Ayatullah Khamenei: Amurka da yahudawan sahyoniya za su gamu da kwakkwarar martani kan abin da suke aikatawa kan Iran da bangarorin gwagwarmaya.
#قطعاً_سننتصر#Israel#하이브불매#bbuk#SB19
DA DUMI-DUMI: Hadaddiyar Daular Larabawa ta kammala aikin gina manyan kejin ƙarfe da aka kewaye tankunan adana man fetur a Abu Dhabi, domin kare su daga hare-haren jirage marasa matuƙa na Iran, bayan shafe kusan watanni huɗu ana aikin.
https://t.co/zrZA9zBoag
Muhammad Baqir Qalibaf, Shugaban Majalisar Shura ta Musulunci ta Iran, ya mayar da martani kan barazanar Shugaban Amurka Donald Trump ga ƙasashen da ke ci gaba da hulɗar kasuwanci da tattalin arziki da Iran.
https://t.co/LENYQv4P4f
YANZU-YANZU: Sojojin mamaya na Isra’ila sun kai wani harin bam a yankin da ke tsakanin garuruwan Mais al-Jabal da Talusa, a kudancin Lebanon.
https://t.co/xIKwcXJiLc
Iran Ta Sauya Lissafin Ƙarfin Duniya, Inji Shugaban Basij
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Mobilization na Masu Rauni (Basij), Hussein Taib, ya ce: “A yau, taswirar ƙarfin duniya ta sauya, tare da Iran a matsayin ginshiƙinta.”
https://t.co/V5ujpPCaGx
Kasar Sin ta bayyana cewa takunkumin da aka kakabawa Iran ba shi da wani tasiri, kuma ba tare da izinin Majalisar Ɗinkin Duniya aka saka shi ba, takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ba shi da ingantaccen tushen doka.
https://t.co/Gt2fjXtiG2
Shugaban Kwamitin Neman Mutanen Iran da Suka ɓace ya ce: Wurin da ake tsare da matukan jiragen Iran a cikin teku ba shi da yanayin da ya dace da kiyaye lafiyarsu.
Ƙarin bayani 👇 👇
https://t.co/EdLkQkmZQf
An bayyana ta a 2020, aka gwada ta a atisayen “Manzo Maɗaukaki (SAWW) 16”, sannan a 2021 aka bai wa wasu rundunoni akalla guda 30 domin tallafa wa ƙungiyoyin sojojin ƙasa da kwamandoji.
“Su'ban”: Sabuwar Makamin Kwamandojin Iran
“Su'ban” bindiga ce mai sauƙin ɗauka da Rundunar Ƙasa ta IRGC ta ƙera, wadda ta samo asali daga Soviet RPD mai harsashi 7.62×39mm, tare da sabbin gyare-gyare da na’urorin hangen nesa.
https://t.co/p7Fm5PRMLx
A wannan makon, ma’aunin Brent ya ƙaru da kashi 6.39 cikin 100, yayin da ɗanyen man fetur mai sauƙi na Amurka ya ƙaru da kashi 5.66 cikin 100. Dukkaninsu sun kai matsayinsu mafi girma tun ranar 24 ga Yuli a zaman ciniki da ya gabata.
https://t.co/SGVwTMdpUq
An Karrrama Yaran Makarantar Minab da suka Yi Shahada a Yarin Baje-kolin Fasaha da ke Gudana a Pakistan Tare Da Bayyana Kima Da Darajar Al’adun Iran
Rahoto: Nasir Kazmi daga Rawalpindi. @PressTV
https://t.co/SPvLpeDWqh
Babu wata ƙasa da ke da ikon tilasta wa bankunan ƙasashen waje, kamfanoni ko filayen jiragen sama su daina gudanar da halastacciyar huldar kasuwanci da wata ƙasa ta uku, Cewar Baqaei
https://t.co/fh70lTysso #México#edrtwt#usa#iran#politics
Mu Horar da Zuciya Yin Afuwa 🎉
Mu horar da zuciyarka kan yin afuwa, mu bar ta ta kalli abubuwa ta fuskoki daban-daban, kuma mu nisanci mummunan zato! Domin tsarkin zuciya shi ne natsuwa, kyakkyawan zato kuma shi ne aminci.
ALLAH ya bamu ikon tsarkake zukatanmu!
#صباح_الخير
Rahotanni daga majiyoyin harkokin jiragen sama da tsarin bibiyar zirga-zirgar jirage sunce wani jirgin yaƙi na zamani kirar F-35, wanda ke da fasahar ɓoye kansa daga na’urorin gano jirage, ya aika da sakon neman agajin gaggawa yayin da yake shawagi a sararin UAE.
Rahotannin @theintercept sun ce korar shugabannin Sashen Leken Asiri na Sashen Iran na Mossad wani mataki ne da ba kasafai ake ganin irinsa ba, kuma yana nuna girman gazawar hukumar leken asirin Isra’ila wajen cimma manufofinta a kan Iran.
https://t.co/xzm23sjed5
🌿 Shin kun taɓa ganin bikin sauya tutar kubbar Haramin Imam Ridha (AS)? 🚩
Wannan wata al’ada ce da ake gudanarwa a Haramin Razawiyya Mai Tsarki, wato haramin Imam Ridha (AS), waje da anan ne Imamin shiriya na 8, Imam Ridha (AS) ke kwance.