I aspire to achieve success, not just for myself but to uplift my family and friends. I aim to spread kindness and positively impact my community while staying true to my faith. I look forward to the day I can help others, bring them joy, and alleviate their burdens. Until then..
Ondo a hotuna..
Komai ya tsaya cak a Akure.
Tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam'iyyar APC ta dira filin wasa na Township, kuma al'ummar jihar Ondo sun fito kwansu da kwarkwatarsu. Dattijai, matasa, mata da 'yan kasuwa. Zuciya ɗaya, murya ɗaya.
Ondo ta shirya tsaf. Tafiyar Renewed Hope na ci gaba.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Ga yadda aka tarbi Mataimakin Shugaban Ƙasa a Jihar Ondo.
A yau ne Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya sauka a Akure, babban birnin Jihar Ondo, domin halartar babban taron kamfen ɗin shugaban ƙasa na APC a filin wasa na Township da ke Akure.
Da saukarsa, Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya tarbe shi tare da manyan jami'an gwamnati, shugabannin APC da sauran manyan baƙi.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
DSS ta kama makamai 25 da harsasai 825 a Sokoto
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta samu nasarar cafke wani babban lodin makamai da ake zargin ana shigo da su Najeriya daga Jamhuriyar Nijar domin kai wa 'yan bindiga a Arewa maso Yamma.
An gudanar da aikin ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, a Dawakawa, Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.
A yayin aikin, DSS ta kwato bindigogin AK-47 guda 21, manyan bindigogin PKT guda huɗu da kuma harsasai guda 825. An kuma ruwaito cewa waɗanda ake zargi sun yi amfani da raƙuma wajen jigilar makaman ta hanyoyin da ba su da sauƙin sa ido.
Kwato waɗannan makamai na da muhimmanci wajen dakile hanyoyin samar da makamai ga 'yan bindiga, tare da rage karfin da suke da shi na kai hare-hare da barazana ga rayuka da dukiyoyin al'ummar Arewa maso Yamma.
Wannan nasara na nuna muhimmancin ayyukan leƙen asiri, sa ido kan iyakoki da haɗin gwiwar jami'an tsaro wajen dakile safarar makamai da dawo da zaman lafiya a yankin.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
From change to prosperity.
The APC’s 2027 policy document outlines a vision for progress and key goals to be achieved by 2031, along with figures and benchmarks to measure the successes achieved.
From security and the economy to job creation, improved electricity supply, education and healthcare, the overarching aim is to ensure that the changes being implemented lead to a better quality of life for Nigerians.
Watch to hear the full details of the APC’s 2027 policies.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Shugaba Tinubu ya ba 'yan wasan Flamingos kyautar Naira miliyan 100 kowacce
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba kowacce daga cikin 'yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya 'yan ƙasa da shekaru 17, wato Flamingos, kyautar takardar ajiyar kuɗin Gwamnatin Tarayya ta Naira miliyan 100, sakamakon nasarar da suka samu a gasar cin kofin duniya ta FIFA U-17 ta mata.
Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya ba babban kocin tawagar kyautar Naira miliyan 100, yayin da kowanne mamba na ma'aikatan fasaha ya samu Naira miliyan 50.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta sanar da kyaututtukan a wajen taron karrama tawagar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a madadin Shugaba Tinubu.
Flamingos ta kafa tarihi ta zama tawagar farko daga Afirka da ta lashe gasar FIFA U-17 ta mata, bayan ta doke Japan da ci 2–1 a wasan ƙarshe a Morocco.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Gwamnatin Shugaba Tinubu na ci gaba da ɗaukar matakan inganta rayuwar tsofaffin ma'aikata, tare da tabbatar da biyan fansho a kan lokaci da samar musu da ingantacciyar kulawar lafiya.
#ArewaForAsiwaju#A4A
Daga sauye-sauye zuwa wadata.
Kundin manufofin APC na 2027 ya bayyana alkiblar ci gaba da kuma muhimman manufofin da ake son cimmawa nan da shekarar 2031, tare da alkaluma da matakan da za a rika amfani da su wajen auna nasarorin da aka samu.
Daga tsaro da tattalin arziki zuwa samar da ayyukan yi, inganta wutar lantarki, ilimi da kiwon lafiya, babban buri shi ne tabbatar da cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa sun haifar da ingantacciyar rayuwa ga 'yan Najeriya.
Ku kalla domin jin cikakken bayani kan manufofin APC na 2027.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
There is a reason these Obidience guys hate @Omojuwa: he will not let them go scot-free with their propaganda and misinformation without fact-checking them.
@PeterObi, you’re a living example of what desperation and dishonesty are all about in Nigerian politics. Be honest even once in your life and campaign with facts and figures and what you have done while you were governor of Anambra State.
#ArewaForAsiwaju #A4A
@woye1@OgbeniDipo@FriendsOfBAT
"Za mu samar muku da wutar lantarki mai ɗorewa a Najeriya."
Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin samar da wutar lantarki mai ɗorewa a Najeriya, a gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC da aka gudanar yau a Jihar Jigawa.
#ArewaForAsiwaju#A4A
Shugaba Tinubu ga Atiku da Peter Obi: "...Kuna cewa za ku dawo da tallafin man fetur, ku maƙaryata ne. Ta yaya za ku biya kuɗin waɗannan alƙawura? Ta yaya za ku gyara hanyoyi, ku kuma kula da su? Ta yaya za ku tafiyar da gwamnati?..." - Shugaban Ƙasar Najeriya
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Duk wanda ya san kansa a Jigawa yana goyon bayan Shugaba Tinubu, har ma da Sule Lamido.
— Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a yau a taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Dutse, jihar Jigawa.
"NELFUND makamin mu ne na yaƙi da talauci, kuma duk kuɗin da EFCC ta ƙwato, yanzu ana tura su zuwa @NELFUND domin ilmantar da 'ƴaƴan mu..." - Shugaba Tinubu
#ArewaForAsiwaju#A4A
Wannan shi ne sabon hangen nesa na bunƙasa tattalin arzikin Najeriya!
A ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu, an fara ganin sauye-sauye a ɓangaren ma’adinai, musamman hakar lithium da sarrafa shi a cikin gida maimakon fitar da shi ɗanye zuwa kasashen waje.
Wannan mataki zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, jawo jarin masu zuba hannun jari, bunƙasa masana’antu da kuma ƙara darajar albarkatun ƙasa.
Ba wai kawai hakar ma’adinai muke bukata ba, har da sarrafa su a Najeriya domin amfanin ’yan Najeriya.
Wannan shi ne hanyar gina tattalin arziki mai ƙarfi da dogaro da kai.
Allah ya kara wa Shugaba Tinubu basira da ikon ci gaba da wannan tafiya ta ci gaban kasa.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Yadda dimbin mutane suka taru a filin wasa na Pa Ngele Oruta da ke birnin Abakaliki yayin da za a gudanar da kamfen na yakin neman zaben shugaba Tinubu a jihar Ebonyi.
#ArewaForAsiwaju#A4A
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya isa Kwali domin gudanar da taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Karamar Hukumar Kwali da ke Abuja.
Taron na da nufin tattauna matsalolin tsaro, bunƙasa ayyukan raya ƙasa a matakin ƙananan hukumomi, tare da ƙarfafa goyon bayan siyasa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya taimaka wajen magance matsalar wutar lantarki da jihar ke fuskanta, tare da jaddada cewa Ebonyi jiha ce ta APC.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai samu kashi 80% na ƙuri'un al'ummar jihar a zaɓen 2027.
#ArewaForAsiwaju
#A4A