masu kishin Arewacin Najeriya suka samar domin wayar da kan jama’a game al’amuran yau da kullum a kafafen sada zumunta.
Lionel Messi ya sake kafa wani sabon tarihi a gasar cin Kofin Duniya, inda ya zama ɗan wasa na farko a tarihin gasar da ya zura ƙwallo a wasanni bakwai a jere, bayan da ya ci ƙwallo a wasan da ƙasarsa ta Argentina ta doke Jordan da ci 3-1.
Duk da cewa ba a fara wasan da Messi ba, sai bayan kimanin minti 60 da fara wasan ne tukuna ya shiga, amma ɗan wasan ya nuna ƙwarewarsa, inda ya zura ƙwallo tare da ƙara kafa wannan sabon tarihi a duniyar tamaula.
Wani matashi mai suna Amir ya gamu da ajalinsa bayan abokinsa ya soka masa wuƙa sakamakon wani saɓani da ya shiga tsakaninsu a unguwar Gama da ke ƙaramar hukumar Nassarawa a Jihar Kano kamar yadda kafar Arewa Updates ta rawaito.
Jami’an bijilanti na Jihar Kaduna (KADVS) sun daƙile yunƙurin yin garkuwa da yara tare da ceto wasu ƙananan yara guda biyu.
KARIN BAYANI:
https://t.co/LN1BppjKKO
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama wani matashi mai shekara 21, kan zargin fashi da makami bayan an gano wani hannun mutum, bindigogi da wasu kayayyakin da ake zargin na sata ne.
KARIN BAYANI:
https://t.co/Ecm2t6DSNu
’Yan bindiga sun keshe ’yan gudun hijira uku sun yi garkuwa da wani a ƙauyen Gangara cikin ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
KARIN BAYANI:
https://t.co/KBeCR73hTb
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Sakkwato, ta kama tan 3.9 na miyagun ƙwayoyi tare da cafke mutum 599 cikin shekarar da ta gabata.
Kwamandan hukumar a jihar, Mustapha M. Gidado ne, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka shirya domin bikin Ranar Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya ta 2026.
A cewarsa, daga cikin waɗanda aka kama akwai maza 532 da mata 67, yayin da kotu ta yanke wa mutum 24 hukunci, sauran shari’u 33 kuma na ci gaba da gudana.
Ya ce miyagun ƙwayoyin da aka ƙwato sun haɗa da tabar wiwi mai nauyin tan 1.2, magungunan ƙwayoyi masu sa maye masu nauyin kilogram 127.5 da kuma tan 2.5 na sinadarin codeine.
Gidado, ya ƙara da cewa mutum 65 sun samu kulawa da gyaran hali saboda matsalar shaye-shaye, yayin da sama da mutum 200 suka amfana da shirye-shiryen ba da shawara.
Ya buƙaci iyaye, shugabannin al’umma da matasa su riƙa ba wa NDLEA bayanai kan masu safarar miyagun ƙwayoyi domin taimakawa wajen yaƙi da wannan matsala.
Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi ta soke hukuncin da aka yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta yi wa jam’iyya NDC rajista.
Mai shari’a Isah Dashen ya ce an yanke hukuncin farko ba tare da sauraron dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa ba, lamarin da ya sa hukuncin ya saɓa wa tanadin doka.
Kotun ta kuma amince da buƙatar jam’iyyar PMP, wadda ta ce rajistar NDC ta shafi haƙƙinta saboda tambarin da aka yi amfani da shi.
Alƙalin ya umarci a mayar da komai yadda yake kafin hukuncin da aka yanke a watan Disamban 2025, sannan a sake fara sauraron shari’ar daga farko tare da haɗa INEC, NDC da PMP a matsayin ɓangarorin da abin ya shafa.
Hakan na nufin duk matakan da INEC ta ɗauka bisa tsohon hukuncin, ciki har da rajistar NDC, za su tsaya har sai an kammala shari’ar.
’Yan bindiga sun ƙone wata makarantar firamare a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, duk da cewa sun karɓi harajin Naira miliyan 10 daga al’ummomin yankin.
Ƙarin bayani 👇
https://t.co/QINRYCYg69
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya ce albashin Naira 70,000 ba ya iya biyan buƙatun ma’aikata la’akari da yanayin tattalin arziki da aka tsinci kai a halin yanzu.
https://t.co/bZRdqk4Vb6
An dai sace marigayin ne tare da abokinsa, Malam Muhammadu Maibarga, malamin addini na ƙungiyar izala, wanda shi ma kusan makonni uku da suka gabata ya rasu a hannun masu garkuwar.
https://t.co/nBZukJLy8g
Rundunar Sojojin Haɗin Gwiwar Jami’an Tsaro na Shiyyar Arewa maso Yamma, ƙarƙashin rundunar Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su. Da ƙwato wani babban makami na musamman, alburusai da babura da sauran kayayyakin aiki na ’yan ta’addan.
KARIN BAYANI:
https://t.co/ArRSj6P7WB
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi su gaggauta rufe asusun ajiyar kuɗaɗen mutane da kamfanonin da aka sanya a jerin masu alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci.
KARIN BAYANI:
https://t.co/f0FpIeTeKL