Hadejia, historic kingdom and traditional emirate in northern Nigeria. According to the Hadejia Chronicle (1890s), the best-known native history of the Hausa people, the Hadejia kingdom was founded as one of the Hausa Bakwai(“Seven True Hausa States”).
GAISUWAR BARKA DA SALLAH
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya karɓi gaisuwar Barka da Sallah kamar yadda aka saba bisa al’adar Masarautar Hadejia.
27.05.2026
Ranar Arfa, Rana ce ta yawaita rahama, gafara da ‘yanta bayin Allah daga wuta.
Falalar Ranar Arfa
Annabi ﷺ ya ce babu ranar da Allah yake yawaita ‘yanta bayinsa daga wuta kamar ranar Arfa.
Yin azumin ranar Arfa ga wanda ba ya aikin Hajji yana da lada mai girma.
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje CON, ya karɓi baƙuncin Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Umar A. Namadi, FCA, bisa halarci sallar jana’izar Hajiya Barira Usman Ginsau, mahaifiyar Amb. Haruna Ginsau (Sardaunan Hadejia).
Allah ya jikan ta da Rahama
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya halarci bikin saukar Alƙur’ani mai girma na Makarantar Markazul Ulumul Qur’an Islamiyya Agumau, Hadejia, wanda ya ƙunshi ɗalibai mata (23), ’yan mata (12) da matan aure (11).
16/5/2026.
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya karɓi bakuncin sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Jigawa, Haruna Yahaya, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa a yau.
9th May, 2026
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya halarci bikin Kaman Kifi na Masarautar Hadejia da ake gudanarwa a garin Kalgwai, ƙaramar hukumar Auyo.
Bikin ya samu halartar Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, FCA, tare da sauran manyan baƙi
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji (Dr.) Adamu Abubakar Maje, CON, ya kaddamar da rabon tallafi ga marayu a Babban Masallacin Juma’a na Hadejia.
Yara marayu 1,260 sun amfana da kayan Sallah, an raba buhunan shinkafa 50 ga masu ƙaramin ƙarfi, tare da atamfa ga zawarawa 70.
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Adamu Abubakar Maje CON, ya halarci kaddamar da shirin Empowerment da Shugaban Rukunin Kamfanin Al-Yusra ya shirya, Matasan 708 sun amfana, an kuma bude masana’antar Recycling a Hadejia. Taron ya samu halartar Gwamna Umar Namadi, FCA. #Hadejia#Jigawa
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Adamu Abubakar Maje CON, ya halarci taron rabon Zakkar kuɗi har Naira Miliyan Saba’in (₦70,000,000) wanda Alhaji Muhammad Isma’il Ɗan Malele na Garin Gabas Tsohuwa ya bayar ga waɗanda Addinin Musulunci ya amince a ba su.
19.02.206
#DAY1 RAMADAN TAFSEER
Mai Martaba sarkin Hadejia Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje CON ya bude tafseer Al-qur'ani mai girma na watan Ramadan wanda Babban limamin Masallacin sarki Mallam Yusuf Abdulrahman Ya'u. Yake gabatarwa a Babban Masallacin Juma'a na Hadejia.
18.02.2026
Mai Martaba sarkin Hadejia Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje CON bisa umarnin Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi na umartar Al'ummar musulmai da Gobe Laraba 18th February, 2026 za a tashi da Azumin watan Ramadan.
Allah ya amsa ibadun mu na wannan wata mai Albarka🙏
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Dr. Adamu Maje, ya kaddamar da rabon Zakkah a Garin Inkaibo, Gundumar Jabo.
Rabon ya ƙunshi kayan amfanin gona, dabbobi da tsabar kuɗi da suka haura Naira miliyan 90, ga waɗanda suka cancanta a shari’ance.
Allah Ya Taimaki Sarki 🙏