Wannan ita ce maganar Sheikh Dr. Lawal Abubakar Triumph. Kuma babu in da ya faɗi ƙarya ko ya yi rashin ladabi ga Ma'aiki, amincin Allah ya ƙara tabbata a gare shi.
Wanda bai yi karatu ba yana ɗaukar duk labaran da ake bayarwa a wajen bikin maulidi gaskiya ce tabbatatta, don haka duk wanda ya saɓa mata bai girmama matsayin Manzon Allah (saw) ba.
Sheikh Lawal, ka yi haƙuri da tsangwama kuma ka ci gaba da bayyana gaskiya.
Allah ya cigaba da ba Sunnah da Malaman ta kariya. Ameeen!