Hanyoyi Huɗu (4) da ake samun kuɗi daga rike Stocks/Shares (Hannun Jari)
1️⃣ Capital Gains
Idan ka sayi share, sai darajarsa ta ƙaru, zaka samu riba.
Misali:
Ka saka ₦100,000
Farashin share = ₦5
Za ka samu shares 20,000
Idan farashin ya tashi zuwa ₦7.5
Darajar jarinka zai koma ₦150,000
Wato ka samu ribar ₦50,000
----------
2️⃣ Dividend
Kamfani tana iya raba wani kaso na ribarta ga masu rike da shares.
Ana yin wannan:
• Sau ɗaya a shekara
• Ko a quarter (wata uku)
Idan kana rike da shares kamar MTN, JAIZ, BUACEMEN, DANGOTECEM zaka rika samun wannan kudin.
--------
3️⃣ Bonus Shares
A wasu lokuta, kamfani tana bada shares kyauta ga masu rike da shares ɗinsu, doriya akan dividend.
Misali:
NAHCO ta bada 1 for 7 Bonus
Idan kana da shares 7, za a baka karin share 1 kyauta.
Wannan yana ƙara yawan shares ɗinka ba tare da ka ƙara kuɗi ba.
4️⃣ Rights Issue
Wato kamfani tana baka damar siyan ƙarin shares akan rangwame (discount) kafin sauran mutane.
Wannan ma babbar hanyar wealth building ce a NGX misali shi ne Dangote Sugar.
Me ka fahimta a wannan rubutun?
Idan kana da kuɗi da kake buƙatarsu cikin wata uku zuwa shida.
Kar ka sayi stocks da su kai tsaye.
A madadin haka ka sayi Mutual Funds.
Mutual Funds basket 🧺 ne na stocks masu yawa kuma HALAL wanda professional ke kula dasu.
Misali a cikin application na Cowrywise, akwai Naira Mutual Funds.
Idan ka shiga sai ka nemi: Halal Balanced Portfolio.
- A hoto na biyu, zaka ga wannan Mutual Fund yayi 45% daga farkon shekara zuwa yau.
Idan ka ajiye ₦100,000 yanzu ya koma ₦145,000.
Kuma wallahy HALAL stocks ake investing kuɗinka a ciki.
Ina fata kun fahimci wannan karatun?
Residents of Katai and Foda villages in Kano State have accused the police of acting unprofessionally during the operation. Lawmakers have also called for improved identification procedures during security operations. @StephenEnoch3 reports.