🚨LABARI MAI ZAFI: Noni Madueke, Martin Ødegaard, Riccardo Calafiori da Jurrien Timber duk sun murmure kuma zasu shirya domin fuskantar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a ƙarshen makon nan. ✅
Jorginho ya bayyana dalilin barinsa Arsenal zuwa Flamengo:
“Ina son jin cewa ina da rai kuma INA DA MUHIMMANCI a cikin ƙungiya.” 😤
“Idan ɗan wasa baya cikin fili yana buga wasa, yana da wahala ya ci gaba da samun ƙwarin gwiwa. Na ji cewa ina buƙatar zuwa wani wuri da zan riƙa
Rahotanni sun bayyana cewa Luka Modrić ya gindaya sharudda uku ga AC Milan kafin ya sabunta kwantiraginsa wanda zai ƙare a watan Yuni, gabanin gasar kofin duniya:
🗣️🔥 Erling Haaland kan fuskantar William Saliba da Gabriel Magalhães:
“Yana kasancewa kamar yaƙi ne koyaushe. Sau da yawa suna kewaye ni da ‘yan wasa da yawa, wanda hakan ma yana da amfani a gare ni. Ba abu ne mai sauƙi ba yin wasa yayin da aka kewaye ka da mutane da yawa.
Barcelona na shirin fara tunkarar wakilan Julian Alvarez da Atletico Madrid domin mika musu tayi a hukumance nan da ƴan kwanaki masu zuwa.
Idan hakan bai faru ba, ko kuma ba'a cimma yarjejeniya ba, Saboda yuwuwar yarjejeniyar zata kasance mai rikitarwa, wasu daga cikin jami'an
A cewar Romain Molina, karsashi a filin ɗaukar horon Real Madrid ya ragu sosai tun bayan tafiyar Xabi, inda rahoton ya bayyana cewa wasu ƴan wasan sun mayar da filin atisayen kamar wani gurin shaƙatawar su. Shi kuwa Arbeloa ba shi da tasiri sosai a kan sauya hakan
Toni Kroos: “Bana fatan Atletico Madrid ta lashe gasar zakarun nahiyar Turai. Atletico Madrid ko Barca? Buri na duka su yi rashin nasara. Bayan shafe kusan shekaru 10 a Madrid, bana fatan ɗaya daga cikin su ya samu nasara. Bawai na tsane su ba ne, amma kun san yadda abun yake
Ahmed Musa zai mallaki kungiyar kwallon kafa ta Mighty Jets Fc da ke Jos, wanda aka kiyasta darajar ta akan kuɗi kusan Dala miliyan 10, dai dai da ₦13,412,800,000.00 (Naira Biliyan goma sha uku da miliyan dari hudu da goma sha biyu da naira dubu dari takwas) a kuɗin Najeriya.
Da ɗumi-ɗumi: FIFA ta yi watsi da ƙarar da Najeriya ta shigar da ƙasar DR.Congo kan amfani da ƴan wasan da basu cancanta a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya da suka fafata. ❌