@Khady_Bamalli Zai karanta ne a asirce (sirri), ba a bayyane ba.
Dalili raka'ar da mutum zai yi bayan liman ana ɗaukarta a matsayin ƙarshen sallarsa. Kinga kuwa A Magriba raka'a ta uku ce ake karantawa a sirrance. Wannan shi ne mashahurin ra’ayi a mazhabar Imam Malik da kuma mafi yawan malamai.