Wannan addu’a ce da Annabi ﷺ ya koya wa Abubakar (R.A.) a ce da safe, da marece, da kuma lokacin da za a yi barci.
A cikinta ana neman tsari daga:
Tushen sharri biyu:
1. Sharri na kanka (nafsinka da ke umartar da mugunta)
2. Sharri na Shaidan da kuma shirk ɗinsa
Sakamakon sharri biyu:
1. Kada ka yi wa kanka mugunta
2. Kada ka yi wa wani Musulmi mugunta