Gwamnan jihar Kwara kuma shugaban gwamnonin Najeriya, Abdulrahman Abdulrazaq ya shawarci shugaban Najeriya Bola Tinubu kan ƙara mafi ƙarancin albashi a ƙasar.
Gwamnan ya ce matakin zai yi amfani duba da irin tsadar rayuwa da ƴan Najeriya ke ci gaba da fama da ita.