Tsohon Gwamnan Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, Danjuma Goje, ya musanta ficewa daga jam’iyyar APC, duk da cire sunansa daga jerin ‘yan takarar da INEC ta fitar na zaben 2027.
Domin karin bayani 👉https://t.co/zF6jAFlSId
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) da ta bayyana duk wani bayani da doka ta amince a fitarwa game da Shugaba Bola Tinubu.
Domin karin bayani 👉https://t.co/251HtYnJ6p
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Sarkin Rano, Mai Martaba Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Kano na shekarar 2027, domin jagorantar alhazai da kuma kula da ayyukan ibadar Hajji na jihar.
Domin karin bayani 👉https://t.co/ITgZVQRkpT
Manchester United ta fara kakar Premier League ta 2026/27 da kafar hagu, bayan da Hull City wadda ta dawo gasar Premier League ta doke ta da ci 2-0 a filin wasa MKM Stadium ranar Asabar.
Domin karin bayani 👉https://t.co/qk34JD0ZG4
Kawo yanzu sunan mawakin APC da kuma shugaba Bola Tinubu, Dauda Kahutu Rarara bai fito ba cikin kwamitin yakin neman tazarcen Tinubu a 2027.
Sai dai sunan Shugaban Hukumar Fina-finai ta Najeriya Ali Nuhu ya samu shiga.
Me ya sa kuke ganin sunan Rarara bai fito ba tukunna?
Daga yanzu mun fara tallar Tinubu - Yari
Darakta Janar na yakin neman zaben shugaban Najeriya Bola Tinubu wato Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar ya bayyana cewa ya karɓi naɗin da aka yi masa na zama Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC.
A cikin sanarwar da ya fitar a yau a Abuja, Yari ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabannin APC saboda amincewar da suka yi da shi yana mai cewa ba zai ɗauki wannan dama da wasa ba.
Ya ce yaƙin neman zaɓe ba wai neman ƙuri’u kaɗai ba ne, illa tattaunawa ce da ’yan Najeriya daga kowane yanki, kabila da addini kan makomar ƙasar da ake son ginawa tare.
A cewarsa, kwamitin zai gudanar da wannan tafiya ne bisa ladabi, haɗin kai da mutunta kowa.
Yari ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar da magoya bayanta a faɗin ƙasar nan da su fara aiki tun yanzu, yana mai cewa akwai gurbi ga kowa, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin siyasa ba.
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta karɓi alluran rigakafin Ebola na Ervebo guda 16,250, a wani mataki na ƙara ƙoƙarin dakile annobar da ta zama mafi muni a tarihin ƙasar.
Alluran da suka isa Kinshasa a daren Juma’a su ne na farko cikin 70,000 da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da abokan hulɗarta suka ware wa ƙasar.
Domin karin bayani 👉https://t.co/aEz453HhEP
'Yadda muka tsira daga kwale-kwalen da ya kife a Gorau na Sokoto'
Wasu daga cikin mutane da suka tsira daga kwale-kwalen da ya kife a kauyen Gorau na jihar Sokoto sun fada wa @ExplorerHausa yadda lamarin ya faru.
Ku kalli yadda ake zaman makoki a kauyen bayan faruwar iftila'in.
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki kan wasu al’ummomi a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja, inda suka yi garkuwa da dimbin mazauna yankin.
Rahoton ya ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a, lokacin da jama’a ke komawa gidajensu.
Domin karin bayani 👉https://t.co/V2lrHiNA8N
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce burinsa gabanin zaben 2027 shi ne kara matsin siyasa ga manyan ’yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi.
Wike ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja yayin da yake duba ayyukan raya birnin.
Domin karin bayani 👉https://t.co/skLuGdJCYd
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen sa, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai zama sakataren kwamitin.
Domin karin bayani 👉https://t.co/Of52qjakZb
Akalla yara biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon ruwan sama mai karfi da ya haddasa rushewar wani gini a yankin Gandun Sarki, karamar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.
Domin karin bayani 👉https://t.co/30OtmesbTh
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce yadda siyasar Najeriya ke sauyawa gabanin zaben 2027 ya sa zaben ke kama da wanda aka riga aka kammala.
Karin bayani 👉🔗 https://t.co/V0uQFjxYfC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta yi amfani da darussan zaben gwamnan Osun wajen shirye-shiryen babban zaben 2027.
Karin bayani 👉🔗 https://t.co/O0p7dt85Wo
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ta nemi wata kotun Amurka ta amince da ci gaba da boye wasu bayanan da suka shafi wani tsohon bincike da ake alakanta da Shugaba Bola Tinubu, tana mai cewa hakan ya zama dole domin kare hanyoyin binciken jami’an tsaro da kuma lafiyar wasu mutane.
Karin bayani 👉🔗 https://t.co/pbfGhC9VHG
Gwamnatin Najeriya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta 2026, a matsayin ranar hutun bikin Eid-ul-Maulud, wanda ake gudanarwa don tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hutun a madadin Gwamnatin Najeriya, cikin wata sanarwa da Babbar Sakatare ta ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar ranar Juma’a.
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya kare sabon tsarin tallafin man fetur da ya gabatar, yana mai zargin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da lalata tattalin arziki da kuma amfani da farfaganda wajen kare manufofinta.
An shiga zagaye na biyu na zaɓen sabon Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, yayin da wa’adin António Guterres zai ƙare a ƙarshen shekarar 2026. ‘Yan takara bakwai ne ke neman kujerar, amma har yanzu manyan ƙasashe masu ikon amfani da veto ba su bayyana wanda suke goyon baya ba.
Sanata Saliu Mustapha, wanda ke wakiltar Kwara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, yana mai cewa rikicin cikin gida da rashin dimokuradiyyar cikin gida sun sa ya ɗauki wannan mataki.