Menene Data Analysis a gaske?
Data Analysis hanya ce ta fahimtar abin da ke faruwa a kasuwanci, makaranta, lfy, ko gwamnati ta hanyar bayanai. Idan ka iya karanta data d kyau, zaka iya taimakawa wajen yanke shawara mai inganci da rage kuskure. A yau, duk dny tn tafiya ne d data.
DO YOU WANT TO BECOME A DATA ANALYST?
If your goal is to learn Excel, SQL, Power BI, Python & build the skills you need to land a Data Analyst job before next year, this is for you.
If you’re serious about learning DTA & ready to put in the work, say “HI” or comment “INTERESTED.
This is a Sales Analytics Dashboard.
It is an Excel dashboard used to track, analyze, and visualize sales performance, including revenue, orders, customers, products, quantity sold, and regional sales.
Comr. AA Wudil
Founder Sadeeq Data Lab
CONDITIONAL FORMATTING:
Conditional Formatting is one of the most useful features in Excel and Google Sheets.
It helps you highlight important data automatically.
Example:
• High scores → Green
• Low scores → Red
• Empty cells → Highlighted
Thread 1.
This makes work easier when handling many rows of data.
Instead of checking everything manually, you can quickly see:
✓ Best performance
✓ Weak performance
✓ Errors
✓ Missing values
This saves time and helps you understand your data faster.
🇳🇬 Maryam Ibrahim Dan’azumi ta samu gagarumar nasara!
Maryam Ibrahim Dan’azumi daga Jihar Gombe ta zo ta 1 a bangaren Women’s Tafsir na sashe na 60 Hizb, inda ta lashe kyautar Riyal 300,000 na Saudiyya, wanda ya kai kusan ₦120 million.
Wannan babbar nasara ce ba ga Gombe kaɗai ba, har ma ga Najeriya baki ɗaya. 🇳🇬
Muna taya ki murna, Maryam Ibrahim Dan’azumi! 🎉👏
Allah ya ƙara ɗaukaka ki, ya sanya wannan nasara ta zama abin alfahari ga ƙasa baki ɗaya. 🇳🇬❤️
GM CT
KADA KA TAƁA RAINA WANDA YAKE ƘASA DA KAI A YAU
Domin itaciyar da take ƙasa a yau, ita ce za ta iya yi maka inuwa gobe. 🌳
Idan ka ga mutum yana yawan murmushi 😊, kada ka ɗauka cewa babu damuwa a cikin zuciyarsa.
Wani lokaci, murmushi sutura ce da ake rufe raunin zuciya da ita. 💔
Ka kasance mai tausayi, ka girmama kowa, kada ka raina kowa.
Rayuwa tana juyawa, kuma matsayin mutum na yau ba lallai ya zama matsayin sa na gobe ba.
🤲 Allah Ya sa mu kasance masu tawali'u, tausayi da kyakkyawar mu'amala da kowa. Ameen.
BA A HAƊA GUDU DA SUSAR MAZAUNAI✍️✔️
Kana matashi, shekarunka daga ƙasa da 18 zuwa 25 ko 30. A kan me ya kamata ka fi mayar da hankali a wannan lokaci? 🤔
GINA KAI 📢
Ka tsaya ka gina kanka. Ba wanda zai gina ka sai dai ya taimaka maka wajen gina kanka.
Iyayenka da za su biya maka school fees tallafi ne. Kai ne za ka zage ka yi karatu, ka fahimci abin da ake koya maka, ka samu sakamako mai kyau. Idan ka yi wasa, kai ka yi wa kanka asara.
Sun yi iya abin da za su iya maka. Wasu ma har ƙasashen waje iyayensu suka kai su karatu, amma suka ƙi mayar da hankali, daga ƙarshe aka dawo da su gida.
Mai gidanka da zai koya maka sana'a ko skill domin ka kware, tallafi ne yake maka. Kai ne ya kamata ka maida hankali ka koya. Idan ka yi wasa, kai za ka yi wa kanka asara.
KA RAYU DA MANUFA ✍️
Saboda sabuwar balaga tana motsa sha'awa, ka koyi horar da kanka. Kada ka bari soyayya ko biyan sha'awa su zama abin da zai cinye maka mafi kyawun shekarunka.
Lokacinka ⏰
Kuɗinka 💰
Ƙarfinka 💪
Tunaninka 🧠
Ka zuba su wajen gina kanka.
Duk wata alaƙa ko wani aiki da za ka yi, ka riƙa tambayar kanka:
“Menene sakamakon wannan?”
“Me zai amfane ni?”
“Ina wannan zai kai ni nan da shekaru 5?”
Uwar me soyayya za ta amfanar da kai a yanzu ko ɓata lokaci? Soyayya za ta iya zuwa daga baya. Amma shekarun da kake da su yanzu ba za su dawo ba.
Idan akwai mutanen da ya kamata ka faranta musu rai yayin da kake fafutukar gina kanka, iyayenka ne, domin neman albarka da addu'arsu.
Ba 'yan matan da idan kuka sami saɓani za su ce maka "ME KA TAƁA MIN?" ko "NI NA SAKA KA?" ba😂
KADA KA YI GAGGAWA
Kada ka takurawa kanka sai ka sa sutura kala kaza, ka riƙe wayar hannu (phone) irin ta wane, ka sayi abin hawa ko cin abincin 'yan gayu. KAI! Ka rayuwa daidai da matsayinka.
KAI! Ka rayu gwargwadon matsayinka.
Kowane sisi da kobo da za ka kashe, ka tambayi kanka:
“Me ya sa nake kashe wannan kuɗin?”
Me ya sa sai wayar ₦500k?
Me za ta ƙara min?
Idan wayar ₦50k tana iya biyan buƙatunka, me ya sa za ka kashe ₦500k domin kawai ka burge mutane?
Ka koyi rayuwa daidai da abin da kake da shi, ba daidai da abin da kake son mutane su yi tunanin kana da shi ba.
A shekarunka, ba lallai ka tara abin duniya irin na ɗan shekara 45–60 ba.
Ka tambayi kanka:
“Yaushe suka fara gwagwarmaya?”
Kar ka ɗauki sakamakon rayuwar wani mutum a matsayin ma'aunin inda ya kamata ka kasance kafin shekara 25 ko 30.
KA RABA KANKA DA MAƘIYANKA
Maƙiyanka ba lallai su kasance mutanen da suke kusa da kai ko nesa da kai ba.
Wani lokaci, babban maƙiyinka yana cikin zuciyarka.
Idan ka bi son zuciya ba tare da horo ba, zai iya dankwafar da kai.
Ka cire kasala. Lokacin fafutuka ba lokacin yawan hutu ba ne.
Ka nisanci abin da zai ɗauke hankalinka daga manufarka.
Kada ka haɗa rayuwarka da shaye-shaye.
Kada ka mayar da rayuwarka gasar da abokanka.
Ka guji dogon buri ba tare da aiki ba.
Kai mai koyo ne a yanzu; ka guji nuna gwaninta da kamala a komai.
Ka kiyaye kanka daga ƙarya, cin amana, girman kai da taurin kai.
Ka sanya Allah a cikin lamarinka. Ka kiyaye ibada, addu'a da neman kariya.
Ka yi aiki tuƙuru, ka koyi sana'a, ka karanta, ka gina halinka da tunaninka.
KA YI AIKI TUƘURU.
KA GINA KANKA.
KA JIRA LOKACI.
Domin abin da ake ginawa da haƙuri, ilimi da jajircewa, sau da yawa yana daɗewa fiye da abin da aka samu cikin gaggawa.
Allah Ya kawo babban rabo. 🤲
✍️ Comr Abubakar Ahmad Soja

# Ra'ayi Kan Haramcin Yin IV da Ƙarin Jini a Shagunan Magani a Kano
Na ga labarin cewa Gwamnatin Jihar Kano ta haramta yin allurar jijiya (IV), saka karin ruwa (IV fluid) da kuma ƙarin jini (blood transfusion) a shagunan sayar da magungunan patent medicine a faɗin jihar.
Na fahimci cewa akwai dalilai na kiwon lafiya da ƙa'idodin aikin jinya da za su sa a bukaci gudanar da irin waɗannan ayyuka a wuraren da suka dace. Amma a ganina, ya kamata a sake duba wannan mataki ta hanyar la'akari da ainihin yanayin rayuwar al'ummar Kano, ba wai ƙa'ida kaɗai ba.
A zahiri, shagunan magani ko **Chemist** sun zama wurin farko da mafi yawan mutane ke zuwa idan suna neman kulawar lafiya cikin gaggawa. Idan aka tambayi mutane 100 da suke karanta wannan rubutu, ina ganin fiye da rabinsu sun taɓa zuwa shagon magani domin neman magani, allura ko karin ruwa, musamman idan ana fama da cututtuka kamar Malaria da Typhoid.
Duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen inganta harkar lafiya, gaskiyar magana ita ce, ba kowane yanki ne ke da asibiti mai sauƙin samu ba. A wasu wurare, shagon magani ne wurin farko da mutum zai iya samu cikin gaggawa idan rashin lafiya ta taso.
Amma wannan ba yana nufin ina goyon bayan a bar kowa ya yi wa kowa IV, karin ruwa ko ƙarin jini ba. A'a. Abin da ake bukata shi ne tsari mai kyau, lasisi, horo, ƙwarewa, kulawa da kuma tabbatar da cewa wanda yake gudanar da aikin ya cancanta.
Idan akwai mutanen da suke gudanar da irin waɗannan ayyuka ba tare da ƙwarewar da ta dace ba, a ɗauki matakin da ya dace a kansu. Idan akwai masu amfani da magunguna ba bisa ƙa'ida ba, a hukunta su ko a rufe wuraren da suka cancanta. Idan kuma ana samun matsalar amfani da miyagun ƙwayoyi, gwamnati ta ci gaba da yaƙar hakan da cikakken ƙarfi.
Amma idan akwai mutum mai ingantaccen lasisi, horo da ƙwarewar aikin jinya, me zai hana a samar da tsarin da zai ba shi damar gudanar da wasu ayyukan da aka amince da su, ƙarƙashin tsauraran ƙa'idoji da kulawar hukumomin lafiya?
Kano jiha ce mai yawan jama'a, kuma har yanzu akwai wurare da dama da ba su da isassun cibiyoyin kiwon lafiya da za su iya biyan bukatun al'umma cikin sauƙi. Saboda haka, duk wata manufar kiwon lafiya da za a aiwatar a jihar ya kamata ta yi la'akari da ainihin yanayin rayuwar al'umma.
A ganina, mafita ba ita ce kawai a ce an haramta ba. Mafita ita ce a tsara tsarin, a tantance masu gudanar da aikin, a tabbatar da lasisi da ƙwarewa, sannan a samar da cikakken horo da sa ido.
Maimakon a rufe ƙofar da mutane da dama suka dogara da ita, ya kamata a gyara tsarin, a tsaftace shi, a tabbatar da cewa ƙwararru ne kawai ke gudanar da ayyukan da aka amince da su, sannan hukumomin lafiya su ƙara sa ido.
Don Allah, Gwamnatin Jihar Kano ta sake duba wannan mataki. Mu da muke rayuwa a cikin al'umma, musamman tsakanin talakawa, mun san irin taimakon da ake samu daga waɗannan wuraren. Abin da muke nema ba rashin tsari ba ne, illa tsari mai kyau da zai kare lafiyar jama'a tare da la'akari da halin da al'umma take ciki.
COMR. Comr Abubakar Ahmad Soja
Freedom Fighter
19/08/2026
This is our Faculty. Faculty of Computing and Mathematical Sciences. I am so proud to be a student of this great faculty.
Alhamdulillah, today marks the successful completion of our first semester at Level 200. I already miss my amazing coursemates the lectures, discussions, jokes, and moments we shared together.
May Allah bless our efforts and grant us excellent results. Ameen.
Ya Alllah ka cika min burina na ganin na kafa cibiyar koyarda "CRYPTOCURRENCY da FASAHAR ZAMANI ta BLOCKCHAIN" mai girma kuma mai tsari a yankin "AREWA" dama kasa baki daya, domin amfanar al’umma, wayar da kan matasa akan damarmakin da suke cikin blockchain, da yaɗa ilimin zamani.
Allāh ina roƙon ka cikin ƙanƙan da kai, tare da tawassuli da azumi da sauran kyawawan ibaduna.
Ina kuma roƙon duk masoyana da suka ji ko suka karanta wannan addu'a da su tuna dani cikin addu'o'insu, kuma su rubuta "Aameen" a comment section.
✍️ @DexEagleJr
RANAR FRIDAY ZAMU FARA JARRABAWA,📝 24/07/2026
Amincin Allah ya tabbata agareku Yan uwa da abokaina maza da mata Yau 17/07/2026 itace ranar dana ware wa kaina zan rage hawa online X (TWITTER), facebook da whatsapp da duk wani abu na social media, ina kara neman afuwar ku ina yiwa kowa fatan alkhairi Allah ya sake hadamu a nan gaba ko zamu sake haduwa, ina alfahari daku allah kuma ya sadamu da alkhairi,
✍️Comr. A² Soja
BSc. (Hons) Computer Science Student.
Darasi Ga Matashi
Idan kai matashi ne, ka mayar da hankali wajen gina kanka da cika burinka. Kada ka ɓata lokacinka kana ƙoƙarin burge mutane ko neman yardarsu, domin ba hakan ne zai canja rayuwarka ba.
Ka saka lokacinka, ƙoƙarinka da kuɗinka wajen ilimi, sana'a, kasuwanci ko wata fasaha da za ta amfani rayuwarka. Idan ka gina kanka, darajarka za ta ƙaru, kuma mutane za su fara girmama abin da kake yi.
Idan ka shiga soyayya, ka tabbatar an gina ta ne a kan mutunci, gaskiya da fahimtar juna, ba wai a kan kuɗi kaɗai ba. Soyayyar da aka kafa saboda kuɗi na iya fuskantar matsala idan kuɗin ya kare.
Ka daina jiran wani ya zo ya canja rayuwarka. Kai ne farkon wanda ya kamata ya ɗauki alhakin rayuwarsa. Ka yi amfani da damar da kake da ita, ka ci gaba da koyon sabbin abubuwa, kuma kada ka tsaya saboda wasu sun daina kula da kai.
Kada ka bari maganganun masu suka ko masu hassada su hana ka ci gaba. Ba kowa ne zai fahimci burinka ba, kuma ba dole ba ne kowa ya yarda da shi. Ka bari sakamakon aikinka ya zama amsar da za ka ba su.
Ka yarda da kanka, ka yi aiki cikin natsuwa, ka kasance mai haƙuri da juriya. Nasara tana zuwa ga masu ci gaba da tafiya duk da ƙalubale.
Ka tuna: Gina kanka shi ne mafi kyawun ramuwar gayya ga masu raina ka, kuma aiki tare da haƙuri shi ne mabuɗin samun nasara.
Young Comr. A-A SOJA
17/07/2026