Ɗanbaiwa, idan kana yawo a wannan space kuma baka da alqibla, baka san inda kake son zuwa ba...To kada ka fara da neman kuɗi.
Abu na farko shi ne ka Fara da neman ILIMI.
Ka sami wanda ya riga ya san hanyar da kake son bi, ka koya a ƙarƙashinsa.
Kayi amfani da kowane hanya d aka samu wajen neman Ilimi - na zamani ne ko na gargajiya.
Ka nitsu har sai ka koya. Ka fahimta.
Sai ka fara aiki da ilimin.
Idan kafinta ne, kada ka tsaya a profile ɗinka kana damun jama'a kana cewa “Ni kafinta ne.”
Ka fara yin kujeru, tebura da gadaje.
Ka ɗaura hotunan a page ɗinka
Idan ka fara aiki kuma abubuwa suna tafiya, abin da kake buƙata shi ne ƙwazo, haƙuri, dagewa da naci.
Domin:
Ilimi yana nuna maka hanya.
Aiki yana fara tafiyar da kai.
Naci kuma yana kai ka inda kake son zuwa.
Da Haka ake gina rayuwa mai inganci.