Soyayya ta fi wahala ga namijin da ke son yin komai yadda ya kamata.
Namijin da yake da mutunci yana yawan tunanin kowane mataki da zai ɗauka.
Namijin da yake da aminci yana sa kansa sosai cikin alaƙar/soyayyar.
Namijin da yake da manufa yana yin taka-tsantsan fiye da kima don faranta mata.
A gefe guda kuma, namijin da ya fahimci yadda soyayyar mace take aiki, yana yin komai cikin natsuwa ba tare da fargaba ko tashin hankali ba.
Mazajen da suke daraja mutunci, ganin anyi daidaito, yawan tattaunawa da amincin gaske...
su ne sau da yawa suke fi shan wahala a zuciya.
Abin takaici shi ne, su ne suke ƙoƙarin yin komai daidai bisa adalci, amma a ƙarshe su ne aka fi yaudara.
Namiji nagari yana ɗaukar soyayya da muhimmanci.
Amma namijin da ya san darajarsa yana kallonta kamar wasa ne da ya san yadda ake buga shi.
Tsakanin waɗannan biyun akwai bambancin tunani mai girma.
Wani yana kwana da tunanin...
Me ya sa take min haka?
Me zan ce mata yanzu?
Ko ta canza ra'ayi ne?
Amma namijin gaske ya riga ya kwanta har ya fara baccinsa, ba tare da yayi tunanin komai ba.
Shi ya sa mazaje nagari suma a karshe suke ƙarewa su zama masu sanyi da rashin damuwa akan mata.
Domin idan mutum yana ba da kulawa sosai, yana ƙoƙari sosai, amma kullum abin da yake samu daga ɗayan ɓangaren kaɗan ne... a hankali hakan yana gajiyar da zuciya har ya karya mutum.
Neman soyayya a zamanin yau yana hukunta wanda yake ƙoƙari ne akanta.
Idan ka kasance wanda ake samunsa sosai?
A ce ka zama mai rauni.
Ka nuna kulawa sosai?
A ce ka cika roƙo.
Ka kasance mai aminci sosai?
A ce ka zama wanda ya daina burgesu.
Tsarin ya koma kamar komai a juye.
Mata suna ta tambaya....
Ina mazaje nagari?
Da yawa daga cikinsu har yanzu suna nan.
Sai dai sun riga sun janye daga wannan wasan, bayan an raunata su saboda ƙoƙarin yin komai yadda ya kamata.
Da yawa daga cikin mazajen da yanzu suke da babu ruwansu, sukayi nesa da mutane, kuma ba sa nuna damuwa, a da sun kasance samari masu zuciya mai taushi da son ayi adalci.
Amma irin abubuwan da suka fuskanta a soyayya ne suka koya musu su kashe wannan ɓangaren kirkin nasu.
Neman soyayya ba shi da wahala ga miyagun maza.
Amma yana wahala ga mazajen da har yanzu suka yi imani cewa ƙoƙarin da sukeyi a soyayyar dole ya kamata ya kasance yana da ma'ana.
Mata zasu rushe ka idan baka fahimce su ba.
Kana shirin lalata gabadaya rayuwarka
saboda mace.
Shiyasa Allah ya cire ta daga rayuwarka.
Wannan ba hukunci ba ne.
Rahama ce.
Kana jure wulaƙanci da rashin mutuntawa, cin amanar dokokinka, watsi da manufarka, hakuri da batun damuwarka, rasa kanka gaba daya, duk saboda yarinya da kuma abinda kake ji na motsin rai.
Wuri mai hatsari kenan ga namiji ya kasance.
Makale wa mutum yana sa maza su kashe ruhinsu.
Sai ka fara kiran, damuwa da so, fargaba da sha'awa, sha'awa da alaka, alhalin yanzu duk rayuwarka ta fara ruɓewa a hankali.
Kuna zaune a can
kuna rokon Allah ya bar muku ita...
yayin da Allah yake kokarin ceton ku DAGA gare ta.
Saboda maza cikin soyayya sun zama makafi.
Za su iya share alamun gargadi, tabbatar da rashin mutuntawa, soyayya da cin amana, watsi da gargaɗin da take musu, kawai don gujewa rasa damar shiga a gurin mace daya.
Gaskiya abin tausayi.
Wani lokaci Allah yana cire mace don kada ta dakatar da abin da kuke shirin
Ba kowace kyakkyawar mace ce aka aiko don ta albarkaci rayuwarka ba.
Wasu suna zuwa ne don su rusa ku.
Kuma bangaren da yafi muni?
Ba ka fahimta nan da nan.
Zakayi kuka amma.
Watanni bayan haka...
Zaka gane, magudi, wasannin kwaikwayo, rashin kwanciyar hankali da rashin mutuntawa
Sai kace...
Dama ashe Allah ya ceci rayuwata ne.
Mata za su lalata rayuwar ku idan ba ka fahimce su ba.
Ka sarrafa sha'awar ka...
Zaka ga halittar mata a yadda take.
Jima'i shi ne kawai abin da mata da yawa ke kawo wa teburin rayuwa.
Gaskiya mai daci kenan da ake tsoron fada muku.
Sha'awa tana makantar da maza a matse.
Halaye marasa daɗi suna zama na musamman yanzu, ba a ganin wulaƙanci da cin zarafi, kuma hirar banza ta zama abin da akafi yi.
Mugun maye.
Talakan namiji ba mata ba ne a zuciyarsa.
Yana da jaraba ne kan jima'i, yabo, kyau,
da kuma mafarkin karya.
Da zaran namiji ya mallaki sha'awarsa...
yana fara auna mata da samun kwanciyar hankali, tunaninta, aminci, da'a, natsowar zuciya, da kuma halayyarta.
Yanzu neman aure yana raguwa.
Wasu mata suna rayuwa ne gaba ɗa daya akan raunin sha'awar jima'i na maza.
Ka cire sha'awa...
Babu abin da ya rage sosai, bayan halin ko in kula da jarabar posting a manhajojin sadarwa.
Matan zamani suna kuskuren ɗaukar
sha'awar jima'i ta maza a matsayin kauna da gaske.
Yawancin maza kawai son saduwa suke yi.
Shi ke nan.
Dalilin da ya sa maza masu da'a suka zama masu wuyar burgewa?
Kyau kaɗai ya daina ruɗar hankalinsu.
Dole ta na buƙatar wani abu mai tushe da ma'ana.
Wata baiwa mai wuyar samu.
Namijin da ke da da'a kan sha'awarsa
yana da wahalar sarrafawa.
Domin a yanzu jarabar da wasu keyi ba ta sarrafa shawarwarinsa kuma.
Wannan shi ne ikon namijin gaske.
Yawan ikon da namiji ke da shi kan sha'awarsa... shi ne yawan adadin matan da dole su yi gasa kan KWANCIYAR HANKALINSA.
Sha'awa tana sa maza su bautawa mata a makance.
Kame kai yana sa maza su yi wa mata hukuncin gaskiya.
Kuma mata da yawa suna daina zama abin sha'awa da zarar rashin haƙuri da jarabar maza ta kare.
Mata za su lalata rayuwar ka idan ba ka fahimce su ba.
Ganin wata mace da ta taba bawa namiji kanta ta yi aure... abin dariya ne.
Shi yana mata kallon mata. Kai kuma kana tunawa da waccan daren da abin ya faru.
Abin sai ya zama kamar wani dukan kawo wuka.
Yana tsaye a wurin daurin aure, yana tunanin ya yi nasara. Amma kai kuma kana tunawa da kiranta tsakar dare, sakonni na banza, da kuma irin halayenta da BA ZAI TABA jin labarinsu ba.
Shi ya sa gogaggun maza suka daina bautawa mata. Saboda sun san komai domin da su matan suke bata dare, kuma da zaran ka ga abubuwa da yawa, za ka gane cewa, kusan kowace matar kwarai a baya ta taba yawo tana yin wasu abubuwan na rashin hankali.
Aure na gyara wa mace fasali.
Jiya, tana yawo duk karshen ƙarshen sati. Yau kuma ta zama matar aure mai natsuwa. Wannan ita ce babbar fasahar tallata hajar da ta fi komai mamaki wacce matan zamani ke amfani da ita.
Aure yana sauya LAKABI. Amma ba dole ya sauya HALAYYA ba. Wannan ita ce gaskiyar da mutane suka tsani su ji ta. Kuma shi ya sa wasu maza ke yi maka dariya a boye yayin da ake daurin aurenka. Saboda sun san cewa hoton da aka tallata maka da kuma gaskiyar abin da suka sani, fina-finai ne guda biyu daban-daban.
Soyayyar zamani ta koya wa maza gaskiya mai zafi guda daya. Kada ka taba bautawa mace kawai saboda ka sadu da ita a lokacin da take budurwa ta gari.
Mace wacce wani namiji ke kiraa, angel, mara laifi, ta taba zama wacce wani namiji ya tura mata sakon, ina jiran ki a dakina. Wannan fahimtar tana kawar da son zuciya da kuma daukar mace a matsayin wani abin bauta har na har abada. Kuma a'a, wannan ba tsana ba ce. Fahimtar abubuwa ce kawai. Gogaggun maza sun kawar da amincewa da abinda kai mutumin kirki baka iya gani.
Abin dariya a auren zamani?
Wani namiji na fadi cikin alfahari cewa ita tawa ce. Yayin da wani namijin a wani wuri yana dariya kan abubuwan da yake tunawa da ba zai taba fada masa ba. Duniyar nan ta lalace.
Mata za su rusa ka idan ba ka fahimce su ba.
Maza sun gaji da yin hakuri da rashin kokarinku. Ko dai ki nuna kokari sosai ko kuma ki rasa damar zama da shi.
Karshe kenan.
Babu sake yadda da kokarin karya da ba a gan a fito fili ba.
Babu sake cewa ya kakeso nayi.
Babu sake bayar da taimakon kalaman karya kyauta.
Mun gaji da cigaba da nuna muku cewa mu su waye.
Mun gaji da gyara marasa galihun cikinku.
Mun gaji da yin cinikin cikin girma da mutunci.
Zaman lafiya kadai....
Ya fi ayi ta hargitsi da wani....
Namijin da ke jin dadin zama shi kadai ba a iya sarrafa shi.
Ki so shi yadda ya kamata ko kuma ki kalli baya nan.
Ki rike abinki da kyau ko mu rabaki da shi.
Babu macen da maza ke amfani da ita su wurgar da ita kamar wacce take da kyau amma babu ƙwaƙwalwa.
Babu hankali, babu daraja, babu wata halayya mai kyau.
Kyau ba tare da hankali ba hatsari ne, kuma abin takaici, gabobin jikinta ne ke biyan duka bashin.
Ko dan karamin yaro kanyi ball da akwatin kayan da babu komai ciki babu shi.
Kyawawan jikin mace kadai ba su zama hujjar da za sa a daura aure ko ayi cikakkiyar huldar ba, su ƙari kawai suke, ba su ne ginshikan ba.
Idan kana tunanin gina dogon zango da abokin rayuwa, ba wai don sha'awa kawai ba, kana buƙatar fiye da kyau a gurin mace.
Ka nemi mace mai amfani da hankalinta, wacce ta horar da halayenta, mai azali a kan ingantattun dabi'u, mai nuna kamala ta mace, mai girmama jagorancin namiji, wacce ke fitar da kanta kunya, kuma ba ta tsammanin cewa kasancewarta wacce zata ja hankali yana nufin ta zama mai ilimi ko nasara.
Yawancin abin da ke kasuwar soyayya a yau kawai kyakkyawan shashanci ne.
Ba za ka iya yin zance mai ma'ana da su ba; ba su da alkibla kuma ba za su iya bayar da abin da ba su da shi ba.
Amma macen da ta yi aiki a kan kanta ta fuskar tunani, zuciya, ruhi, da kuɗi, ita ce ginshiki mai karfi.
Ba za ta saukar da ka'idodinta saboda wani yaro ba, amma za ta ba da komanta ga wani namiji da ya cancanci girmamawarta da amincinta.
Ka zabi mace mai daraja sama da waccan.
Ka bar wadannan matan da ba su da abin hannunsu wadanda ke da matsalolin gado da mummunan halin su kadai.
Ka nemo mace wacce take daidai da kai ko kuma wacce za ta kalubalanci cigabanka.
Ka daina tsoron matan da ke da matsayi da daraja, ba wai kana neman baiwa ba ne, kana neman abokin rayuwa ne.
Dalilin da ya sa kake ci gaba da zawarcin marasa tabbas da matan da ke bukatar taimako a kowane lokaci shi ne saboda ba ka tab girma gwargwadon yadda za ka tsaya kusa da mace mai karfin iko ba.
Ka gyara hakan.
Mata zasu rushe ka idan baka fahimce su ba.
Maza sun fara daina sha'awar soyayya. Ko ƙoƙarin yi ma ba sa yi.
Meyasa?
Ba wai don ba za su iya ba.
Ba wai don suna tsoro ba.
Amma sun gaji da...
Isa da jan aji mara ma'ana.
Rashin nuna wani ƙoƙari daga bangaren mata.
Buƙatu masu yawa ba tare da gamsassun dalilai ba.
Rashin ɗaukar alhakin kuskure
Sun ga yadda...
Zinace-zinace suka zama abin da aka saba da shi.
Aminci ya zama sai wanda aka zaɓa.
Alƙawari da kuma tsare mutunci suka zama abin dariya.
Sun ga an maida namiji kamar wani abu da za a rinka amfani da shi a wurgar da shi.
Sunga yadda auren yayi tsada
Sannan a hankali sun janye jikinsu.
Matsakaicin namiji a yanzu ba ya bin mata.
Abubuwan da yake bi a rayuwa yanzu su ne.
Kuɗi.
Zaman lafiya.
Lafiyar jiki.
Yanci.
Bacci mai daɗi da natsuwa.
Sau nawa zaka iya taɓa tukunyar wuta kafin ka daina taɓata?
Zafin yayi yawa.
Akwai radadi.
So Kake ka kone?
Halin ɗan adam kenan.
Babbar magana harkar soyayya a yanzu ba wai maza ne ke shan wuya wajen neman mata ba.
A'a, maza ne dai suka daina jin sha'awar matan.
Yawancin marasa aure ba wai sun fice daga harkar soyayya ba ne saboda sun gaza.
Sun fice ne saboda sun duba abin da soyayyar ke bayarwa da kuma abin da take ci musu a rayuwa.
Sun yi lissafi.
Ribar ba ta zo daidai da haɗarin da ke ciki ba.
Sun yanke shawarar zuba lokacinsu a wani wuri daban.
Ka nayi ƙarya in kaso.
Mata za su rusa ka idan ba ka fahimce su ba.
Lokacin da mace ta ci amana, ba ta jin tayi laifi a zuciyarta. Maimakon haka, sai ta yi fushi da namijin da ta ci amanar tasa.
Zata sake rubuta labarin gaba daya, har sai ta mai da kai matsayin mai laifi (mugu). A karshe, har ita da kanta sai ta yarda da karyar da ta kirkira. Wannan ba hauka bane, hanyar kare kanta ce.
Tana shiga tsoro da fargaba. Zuciyarta tana bugawa da sauri. Wataƙila ma ta iya yin kuka. Amma ba don ta ji zafin cutar da kai din da tayi ba ne, a'a, domin an kama ta ne. Wannan zafin kamun take ji.
Sannan kwakwalwarta zata fara kago wa kanta hujjoji kamar haka. Bai damu da ni ba, Dama ni ba dadin zama da shi nakeji ba, Mun kusa rabuwa. Daga nan sai jin laifin da tayi ya bace gaba daya, ta koma kan neman abubuwan da za su halasta mata abin da ta aikata.
Yanzu ba ita ce mai laifin cin amana ba. Ita ce wacce aka cutar, kai kuma kai ne namijin da ya tura ta ta aikata hakan, har an juya labarin. Dole ne ta nuna ta tsane ka domin ta samu damar yin barci da daddare.
Tana bincikowa dukkan kurakuranka. Muryarka.
Shirunka.
Aikinka.
Tana karkatar da komai har sai cin amanar da ta yi ya zama kamar abin da ya dace.
Wannan fushin ba adalci ba ne; kariya ce akan zuciyarta da emotion dinta.
Kada ka yi fada da shiryayyar karyarta. Kada ka biyo bayan neman cikakken bayani ko sulhu (closure). Kada ka gyara abin da ta riga ta kona. Kawai ka yi tafiyarka.
Mata za su halakar da kai idan ba ka fahimci su ba.
Babbar faduwa ga namiji ba talauci ba ne. Aure ne da wata mace mai hayaniya, wawiya wacce take ganin ita ce da gaskiya a kowane lokaci.
Wannan ba mata ba ce.
Wannan hukuncin daurin rai da rai ne.
Idan ka auri irin wannan matar, ba kai ba kara fafutukar neman soyayya. Sai dai Ka koma kana fafutukar kare hankalinka da zaman lafiyarka.
Ba zaka iya gina huldar alaka mai kyau da ita ba.
Sai dai ka gina filin yaki ne.
Ba sa sauraro.
Tana jayayya ne domin ta yi nasara, ba domin ta fahimta ba.
Manufarta ba ta warware matsala ba ce. Manufarta ita ce ta mallake ka (domination).
Ka yi kokarin lallashinta ko nuna mata aikin hankali?
Kai mai laushi ne sosai.
Ka yi shiru?
Ba ka damu ba.
Ka mayar da martani?
Yanzu kai ne mugu.
Babu nasara ta ko ina.
Tsira kawai ake yi da kyar.
Tana bukatar iko akan ka kamar yadda take bukatar iska don numfashi.
Duk wani sabani tafiya ce don nuna iko. Wannan ba soyayya ba ce.
Wannan yaki ne na tunani a cikin falon gidanka.
Za ta kwashe kulawar da kake da ita.
Ta kashe maka yarda da kanka.
Ta yi ta gaslighting din ka har sai ka yarda cewa kai ne matsalar.
Sannan ta zarge ka da mayar da martani ga hargitsin da ita ta kirkira.
Wannan ba mata ba ce.
Wannan hargitsi ne da da kyawawan labba a jikinsa.
Idan ka auri irin wanann matar, ba ka kara fafutukar neman soyayya. Sai dai kana fafutukar kare zaman lafiyarka ne.
Adana wannan sako ka kuma tura wa wani dan uwa da ke bukatar jin sa.
Mata za su halakar da kai idan ba ka fahimci su ba.