Majalisar Wakilan tayi wannan rokon ne bayan juyin mulkin da Sojin kasar Guinea Bissau suka yi, ya yin da lamarin ya ritsa da tsohon Shugaban Kasar ta Najeriya Goodluck Jonathan.
follow: MMC Hausa
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa ya rasu ne a daren jiya Laraba 26 ga watan Nuwambar 2025 Kuma za a yi jana'izarsa a gidansa dake jihar Bauchi.
Sheik Dahiru Usman Bauchi shahararran malamin addinin musulinci ne a Najeriya.
Allah ya jikansa da Rahama.
Majalisar mahaddata Al'qurani mai girma ta nada Bello Galadanci wanda aka fi sani da Dan Bello a matsayin sarkin yakin talakawan Najeriya.
Ya kuke ganin wannan nadi.
Tsohon ministan na sadarwa ya nuna jin dadinsa tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta karrama Nafisa da dala 100,000 da gida mai ɗakuna uku da kuma lambar girmamawa ta OON kamar yadda ta yi wa 'yan wasan tawagar Najeriya domin nuna muhimmancin ilimi da ɗaukaka darajarsa.
'Yar shekara 17 daga Jihar Yobe, Nafisa Abdullah Aminu, ta lashe gasar kwarewar harshen Ingilishi ta duniya a gasar TeenEagle Global Finals ta 2025 a Birtaniya.
Nafisa, ta wakilci Najeriya ta hanyar NTIC, Yobe, ta yi fice a cikin ɗalibai sama da 20,000 daga ƙasashe 69.
Shugaban kungiyar na kasa, Morakinyo Rilwan, ya bayyana cewa za su dakatar da ayyukan jinya gaba daya a asibitocin gwamnati, har da na gaggawa, har sai bukatunsu sun samu kulawa.
A cewar kungiyar, wannan ne karon farko da malaman jinya ke yajin aiki a Najeriya cikin shekara 40.