‘Yan Najeriya na nuna jin dadinsu bayan da kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya bai wa tsohon dan wasan Super Eagles Kingsley Obiekwu Naira Miliyan 2.
Tsohon dan wasan dai ya shiga wani hali saboda yanayin rayuwa wanda ya sa har ya koma aikin direba a jihar Enugu.