Na Samu Kira Na Musamman Daga Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kuma Wazirin Adamawa Alhaji ATIKU ABUBAKAR
Ban taba tunanin irin rubuce-rubuce da nakeyi akan Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa), da irin Tagging nasa da nake yana gani ba. Ina zaune na samu kira akan cewa lallai-lallai yana buƙatar ya samu zama dani, mu ƙulla mu'amala maikyau kuma na shiga cikin kwamitin yaƙin neman zaɓe na 2027 ba.
Wato ban taba tunanin haka waziri yake da sauƙin mu'amala da mutane ba, da muka haɗu tun kafin nayi magana ya kira sunana (Muhd Sheka). Ban mayi tunanin zai iya gane fuskata ba, ko mu zauna muyi tattaunawa ta tsowon irin lokacin da mukayi dashi ba.
Allah ya sani ni lokacin da nake maganganu na, ina yin su ne dan kawai kishin Arewa, da kuma imanin cewa a yanzu bamu da dan takarar da ya wuce sa. Ban tunanin ashe yana gani ba, for me wannan ba karamin nasara bace da abun alfahari matuka sosai da sosai.
Ni lokacin da yana magana gabaki daya ma dibibicewa nayi, dan mutum kamar sa da yake da tasiri a siyasar Afirka da Nigeria. Kuma muke gani kamar ya zama shugaban ƙasa ne a 2027 ace wai ya zauna dani gaskiya abune mai nauyin gaske.
Abu guda da ban manta dashi ba shine Yan Crypto na Arewa, wannan ne kuɗirin da ban manta dashi ba. Kuma ya nuna jin dadinsa sosai da yaji ina cikin manyan waɗanda suke jagorantar harkar a Arewa, kuma na roka mana Alfarma har idan aka ci zaɓe kada a manta da al'ummar mu ta yan Crypto ɗin Arewa.
Ya kuma ji dadin irin Abubuwan ci gaba da muke so a kawo mana a tsakanin matasan mu na yan Crypto idan aka samu nasara a 2027, In Sha Allah idan Allah ya tabbatar da Waziri a matsayin shugaban ƙasa za'a ga sauyi na Alkhairi akan harkar Crypto fiye da kowane lokaci a Tarihin Nigeria.
Gwamnatin da Alhaji Atiku Abubakar zai kafa a 2027 ba gwamnati ce da zatayi yaƙi da yan Crypto ba musamman na Arewa, gwamnati ce da zata jawo su a jiki a tallafa musu. Ba gwamnatin da zata dinga kawo tsare-tsaren da zasu ruguza harkar ba.
Akwai miliyoyin yan Crypto a Arewa wadanda suka dogara da harkar Crypto ta zama da ita suke ci kuma suke sha, lalata harkar bazai taba zama shine alheri ba. Nan gaba kadan yan Crypto kananun mu da manya zasu amfani gwamnati fiye da yadda yan harkar drama suke morar ta In Sha Allah.
#Atiku2027 #Atiku2027
In solidarity for the #BornoSix#TMG ambassadors arrested and detained oppressively. While our lawyers are working tirelessly, I’ll be wearing this every they are free!
Abubuwan da nake so a kula dasu game IPO na kamfanin Dangote, nayi wannan rubutun ne bayan tambayoyin da na samu masu yawa daga mutane.
Idan kayi placing order domin sayan hannun jarin Dangote ba dole ne a baka adadin abinda kake so ba. Misali; kana so ka sayi hannu jari na Naira dubu 100,000 sai kayi placing order a yanzu da ake yin IPO.
Idan aka kammala IPO ranar 13 Oct 2026 ba lallai ne a baka SHARE din Naira dubu 100,000 gaba daya ba, zasu iya baka SHARE na Naira dubu 40,000 su dawo maka da Naira dubu 60,000. In yaso daga baya ka shiga kasuwa ka sayi na sauran kudin da aka dawo maka dashi.
Baka da garanti cewa za'a baka na kudin da kake so gaba daya a IPO. Zasu buga lissafi ne base on adadin SHARE da suke so su siyar wato 4.1 billion SHARE da kuma adadin order da aka yi placing a IPO.
Already dama suna so su samu Naira trillion 2.1 ne.
Idan Order din da aka yi placing ya zarce Naira trillion 2.1 toh a nan ne za'a buga lissafi aga na Naira nawa kake son saya kuma na nawa zasu baka, Naira nawa za'a dawo maka da.
Na biyu, Ni ba zan yi placing order na IPO da kudi mai yawa ba a yanzu, ko zanyi ma kudi kadan zan saka a IPO, zan jira har sai ya shiga kasuwa an fara trading dinsa. Domin akwai yuwuwar yayi kasa zuwa 500 ko 450 ko 400 ko ma 350 bayan an sake shi a kasuwa. A dai dai wannan lokacin nake ganin ya kamata in saya base on technical and fundamental analysis da kuma period da nake so nayi holding dinsa.
Na uku, idan aka ce IPO toh abinda kake so ka saya babu shi a kasuwa a yanzu, yana hannun masu shi, dan haka zaka ga idan kayi placing order akan Bamboo ko daya daga cikin Application babu kudin kuma babu SHARE. Sannan dole ka jira sai an kammala IPO idan ma kana son siyarwa domin fitar da kudin ka.
Za'a yi listing dinsa a Naira 525 ne, ba za suyi listing dinsa kasa da haka ba. Idan kaga ya sauka bayan anyi listing toh kasuwa ce ta saukar dashi ba kamfanin ba. Kamfanin man Dangote babban kamfani ne a duniya dan haka ko ba yanzu ba farashin hannun jarin zai tashi zai zarce inda ake zato da ikon Allah, amma sai mai hakuri ne zai ci ribar hakan.
Yana da kyau a sani cewa Stock ba kamar crypto bane, baya da volatility kamar crypto, sannan ba sha yanzu magani yanzu bane. Idan kana da ilimin technical and fundamental analysis zaka iya trading stocks, idan kuma baka dashi zaka iya holding na tsawon wasu shekaru.
Sannan karamin kudi baya kaika inda kake so a stock koda kuwa ka shekara biyar kana holding. Dole kudin su zama suna da dan nauyi kadan. Ba kamar crypto bane da zaka sayi abun Naira dubu 100,000 a cikin kwanaki kadan ya koma miliyan 1 ko 2 ko ya sauka zuwa Naira dubu 20,000.
Idan yanzu yanzu kake son yin kudi toh karka shiga harkar Stock wato hannun jari.
Wannan IPO din ana kiran sa da Presale a kasuwar crypto, ana kiran sa da ICO (Initial Coin Offering) anyi wa Ethereum haka a June 2015 ko kuma suna kiran sa da IDO (Initial DEX Offering) idan a DEX ne, wato Decentralized Exchange.
Just hit 33,000 followers 🎉🥳🥰
Appreciate everyone supporting me, grateful fr.
Turn notifications on, let’s win & grow together in 2026.
Thank youuuuuuuuuuu 💯🤝
Yadda zaka samu damar sayan IPO na Dangote Refinery cikin minti 5.
Idan kana son mallakar kaso a kamfanin Dangote Refinery, ga abin da zaka yi:
1️⃣ Sauke Broker App
Ka shiga Play Store ka sauke ɗaya daga cikin:
• Bamboo
• i-invest
• Cowrywise
• Afrinvestor
• Meristem
2️⃣ Buɗe Account
Ka yi registration sannan ka kammala KYC verification da BVN ko NIN.
3️⃣ Jira Verification
Yawanci verification na iya ɗaukar kwana 1–2.
4️⃣ Saka Kuɗi
Bayan account ɗinka ya samu approval, ka saka adadin kuɗin da kake son amfani da shi.
Misali: ₦10,000.
5️⃣ Ranar 14 September
A lokacin da IPO ya buɗe, ka shiga app ɗinka ka nemo damar IPO ɗin.
Sai ka zaɓi adadin shares da kake son nema.
6️⃣ Jira Allocation
Bayan rufe IPO, zaka jira allocation.
Idan aka ba ka shares, zaka ga su a account ɗinka .
---
A TAƘAICE:
Buɗe Broker Account → KYC → Saka Kuɗi → Apply for IPO → Jira Allocation → Karɓi Shares.
Kada ka jira ranar IPO kafin ka fara shiri.
Ka buɗe account tun yanzu.
Idan kana da tambaya game da IPO ɗin, ka rubuta ta a comment section. 👇🏾
Madalla da Ubangijinmu mai bayarwa kafin mu roka.
Sannan ya amsa mana idan muka roke shi!
Kuma ya ninka mana idan muka gode mishi.
Ya Allah ka tabbatar damu akan gode ma ni'imominka! 🤲🏾
Wallahi wallahi wallhi Na Rantse Muku da Girman Allah da Anyi Burning din 50% na $SANUSI Token Yau da sai Mun Taba $5M Market cap
Munada Buri dogo Munyi Maganganu Sosai da Manyan Exchange Akan Yadda Zasuyi Listing dinsa idan Munje wani Mataki na Market cap Shiyasa Muka zabi Kona 50% na Abinda Muke Dashi domin kaiwa wajan
Munyi Magana sosai da Manyan investors da zasu Shigo su saka Kudi domin kaiwa wani Mataki wanda kowa yasan Manyan Project suna subada irin wannan tsarin
Munga Soyayya Sosai da Mutane masu Tarih Yawa da sukeso a basu dama suzo suyi Hidima da Kudin Su Domin kaiwa wani Mataki
Amman daka Karshe Mun Fada Tarko kuma Tarkon da baifi Karfin Kowa ba Hatta Manyan Exchange irin su Bybit sun fuskanci irin haka
Dan Haka ina Mai Tabbatar Muku wannan bazai zama sarewar Guiwa Ko kuma na Karshe ba koda SANUSI ya tsaya sai Mun janyo Ra,ayin sa akan kada ya Tsaya
Mune dai Mukai Asara Kudin Mu ne dan Haka wannan bazai sare mana Guiwa ba sedai kawai Mun Koyi wani Darasi Babba Mai Tarih Yawa da dole sain Mun Gyara kafin mu dawo
Kuma Akwai Bukatar Ku sake Shigo da wasu cikin Tafiyar Mu domin a Gudu Tare a tsira Tare
Jami'an gwamnatin Taliban da kuma shugabannin 'yan adawar Afghanistan sun halarci jana'izar Ali Khamenei a birnin Tehran na ƙasar Iran.
Ƙarin bayani - https://t.co/aVL9wMbsgu