Inna lil Laahi wa Inna ilaiHi Raaji'un!
Muna miƙa ta'aziyyar rasuwar Dan'uwa Mai daraja, Dr Ibrahim Muhammad Fadul Maiduguri (Imam Abuya) wanda Allah Ya dauki rayuwarsa a yau a garin Abuja.
Lalle wannan babban rashi ne gare mu. Dr Abuya mutum ne mai hakuri, da zumunci da juriya da yan'uwantaka. Muna mika ta'aziyyar mu zuwa ga iyalansa da yan'uwansa da aminansa da makwabtansa da almajiransa da masoyanmu.
Muna roƙon Allah Ya sanaya Aljannah ce makoma gare shi tare da iyayenmu da malamanmu da zurriyyarmu da aminanmu da yan'uwanmu da masoyanmu.