Akwai zalunci ace an kirkiri tokens
Ba'a san ta yanda mutane suka samo kudadensu ba an kawo musu sun shiga kawai daga karshe a zaluncesu a cinye musu kuɗi
Ba laifi bane kayi coin,
Amma laifi ne kacewa Mutane su shiga saboda wata manufa taka
Ba laifi bane ka tallata coin
Amma kuskure ne da mugunta kana ganin ana zaluntar mutane bazakayi magana ba
Babban zalunci shine kayi abu da gangar kuma kasan Allah yana kallo baya kyale duk wani azzalumi
Ni yanzu duk wanda ya cuceni a social media, KOTU ko DSS ne zasu zarabamu dashi kawai ba mutunci
SABON KARATU
ABUBUWAN DA YA KAMATA KA KIYAYE BAYAN KA KOYA TRADING
Rubuta na farko munyi bayani game da abubuwan da kake buƙata kafin ka fara trading
Yau zamu daura
Bayan ka koya trading, babban yaƙi yana farawa ne da sarrafa zuciya da bin ƙa'idoji.
Kasani (A Trading, kare jari shine mataki na farko, riba kuma sakamakon bin ƙa'idoji ne da kayi).
1. Kada Ka Yi Trading Da bin Zuciyarka,
Tsoro, kwaɗayi, da fushi suna daga cikin manyan abubuwan da ke sa trader ya yi kuskure ko asara, ka tabbatar Ka bi tsarin ka, ba zuciyar ka ba.
2. Kada Ka Yi Overtrading
Ba sai kullum kayi trading ba. mafi kyawun trade shine wanda baka shiga ba saboda babu ingantaccen setup.
3. Ka Riƙa Amfani Da Stop Loss
Stop Loss kariya ne ga jarinka. Duk trader da kaga yayi nasara yana kare jarinshi ne kafin ya yi tunanin riba.
4. Kada Ka Bi Kowane Signal Da Kake Gani daga wajan nutane
Kafin ka shiga kowani trade koda Signal ake baka, ka yi naka binciken. Kada ka dogara da bin signals ko maganar mutane kawai.
5. Kada Ka Yi Revenge Trading
Idan ka yi asara, kada ka shiga wani trade cikin gaggawa domin mayar da asarar. Wannan yana jawo ƙarin asara fiye da wanda kayi a farko, mafi yawanci.
6. Ka Rubuta Tarihin Trades Dinka
Ka riƙa rubuta:
Dalilin shiga trade
Wurin da ka shiga
Wurin Stop Loss
Wurin Take Profit
Sakamakon trade
Wannan zai taimaka maka gano kurakuranka hakan zaisa ka sama gyarawa cikin sauƙi.
7. Kada Ka Daina Koyo
Kasuwar trading tana canzawa koyaushe. Trader mai nasara shine wanda yake ci gaba da koyon sabbin dabaru da inganta tsofaffin dabarunsa, kana bukatar koyo saboda sabonta ilimi da dabaru.
8. Ka Kula Da Risk Management
Ko da setup ɗinka yana da ƙarfi, kada ka saka duk kuɗinka a trade ɗaya. Kare jari yafi neman riba muhimmanci.
9. Ka Guji FOMO
FOMO (Fear Of Missing Out) yana sa mutane shiga trade bayan farashi ya tashi sosai a lokaci daya, daga karshe kuma su fita a cikin asara babu shiri, zaifi kyau Ka jira damar da ta dace dakai maimakon bin kasuwa da gudu.
10. Ka Kasance Mai Ladabi Da Juriya
Nasara a trading ba ta zuwa cikin dare ɗaya. Masu nasara sun yi shekaru suna koyo, suna yin kuskure, sunayin asara, sannan suka gyara kuskurensu daga baya. Ka ba wa kanka lokaci, komai me wucewa ne, bayan wuya......
NOTE:
Trading ba caca ba ce, kuma ba hanyar arziki cikin dare ɗaya ba ce. Sana'a ce da ke buƙatar ilimi, haƙuri, ladabi, da bin ƙa'idoji. Idan ka mayar da hankali wajen kare jarinka da ci gaba da koyo, damar samun nasara zata ƙaru sosai a gare ka.
"A Trading, kare jari shine mataki na farko, riba kuma sakamakon bin ƙa'idoji ne da kayi".
LIKE, SHARE, COMMENT.
✍️ISMAIL IBN ABDULLAH✍️

ABUBUWAN DA MUTUM YAKE BUKATA KAFIN YA FARA KOYON TRADING
Mutane da yawa suna ganin trading hanya ce ta samun kuɗi cikin kankanin lokaci, Amma gaskiya ita ce, trading sana'a ce da ke buƙatar ilimi, haƙuri, da ladabi. Kafin ka fara koyon trading, akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata ka tanada.
1. Niyyar Koyo Ba Niyyar Arziki Cikin Dare Ba
Idan ka shiga trading da tunanin cewa zaka zama millionaire cikin kwanaki kaɗan, zaka iya shiga matsala. Ka shiga ne domin koyon sabuwar sana'a da gina ƙwarewa a hankali. Saboda idan ka shiga da gaggawa, kawai ka lissafa kanka cikin masu bada sadakar kudinsu ga market
2. Haƙuri
Trading ba abu bane da ake iya koya cikin rana ɗaya ko mako ɗaya. Yana buƙatar lokaci, gwaji, kuskure, da gyara. Mutum mai haƙuri yafi samun nasara fiye da mai son gaggawa, musamman ma a harkar trading
3.Wayar Hannu Ko Kwamfuta Mai Kyau
Kana buƙatar na'urar da zata baka damar ganin charts, yin bincike, da gudanar da trasing dinka cikin sauƙi.
4. Intanet Mai Kyau
Lallai kana bukatar network, Mummunar intanet na iya jawo maka matsala ko asara yayin shiga ko fita daga trade. Saboda haka ka tabbatar kana da ingantacciyar network.
5. Ilimin Asali Na Kasuwa
Kafin ka fara saka kuɗi, ka fara fahimtar abubuwa kamar:
Menene chart?
Menene banbancin strategies
Menene support da resistance?
Menene trend?
Menene stop loss da take profit?
Sanin Wadannan sune ginshiƙin trading.
6. Jari Da Zaka Iya Jure Rashinsa
Kada ka yi amfani da kuɗin
abinci,
haya,
makaranta,
ko kuɗin da kake buƙata cikin gaggawa. Ka yi amfani da kuɗin da idan ka rasa su, rayuwarka ba zata tsaya ba, kuma bakada damuwa.
7. Tsarin Koyo
Ka zaɓi hanya ɗaya ka bi ta. Kada yau kana kallon malami ɗaya, gobe wani daban, jibi kuma wani daban, yau kaga wancan strategy din kace zaka koya gobe ma kaga wani kace shi kakeso, Yawaita canza hanya yana rikitar da dan koyo.
Wadannan suke
Next zamu kawo abubuwan da zaka kauce mawa, bayan ka koya trading.
Like, share
✍️ISMAIL IBN ABDULLAH✍️
Duk wanda yaci kudinmu saiya biya.
Kamar yanda nake gani a wasu postings din
Duk abinda zakayi kuma duk abinda zakace kana buƙatar hujja, kowani lokaci magana batare da hujja ba
Tana alakanta mutun ya kasance daga cikin jahilai
Kada kai tsaye ka yanke hukunci, kawai saboda kaji wasu sun fada kokuma ance kace.
Wannan binciken nayishi ne domin tabbatar da zargi akan cewa, akwai wanda yaci kudinmu,
Idan kuma na tabbatar da hakan lallai bazan kyale kowaba kuma koma wanene, saboda zai kasance yaci amanarmu.
Bisa binciken da nayi game wallet address
"●#mP4tnNkwAtRLpSZG5CqcH3CVPJHgVw7XH3j6YRyayQP●"
Wacce ake tunanin cewa wata wallet ce ta mutun daya specific person wanda shine yake amfani da ita kai tsaye, wanda shi kanshi @SunusiMinjibir naga jiya ya wallafa hakan a shafinshi na X tare da tambaya akan me wannan wallet din.
A iya abinda na bincika shine, ita wannan wallet din ●#mP4tnNkwAtRLpSZG5CqcH3CVPJHgVw7XH3j6YRyayQP● batada alaka da mutum daya kai tsaye wajan gudanarwa, bata siyan token saidai ta siyar.
Domin, ita ce official fee collection wallet na https://t.co/Qqb7cZT73X
Dalili shine tanada alaka da transactions da ake gudanarwa tsakanin tokens wajen charges fees kokuma transactions fees na wannan token din daga https://t.co/RpDfETvjmb
Wannan ne ya sa idan ka duba tarihinta, za ka ga tana yawan sayar da tokens na projects da suka riga suka yi migration (graduation) daga https://t.co/Qqb7cZT73X
Yanda abun yake
Su https://t.co/RpDfETvjmb, suna karbar duk token daya kasance anyi transactions, da wannan token din suna tarawa idan yayi yawa saisu siyar su maidashi SOL
Idan kuka duba, zakuga ita wannan wallet din tana, rike da tokens wadanda bata riga ta siyarba tukunna, kimanin (5,000) wandanda darajarsu takai $20,621.64 a wannan lokacin,
Token kuma Wanda ta maida SOL a wannan lokacin shine ya kama (9.9 SOL) wanda darajashi takai ( $741)
Shine total value na wallet din ya kama ($21,363)
Sannan a yanda na fahimta https://t.co/RpDfETvjmb tana siyarwa ne tana maida wannan tokens din SOL Musamman idan taga wannan coin din yana sauka yana dumping
Wato idan coin yana tashi basa siyarwa saboda suna samun riba suma, sunga yana dumping sai su rinka fita a hankali a hankali idan charges fee ta taru.
Wannan normal aikine na system, kokuma bot
Abu na karshe daya tabbatar min da wannan binciken shine, ita wannan wallet #mP4tnNkwAtRLpSZG5CqcH3CVPJHgVw7XH3j6YRyayQP da ake zargi tana karba transactions a cikin kowani second da minti na agogo cikin hada hada take,
Sannan idan muka duba cikin wandannan hotunnan, zamuga cewa akwai coins din da da dama zakuga suna rike dasu Sannan sun siyarda wani kaso a ciki
Ciki harda token
$SUNUSI
$GAYU
$MAHUTA
Kamar yanda mutane suke tunanin cewa wannan wallet ce ta wani a zahirin gaskiya wannan ba haka bane.
Wannan shine kadan daga cikin abinda zan iya cewa a wannan lokacin,
Idan akwai gyara sai amin
Idan munga wani al'amari zamuci gaba da bincike
Kada ka dauki alhakin wanda be maka komaiba.
Barka da safiyar JUMA'AH
✍️ISMAIL IBN ABDULLAH✍️
@SunusiMinjibir@theafricanbulll
SABON KARATU
RISK MANAGEMENT
Yanda nakeyi shine
Wannan tsarin lissafina ne da nake amfani dashi a trading, kuma Alhamdulillah yana taimakamin sosai. Kowa ma zai iya amfani dashi gwargwadon capital ɗinsa.
Zamuyi Misali da $100 saboda kowa ya gane
RABA CAPITAL
1, Misali inada $100 zan rabata gida 5 ya zama $20 $20 kenan sau 5 Idan nayi haka na sama point na farko kenan
2, kowani trade idan zan shiga zan shiga da $20
3, kowace $20 ina tsara mata RISK MANAGEMENT nata na kanta
amma akwai sharudda da nake amfani dasu kafin shiga kowani trade
Gasunan kamar haka
i) _ina nemo coins masu karancin rashin hankali da rashin natsuwa (LOW VOLATILITY) COINS, ina neman masu saukin hawa da sauka wadanda basada high risk, ba wadanda zanje saka SL naga tun a karamin timframe kamar 15mins naga -20% SL wadanda ana karamin motsi zakaga anyi +5% -7%
Nasan duk trader ya gane irinsu kamar wani coin $XCX
Ina neman coins masu sauki wadanda a karmin TIMEFRAME har zuwa babban TIMEFRAME SL baya wuce 10% yayi yawan gaske kenan, irin wadannan coins din majority sune a whatchlist dina
ii) _duk trade idan har zan saka $20 dole saiya kasance risk dinda zanyi bazai wuce 5% ba $1 kenan matukar zan shiga trade naga SL dina ya wuce 5% yakai daga 6% har zuwa 10% to shikenan position size dina ya dawo $10
Misali ace 10% SL ya bani 10% na $10 kunga ya zama $1 kenan ya zama tayi balance
Kada ku manta capital dina $100 ne
iii) _wajan daukan TP kuma yanda nakeyi shine, idan har na shiga kowani coin target dina yana farawa karanci daga 1:3 zuwa 1:5 zuwa sama Misali idan na shiga trade SL ya bani 2% to dolene take profit dina ya fara daga 5 - 6% zuwa sama haka idan na shiga Wani SL ya bani 5% to lallai TP zan nema 12 - 15% zuwa sama matukar ban sama haka ba ina hakura da trade
iv) _ Sannan inada tsari wajan taking profit saboda bana wasa dashi, duk lokacin da na shiga coin, Misali Stop loss dina na sama 3% to lallai koda TP din ya bani 20% kuma na saita hakan indai nazo dubawa naga trade din ya bani 1:3 Wato 9% zuwa 10% to lallai fita nakeyi kai tsaye dukda wani lokaci ina matsar da SL amma nafi fita mostly saboda shine tsarina bana ganin profit na kyale.
<>_Duk wannan lissafin ya zama kenan idan har zan shiga trades guda 5 da kowace $20 kuma nayi loosing dukkansu 5 din da -5% a kowanne ya zama nayi loosing $5 kenan a trades guda 5 cikin $100 ya zama inada ragowar +$95 a trades biyar da nayi
<>_Sannan misali idan ya zama nayi winning trades guda 3 kowani trade na shiga da $20 kamar yanda na lissafa a baya kuma a kowani trade na sama 15% 15% guda biyu 10% guda daya cikin kowace $20 dana saka a kowani trade ya zama inada $8 kenan, still ina cikin profit kenan dukda nayi loosing 5 winning 2 zuwa 3
Da irin wannan risk management ɗin, zuwa yaushe za'ayi blowing account, idan ana bin discipline?
Har zuwa yaushe wannan $100 din zata kare kenan 🤔🤔🤔🤔
Me zakuce game da wannan lissafin nawa?
✍️ISMAIL IBN ABDULLAH✍️
Less than 48 hours since launch.
✅ Reached a $3.7M All-Time High
✅ Currently holding strong at $1.4M–$1.5M
✅ Over 10,800 organic holders and growing
solana:2vvw3cSwibzGD6SgW9QzRaBdmjkYrvs218DUy6VWpump
CA:
2vvw3cSwibzGD6SgW9QzRaBdmjkYrvs218DUy6VWpump
We’re not just building another meme coin, we’re setting a new standard.
We’re setting records.
And we’re aiming for a new ATH today.
Join the movement before the next leg up.