Duk wanda yake rayuwa yana iya yin kuskure, amma hikima tana cikin yarda da kuskuren da kuma ƙoƙarin gyara shi. Kada ka hukunta kanka har abada saboda abin da ya riga ya wuce; ka ɗauki darasi ka ci gaba.
Wallahi na dade banga abinda yabani dariya ba kamar yau😂 na sauka a keke napep kenan dazu kawai nagani wani police yana min magana bayan na tsaya kawai naji yacemin “don Allah in taimakeshi tun safe Baici abinci ba”😂💔
Wata Akuya a Kano ta aikata babban laifi bayan ta cinye Naira 500 ta wani yaro.
Yaron yace ya kama Akuyar ne saboda ta cinye masa Naira 500, kuma yaje wajan mai Akuyar tace yaiwa Akuyar hukuncin da yaga dama.
Yanzu haka dai yaron yace zaiyi gaba. Da akuyar zuwa gidansu, har sai mai akuyar ta biya 500 din 🤣😂
Mafi kyawun yadda mutum zai kalli kansa shine kada ya ɗauki kansa sama da sauran mutane, Ya kasance mai tawali'u, domin tawali'u yana rufe aibin mutum, yana ƙawata darajarsa, yana ƙara masa ƙima a idon mutane, kuma yana cika rayuwarsa da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Ƙoƙari yana daga mutum, amma nasara kuma tana daga Allah, wasu suna ƙoƙari matuƙa, sai dai lokacinsu bai yi ba tukuna, Idan lokacin Allah yayi, abin da yayi nisa zai zama kusa.