Labarin Dr Gwadabe is just one story with many faces.
Wannan halin da Dr Gwadabe ya tsinci kansa, a matsayin wanda yake amfani da Alfarmar ilimi yake cin amana. A iya cewa labari ne mai fuskoki da yawa idan aka dora shi a wata mahangar.
Ni malamin makaranta ne, kuma akalla na koyar a Nigerian Universities har guda biyu, da kuma two foreign universities. Kuma zan iya bugar kirji nace muku kamar yadda Dr Gwadabe yayi approaching wannan baiwar Allah daliba, haka suma dalibai suke approaching malamai wanda basu ji ba basu gani ba. Kuma wannan matsalar ba matsalar Nigeria bace kadai, ko ina akwai. Har yanzu ina ajiye da record na police report da nayi akan wata student a wata foreign university da na koyar.
Kullum idan zan fita iyalina sukan min addua su ce Allah ya raba ka da matan banza. Wannan addu'a ce da na tashi naji mahaifiyata tana yi wa mahaifana. Kuma addu'a ce da kowannenmu yake bukata a rayuwarsa. Kamar yadda mata ke cin karo da mazan banza, haka mu ma muke cin karo da matan banza. A wajen aiki, a kasuwa, a restaurant, a parking lot, a ko ina fa.
Duk sabon session idan aka yi admission sai ka samu yara freshers masu bi office office suna neman wane malami za suyi wa apprentice, wato kamar kace almajiri a ilmance. Wasunsu zasu gaya maka straight idan ka dauke ni apprentice, to zan maka duk abin da kake so including mu'amalar da bata dace ba. Ni personally nayi rejecting apprentice akalla biyu a career dina as a lecturer.
Haka kuma duk end of semester idan aka yi exam, sai ka ci karo da solicitations notes a cikin booklet, yarinya tana ce maka don Allah ka taimake ta bata yi karatu ba, she is ready to offer anything. Wasu har da address din daki ko lambar waya. Irinsu idan ka tonasu ka taimaka wajen samar da yan iska a cikin society. To kawai sai dai kayi hakuri ko ka kira su ka musu nasiha.
Nayi aiki a office din da wata ta tsane ni sabida ance ni wai idan nazo wucewa bana daga kai na kalli mata. Suna kwalliya amma bana musu complement. Aka ce ku rabu da shi zai ga sharrin mace. Aiki ya hada mu watarana ta yi ta catwalking a office dina ko kallon gurin banba. Haka ta gama ta fita.
Aikin koyawar is one of the most dangerous jobs in the world as person as irin wannan abubuwan are concerned. Yanzu zaka zama tempted. Yanzu za'a rude ka. Yanzu za'a maka sharri. Yanzu za'a lalata ka. Muna da colleagues yan iska. Mu munsan suna yi kuma har tayi suna wa abokansu. Wasu har league ne dasu. Suma kuma matan wasu har Group gare su.
Nasan wata student a wani state da bazan fada ba. Take cewa yan hisba ba malaminta da bata kwanta da shi ba don tayi passing exam. Idan kana jin wannan labaran sai ka rantse karya ne shiryawa kawai akai. To amma wuyarta kaje wajen. Da ka je zaka gani. Kaima sai dai azkar. 😁
So in my professional opinion ina bada shawara. Idan zina ta zame maka jiki to ka sanyawa kanka ka'ida. Ko nama 🥩 akwai haram ballantana farji mace. Ka gayawa kanka gaskiya wajen aiki ba wajen iskanci bane. Wajen sana'a shima ba wajen iskanci bane. Duk inda kake neman arzuki ko neman sa'a, ba'a zina a wajen. Lalata rayuwa take. Duk wanda suke zina a wajen sana'a wallahi basa dorewa a wajen.
Sannan babbar illar zina da students shine sai sun bada labari. Haka muka rika faman ceto wani Ustazu ni da Malam Abdallah da Shaikh Ali Yusuf da ya samu irin wannan jarrabawar. Student din da ya nema ne suke yayata shi cewa yana nemansu, ko ya taba nemansu. Wallahi ba karamin aiki mu kayi don ganin ya daina ba. Kuma har yanzu idan suka samu wuri zancen suke. Kaga mutum da mutuncinsa da kimarsa amma yana wucewa ana masa kallon fasiqi. Allah ya shirye mu. Allah ya mana tsakani da shaidan. Allah ka kare mana farjinmu daga haram. Ka bar mu akan halaliyarmu har abada.
Facebook: Muhammad Ubale Kiru
Midnight politics in Kano:
Former Governor Dr. Abdullahi Umar Ganduje has met with Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, as rumours of a possible alliance continue to shake the political waters in the state.
With Gawuna reportedly set to join the ADC, this could spell serious trouble for Abba Kabir Yusuf’s political future in Kano.
Tsohuwar matar Aminu Warkal ce mai suna Khadija Hassan Yar asalin garin Jos na Jihar Pleatoe, tayi zargin cewar yaci mutuncinta ya kuma koreta daga gidansa Cikin dare.