Bankin Duniya ya sanar da cewa zai bayar da dala miliyan 207 don tallafa wa samar da abinci a kasar Yaman da ke fama da matsalolin fatara da rashin aikin yi
https://t.co/37Nl7Lpfse
Mutane 39 ne suka rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta kama a wata cibiyar tsare bakin haure ta kasar #Mekziko da ke kusa da kan iyakar #Amurka
https://t.co/Dpp4zwzYZf
Burodin Vakfikebir, mai suna bayan gundumar Vakfikebir na Trabzon, birni mai tarihi a gabar tekun Bahar Maliya ta #Türkiye, abinci ne wanda ya samo asali daga al'adun yankin kuma ya shahara don yadda ake iya ajiye shi na dogon lokaci
https://t.co/L9iBRD1xmR
Bankin Duniya ya ba da rahoton cewa ana sa ran matsakaicin adadin ci gaban tattalin arzikin duniya zai ragu zuwa kashi 2.2 cikin 100 a tsakanin shekarar 2022 da 2030, adadi mafi karanci a cikin shekaru 30
https://t.co/A5RVXZZyBt
Ministan Harkokin Wajen kasar #Türkiye, Mevlut Cavusoglu ya tattauna da Ministan Harkokin Waje, Hadin Gwiwar Kasa da Kasa da Hadin Gwiwar Kasashen Afirka da 'Yan Kasar #Gini da ke Kasashen Waje, Morrisda Kouyate a Ankara, babban birnin kasar
https://t.co/3alx5Na5VH
Shugaban Majalisar Dokokin #Türkiye ya mayar da martani game da karbar bakuncin 'yan kungiyar ta'adda ta PKK/YPG a Majalisar Dattawan #Faransa tare da ba su lambobin yabo
https://t.co/qCfYhoaTJv
Masana suna ganin cewa idan muka tashi daga bacci, muna mantawa da kashi 50 cikin 100 na mafarkin da muka yi kuma bayan minti 10 muna mantawa da kashi 90 cikin 100
https://t.co/siBnj0rFFV
Ma'aikatar Tsaron #Rasha ta bayar da rahoton cewa #Yukren ta kai hari kan yankin Rasha da wani jirgin saman yaki mara matuki kirar Tu-141 Strizh
https://t.co/qq9B0su3gp
An aiyana dokar ta baci sakamakon guguwar da ta yi mummunar barna a jihar Mississippi da kewayenta tare da kashe mutane 26 a #Amurka
https://t.co/BJ1NrgQyNC