Shehu Sani ya yaba da batun jam'iyyar LP na cewa ƴan majalisunta ka da su karɓi motocin N160m.
Tsohon sanatan ya yi nuni da cewa kalaman na LP abun a yaba ne.
https://t.co/AcG8rKtKwA
Hotunan ɓarnar da harin da aka kai a asibitin Gaza ya yi wanda ya janyo mutuwar aƙalla mutum 500.
Har yanzu dai Isra'ila da yankin Falasɗinawa na zargin juna da aikata wannan harin yayin da hukumomi ke ci gaba da gudanar da bincike kan ainihin abin da ya faru.
Shugaba Tinubu ya faɗi hakan ne yayin ƙaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga magidanta miliyan 15, yayin bikin ranar kawo ƙarshen talauci ta duniya, wanda aka gudanar ranar Talata a Abuja.
Ƙarin bayani - https://t.co/6BClFNJaCg
Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda, ya ce zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kawo ƙarshen matsalar 'yan bindigar da suka addabi jiharsa
https://t.co/NPfJJL9B0v
Kotun ɗaukaka ƙarar da ke zama a Abuja ta ce akwai ƙuri'un da ba halastattu ba cikin waɗanda aka kaɗa wa Mista Abbo na jam'iyyar APC, bisa la'akari da Dokar Zaɓe ta 2022.
Ƙarin bayani - https://t.co/QBUy2SPrOb
A cikin wata hira ta musamman da BBC, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya lashi takobin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi jiharsa.
Za mu kawo muku cikakkiyar hirar a cikin makon nan.
Ƴan Najeriya sun yi martani kan yadda farashin siminti ke tashin gwauron zaɓi.
Hakan na zuwa ne bayan Dangote ya musanta rage farashin buhun siminti.
Tashin farashin simintin dai ba ya yi wa ƴan Najeriya daɗi.
https://t.co/vBA01rxg3J
Sashen Tantance Labaran Ƙarya na BBC ya yi bincike kan zarge-zargen cewa takardar kammala karatun digirin shugaban Najeriyar ta jabu ce, bayan Jami’ar Jihar Chicago (CSU) ta fitar da bayanan karatunsa a makon jiya.
Ƙarin bayani - https://t.co/tjIhpkk3dA