ABUBUWAN DA IDAN KA RAGE KO KA DAINA YIN SU ƘIMAR KA ZATA CIKA:
1. Rage yawan surutu
2. Idan baka tabbatar da gaskiyar lamari ba kada ka dorar
3. Ka damu da rayuwar ka fiye da wasu.
4. Ka guji bayyana sirrin ka
5. Ka rage zaton wai kowa sai ya fahimce ka.
Sai ka zauna lafiya
Babyna wannan shi ne sabon layina na WhatsApp.
Okay! Sweetyna!
Baby akwai matsala, don Allah ka turawa ƙaninka 10k zan aike shi.
Babu komai baby!
Alert ya shigo, na gode sosai sosai My Love. Dama ina so na gaya maka wani abu amma kar ka ji haushi don Allah.
Faɗi Babyna babu komai!
Ka yi haƙuri ba Baby ba ce Ƙaninka ne Auwalu, tun satin da ya wuce nake tambayarka kuɗin form na makaranta ka hana ni.
Na gode sosai sosai babyna au babynta 😜😘
- Sukairaj Hafiz Imam