☘️Ya Ubangiji Ka Bamu Sanyin Idanuwa Daga Cikin Matayanmu Da Zuri'armu,Ka Sanya Mu Zama Jagorori Ga Masu Jin Tsoron Allah.🤲
🌹An kar6o daga Aby Mas'ud Albadry R.A yace :Manzon Allah S.A.W yace : Sallar mutum ba ta wadatarda shi,har sai ya miqarda bayansa a ruku'u da sujjada.🌹
🌹Daga Annabi ﷺ yayin da yake kan minbari ya ce:"Ku yi rahama,za a yi muku rahama. Ku yafe, Allah zai yafe muku.Kaico ga waɗanda kawai suke jin magana amma ba sa amfani da ita. Kaico ga masu tsananin ɗaukar laifi, waɗanda suke ci gaba da aikata abin da suka sani ba daidai ba."🌹
☘️Ya Ubangiji Ina Roqonka Shahada A Bisa Tafarkinka.🤲🏽
🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Idan dayanku ya shiga masallaci, ya sallaci raka'o'i guda biyu kafin ya zauna.🌹🌹
Bukhari da Muslim
☘️Ya Ubangiji Ka Gafarta Min Zunubaina Ka Shigarda Ni Mashiga Ta Karamci A Ranar Alqiyama.🤲🏽
🌹🌹Abdullahi bn Mas’ud R.A ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Allah yana da mala’iku masu yawo a ƙasa, suna isar mini gaisuwa daga al’ummata."🌹🌹
(Nasa’i)
☘️Ya Allah,ina neman tsari a wurinka daga sharri na abin da na aikata,da kuma daga sharri na abin da ban aikata ba.🤲
🌹An kar6o dg Abdullahi ɗan Umar R.A ya ce: Manzon Allah S.A.W ya ce:"Wanda ya ja tufafi a kasa Dan girman kai,Allah ba zai kalli gare shi ba a ranar kiyama."🌹
☘️Ya Ubangiji Ka Yi Salati Ga Annabi Muhammad S.A.W Da Iyalan Annabi Muhammad.🤲
🌹🌹An kar6o daga Hafs bn Ãsim R.A yace : Manzon Allah S.A.W yace : Ya ishi mutum ya yi qarya, idan ya zama yana bada labarin duk abinda ya ji.🌹🌹
Muslim
🌹daga Aby Hurairah R.A,daga Annabi S.A.W yace : Lallai za ku kasance masu tsananin kwaɗayin samun shugabanci, Amma a ranar Alƙiyama zai zama abin nadama, D farko yana da daɗi kamar na jariri wanda ake shayarwa,amma a ƙarshe yana da zafi kamar na jaririnda ake yayewa.🌹
Bukhari
☘️Ya Ubangiji Ina Roqonka Ka Shiryeni Izuwa Ga Gaskiya Da Izininka🤲
🌹An kar6o daga Aby Hurairah R.A, Haqiqa Annabi S.A.W yace : Addu'o'i guda uku ababan amsawa ne, babu kokwanto a cikinsu, addu'ar wanda aka zalinta, da addu'ar matafiyi, da addu'ar mahaifi akan dansa.🌹
☘️Ya Ubangiji Mai Sarrafa Zukata,Ka Sanya Zuciyarmu A Wajan Yimaka Biyayya.🤲
🌹🌹An kar6o daga Aby Hurairah R.A yace : Haqiqa Annabi S.A.W yace : Allah S.W.T yace : Ni ina inda bawana yake zatona, kuma ina tare da shi idan ya kirayeni.🌹🌹
Muslim
☘️Babu Abin Bautawa Bisa Cancanta Sai Kai,Tsarki Ya Tabbata A Gareka,Haqiqa Ni Na Ksance Daga Cikin Azzalimai.🤲🏽
🌹haqiqa Annabi S.A.W yace : Babu wata addu'a da bawa zai yi roqo da ita,sama da yace : Ya Ubangiji Ina Roqonka Lafiya Da Zama Lafiya A Duniya Da Lahira.🌹
☘️Ya Ubangiji Ka Shiryeni Ka Dorani Akan Hanya, Ya Ubangiji Muna Roqonka Shiriya Da Tsayuwa Akan Hanya.🤲🏽
🌹haqiqa Annabi S.A.W yace : Masu cike gurbi, mai fadarsu ba ya ta6a ta6ewa, ko kuma mai aikata su, tasbihi 33, tahmidi 33, da kabbara 34 a qarshen kowacce sallah.🌹
🌹An kar6o daga Anas bn Malik R.A, haqiqa Annabi S.A.W yace : Duk wanda ya fadi wannan addu'ar sanda ya futo daga gida yace : Bismillahi Tawakkaltu Alallahi Wala Haula Wala Quwwata Illa Billahi za a ce masa an isarmaka, an tsareka, kuma shaidan zai nisanci inda yake.🌹
Tirmizy
☘️Y Ubangiji Kyi Salati G Annabi Muhammad S AW,Da Iyalan Gidan Annabi Muhammad SAW🤲
🌹Haqiqa kun kasance kuna aikata wasu ayyuka,wadanda sun fi gashi qanqanta a idanuwanku, mu kuwa mun kasance muna kallon wadannan ayyuka a matsayin ayyuka masu halakarwa a zamanin Annabi SAW🌹
🌹Haqiqa Ummu Sulaim R.A ta yi sammako zuwa wajan Annabi sai tace:ka koyamin wasu kalmomi da zan ringa yinsu a sallarta,sai yace SAW:ki yiwa Allah kabbara sau goma,ki yiwa Allah tasbihi sau goma,k godewa Allah sai goma, sannan k roqi abinda kike so,Allah zai ce Na amsa Na Amsa.🌹
☘️Ya Ubangiji ka kawo mana shi cikin aminci da amana,da salama da miqa wuya,da dacewa cikin abinda kake so kuma ka yarda da shi.🤲
🌹Manzon Allah S.A.W yace : Idan dayanku yayi duba izuwa wanda aka bashi dukiya sama da tasa,to ya sake duban wanda kuma yake qasa da shi shi ma.🌹
Y Ubangiji In Rqnk Firdausi Madaukakiya A Cikin Aljannatai.🤲
🌹Annabi SAW yace:Za ku ringa bin sunnar wadanda suka gabaceku dani da dani,zira'i da zira'i,d za su shiga ramin damo,d sai kun bisu,sai muka ce : y Ma'aikin Allah,kana nufin yahudawa da nasarawa? Sai yc: To su wa ?🌹
☘️Y Allah K gafarta min, ka yi min rahama,ka shiryar da ni,k ba ni lafiya,kuma k azurta ni.🤲
🌹Manzon Allah S.A.W yace :Duk wanda ya amince ya soke cinikin da wani Musulmi ya yi saboda ya yi nadama,Allah zai yafe masa kuskurensa kuma Ya tsare shi daga tuntuɓe a ranar Alƙiyama.
☘️Ya Ubangiji Muna Roqonka Ka Qaramana, Kada Ka Ragemana, Ka Karramamu, Kada Ka Bari Mu Wulaqanta, Ka Bamu, Kada Ka Hanamu.🤲🏽
🌹🌹 Annabi S.A.W yace : Allah ya jiqan mutuminda yake da sauqin kai idan zai sayar, da sanda zai saya, da sanda zai biya bashi.🌹🌹_
Bukhari
☘️Ya Ubangiji Ina Roqonka Tatacciyar Rayuwa Da Sassauqar Mutuwa,Da Makoma Wadda Babu Qasqanci Ko Kunyata A Cikinta.🤲
🌹haqiqa Annabi S.A.W yace : Lallai Allah Ya la'anci ko Ya yi fushi da wani ɓangare daga Bani Isra'ila, sai Ya mayar da su dabbobi masu rarrafe a doron ƙasa.🌹
☘️Ya Ubangiji Kayi Salati Ga Annabi Muhammad S.A.W Da Iyalan Gidan Annabi Muhammad S.A.W.🤲
🌹🌹An kar6o daga Aby Hurairah R.A yace : Manzon Allah S.A.W yace : Ba dan banu isra'ila ba, da ba'a ringa taskance nama ba.🌹🌹
Bukhari da Muslim