It’s indeed an immeasurable honor to be called upon to serve, in whatever capacity, to ensure Abba Kabir and Asiwaju’s victory, Insha Allah. 🙏🏾
Congratulations to me, and other friends as well as colleagues that made the list. 🥳
At this point, people who are waiting for Tinubu to lose the 2027 elections are just wasting their time.
This is Bichi, Kano State.
This is supposed to be Kwankwaso’s strongest hold, and look at the huge numbers of people who came out in support of the APC. #ArewaForAsiwaju
The OK team will be sad this week as supporters of House of Representatives member Abubakar Kabir Bichi organised a rally in Bichi, Kano State, today. The rally was to galvanise support for Bichi, Governor Yusuf and President Tinubu. The crowd danced to Rarara’s song for the President.
Bichi Local Government Area in Kano State demonstrated its support for President Bola Ahmed Tinubu and the All Progressives Congress (APC) earlier today.
Na yi matuƙar baƙin ciki da mummunan hatsarin da ya faru ranar Juma'a a Ukubie, kusa da garin Oweikorogha, a Ƙaramar Hukumar Southern Ijaw da ke Jihar Bayelsa. A wannan hatsarin, wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mutane da dama ya kife, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka.
An ce waɗanda suka rasu masu ta'aziyya ne da ke kan hanyarsu ta zuwa jana'iza a garin da hatsarin ya faru.
Waɗanda suka rasa rayukansu a wannan bala'i ba su cancanci irin wannan mutuwa ba. Na umarci dukkan hukumomin agajin gaggawa na gwamnatin tarayya da abin ya shafa da su haɗa kai domin ganin an yi nasarar aikin ceto da lalubo waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Haka kuma, na ba da umarnin a gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓenmu na shugaban ƙasa a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, 2026, cikin nutsuwa ba tare da wani shagali ba. Mun yi haka ne domin girmama rayukan da aka rasa, da kuma nuna juyayi ga 'yan uwa da iyalan waɗanda bala'in ya shafa.
A madadin al'ummar Najeriya baki ɗaya, ina alhinin waɗanda suka rasa rayukansu a wannan hatsari. Ina kuma jajanta wa iyalansu, da gwamnati da kuma al'ummar Jihar Bayelsa.
Musamman, ina taya Gwamna Duoye Diri alhinin wannan lamari mai ban tausayi.
Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansu, Ya kuma ba iyalansu haƙurin jure wannan rashi.
Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunonin Soji
Jamhuriyar Tarayyar Najeriya
#ArewaforAsiwaju #A4A
Gwamnatin Tinubu ta hannun NEMA ta raba kayan agaji ga waɗanda zaftarewar ƙasa da zaizayar ƙasa suka shafa a Jihar Abia
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta hannun ofishinta da ke Owerri, ta ƙaddamar da rabon kayan agaji ga mutane da al'ummomin da zaftarewar ƙasa da zaizayar ƙasa suka shafa a Ƙananan Hukumomin Umuahia ta Arewa, Umuahia ta Kudu da Ohafia a Jihar Abia.
An gudanar da rabon ne ranar Juma'a, 20 ga watan Nuwamba, 2026, a Umuahia, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Abia (ABSEMA). Wannan na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kai ɗaukin jinƙai da kuma sauƙaƙa wahalhalun da iyalan da bala'o'in suka shafa ke fuskanta.
A wajen ƙaddamarwar, wakiliyar Babbar Daraktar NEMA, Zubaida Umar, ta isar da saƙon jaje daga Gwamnatin Tarayya da mahukuntan NEMA zuwa ga Gwamnatin Jihar Abia da al'ummomin da abin ya shafa.
Ta bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ce ta amince da bayar da kayan agajin ta hannun NEMA, domin rage raɗaɗin bala'o'in ga mutane da iyalan da abin ya shafa. Ta ce duk da cewa kayan ba za su iya maye gurbin dukiya da hanyoyin samun abincin da aka rasa gaba ɗaya ba, za su taimaka wajen rage wahala da matsin rayuwa ga iyalan da abin ya shafa. Kayan za su kuma ƙarfafa ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi.
Ta kuma buƙaci mazauna yankunan da su guji duk wasu ayyuka da ɗabi'un da ke cutar da muhalli, waɗanda ka iya ta'azzara zaftarewar ƙasa da zaizayar ƙasa. Ta jaddada muhimmancin kare muhalli da kuma ɗaukar matakan rage haɗarin bala'o'i a cikin al'umma.
A nasa jawabin, Sakataren Zartarwa na ABSEMA, Dakta Jackson Sunday, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar, ya gode wa Babbar Daraktar NEMA bisa yadda take ci gaba da tallafa wa al'ummomi masu rauni a Jihar Abia. Ya kuma yaba wa hukumar bisa ɗaukin da take kawowa a kan lokaci, da kuma yadda take amsa kiran jihar a duk lokacin da ta nemi taimako.
Da yake magana a madadin al'ummomin da suka amfana, Injiniya Ernest Otuonye ya gode wa Gwamnatin Tarayya ta Shugaba Tinubu da Gwamnatin Jihar Abia, musamman NEMA, bisa wannan tallafi. Ya bayyana tallafin a matsayin shaida da ke nuna yadda gwamnati ta damu da 'yan ƙasar da bala'o'in yanayi suka shafa.
Rabon kayan ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin agajin gaggawa na tarayya da na jihohi wajen biyan buƙatun waɗanda bala'o'i suka shafa. An kuma shawarci waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayan agajin yadda ya kamata domin biyan buƙatun gidajensu na gaggawa.
NEMA ta kuma sake jaddada buƙatar ci gaba da haɗin kai tsakanin hukumomin gwamnati, shugabannin al'umma da mazauna yankuna. Hakan zai taimaka wajen kula da muhalli yadda ya kamata, ƙarfafa shirin ko ta kwana kan bala'o'i, da kuma rage haɗarin aukuwar zaftarewar ƙasa da zaizayar ƙasa a nan gaba.
#ArewaforAsiwaju #A4A
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar APC da su tashi tsaye wajen tara goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar, Dr Jamilu Ishyaku Gwamna, da kuma sauran 'yan takarar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen APC da aka gudanar a garin Tula, hedikwatar Yankin Ci gaban Ƙaramar Hukumar Kaltungo ta Gabas (LCDA), inda ya gode wa al'ummar yankin bisa yadda suke ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa.
Gwamna Yahaya ya danganta ayyukan ci gaban da aka samu a faɗin jihar da goyon baya da jagorancin Shugaba Tinubu, yana mai cewa gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan da kowa ke gani a ƙasa, kuma al'umma ke cin moriyarsu. "Abin da muka yi a zahiri yake, na gaske ne, ba na fatar baki ba ne," in ji gwamnan, inda ya buƙaci jama'a da su yi amfani da ƙuri'unsu wajen saka wa irin ɗimbin ayyukan ci gaban da aka kawo musu a yankunansu.
Ya kuma yi kira ga masu kaɗa ƙuri'a da su mara wa 'yan takarar APC baya, yana mai jaddada cewa ci gaba da tafiya a kan turba ɗaya ta mulki ne zai ba da damar ɗorewar ayyukan da ake kan yi da kuma shirye-shiryen ci gaba.
A cewarsa, sake samun gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Dr Jamilu Gwamna zai ba da damar ɗorawa a kan harsashin da gwamnatinsa ta aza, tare da ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba a faɗin jihar. "Da aiki muka fara, kuma da aiki da ci gaba za mu kammala wa'adin mulkinmu. Idan aka sake samun gwamnatin APC ƙarƙashin Jamilu Gwamna, za ta ɗora daga inda muka tsaya," in ji shi.
A cikin ayyukan da aka gudanar yayin gangamin, Gwamna Yahaya ya ƙaddamar da aikin gina hanya mai tsawon kilomita huɗu da za ta haɗa yankunan Wange da Baule a Tula. Ana sa ran kammala aikin hanyar cikin watanni shida.
#ArewaforAsiwaju #A4A
Yanzu haka...
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya isa Bayelsa bisa umarnin Shugaba Tinubu kan mummunan hatsarin jirgin ruwa
Bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya isa Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa. Ya je ne domin yi wa gwamnati da al'ummar jihar ta'aziyya, musamman iyalan da suka rasa 'yan uwansu a mummunan hatsarin jirgin ruwan da ya auku ranar Juma'a a Ƙaramar Hukumar Southern Ijaw.
Da isarsa, Gwamna Douye Diri ne ya tarbe shi, tare da waɗannan:
• Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur (Ɓangaren Mai), Sanata Heineken Lokpobiri
• Manajan Daraktan Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Dakta Samuel Ogbuku
• Shugaban jam'iyyar APC na Jihar Bayelsa, Dakta Dennis Otiotio
• Manajan Daraktan Hukumar Raya Kogunan Neja Delta, Yarima Ebitimi Amgbare
Har ila yau, 'yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa da sauran manyan jami'an gwamnati sun halarci tarbar.
Mataimakin Shugaban Ƙasar na tare da Babbar Daraktar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da sauran manyan jami'an Gwamnatin Tarayya. Zai isar da ta'aziyya ta musamman daga Shugaba Tinubu ga iyalan waɗanda suka rasu. Haka kuma, zai samu bayanai kan yadda aikin ceto da lalubo waɗanda hatsarin ya rutsa da su ke gudana.
#ArewaforAsiwaju #A4A