Al-Hadeeth
Manzon Allah SAW ya ce: Shahidai (kala) biyar ne: Wanda a ka soke shi har ya mutu, da wanda ciwon ciki ya kashe, da wanda ya nutse a ruwa ya mutu, da wanda gini ya ruso masa ya mutu, sai kuma wanda a ka kashe a wajen yaki.
Bukhari&Muslim.
Al-Hadeeth
Manzon Allah SAW ya ce: a cikin Aljannah a kwai wasu dakuna ana ganin waje daga ciki, ana ganin ciki daga waje, sai wani mutumin kauye ya mike ya ce: ya ma'aikin Allah na waye? Sai ya ce: na wanda ya kyautata magana ne, ya ciyar da abinci, ya dore da Azumi,
Al-Hadeeth
Manzon Allah SAW ya ce: Kalmomi biyu marasa nauyi a harshe, masu nauyi a sikeli (ranar kiyama) abun so a wajen Allah: SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI SUBHANALLAHIL AZEEM.
Bukhari&Muslim.
jawo hankali, karkatattu, kawunan su kamar tozon rakumi mai karkata, ba za su shiga Aljannah ba! kuma ba za su ji kanshin ta ba! duk da kanshin ta a na jiyo shi tun daga nisan kaza da kaza.
Muslim.
Al-Hadeeth
Manzon Allah SAW ya ce: wasu 'yan wuta iri biyu tukun ban gan su ba,
1- Mutane dauke da bulalu kamar jelar shanu (sabo da tsawo da kauri) su na dukan mutane da su,
2- da kuma mata sanye da tufafi amma tsirara suke, (sabo da tufafin ba na rufe tsiraici bane) masu