Mun samu kyakkyawar tarba daga al’ummar Danja, Kahutu, Dan Mai Gauta da Tsintsiya a ranar Alhamis, 24 ga Satumba 2026.
Mun kai ziyarar ta’aziyya da sada zumunci, inda muka jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwa, muka duba marasa lafiya, tare da ziyartar wasu daga cikin muhimman mutane a waɗannan garuruwa.
Muna matuƙar godiya da irin tarba, addu’o’i da goyon bayan da muka samu. Allah Ya saka da alheri, Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya ba marasa lafiya lafiya. 🤲🏽
Adade Anayi, Sai Gaskiya.
#VOTEGUGA2027
#VOTEGUGA4REPS🇳🇬
#BAKORIDANJA2027
#ABDULJABBARSURAJOGUGA
#ADADEANYISAIGASKIYA
A yau Laraba, 23-09-2026, Mun kai ziyara gidan marigayi Alh. Sani Liti Yankwani da ke Dutsen Reme domin mika ta’aziyyarmu ga iyalansa da ‘yan uwansa.
Marigayi Sani Liti Yankwani ya kasance dattijo mai kirki da mutunci. Ina rokon Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa, Ya kuma ba iyalansa da ‘yan uwansa hakurin jure wannan rashi.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa da sauran Musulmi baki daya. Amin 🙏
Abduljabbar Surajo Guga
PDP House of Reps Candidate
Bakori-Danja Federal Constituency 🇳🇬
Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji’un!!!
We are deeply saddened by the loss of our dear elder, mentor, champion, and hero of democracy, Hon. Sani Liti Yankwani Rasuwa.
Our hearts go out to his family and loved ones, praying that Allah forgives him, showers him with mercy, and grants him Jannatul Firdausi as his eternal home.
May Allah give strength and patience to everyone affected by this great loss.
Ameen ... 🙏
Abduljabbar Surajo Guga
PDP House of Reps Candidate
Bakori-Danja Federal Constituency
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Cikin alhini da jimami nake miƙa saƙon ta’aziyyata ga Malam Jamilu Halilu, da sauran ’yan uwa, abokan arziki da iyalan marigayiyar, bisa rasuwar mahaifiyarsa da ta riga mu gidan gaskiya.
Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan ta da rahama, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarta.
Allah Ya ba Malam Jamilu Halilu da sauran iyalai haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.
Abduljabbar Surajo Guga
PDP House of Reps Candidate
Bakori-Danja Federal Constituency🇳🇬
🗳️ Cast your ballot in the NEIS 2027 Civic Poll! Track real-time presidential & legislative results down to your polling unit: https://t.co/VqMNDVgwvq
🕌 SAƘON BARKA DA JUMA’A
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
Ina miƙa gaisuwar Barka da Juma’a ga al’ummar Bakori da Danja, da dukkan al’ummar musulmai baki ɗaya.
Ina roƙon Allah Ya sanya wannan Juma’a ta zama sanadin samun rahama, zaman lafiya, haɗin kai da albarka a gare mu da ƙasarmu baki daya, Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya yafe mana kurakuranmu, Ya biya mana buƙatunmu na alheri, sannan Ya ba mu ikon yin abin da zai amfani al’ummarmu. Ameeen.
Mu ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, zaman lafiya da kishin ci gaban Bakori-Danja.
Barka da Jumma’a daga:
Hon. Dr. Abduljabbar Surajo Guga
Ɗan Takara na Majalisar Tarayya, Bakori-Danja Federal Constituency
PDP
*Adade Anayi Sai Gaskiya*
#GUGA2027
#VOTEGUGA2027
#VOTEGUGA4REPS
#BAKORIDANJA2027
#ABDULJABBARGUGA
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN.
Cike da Alhini tare da Kaduwa nake Mika sakon ta'aziyata ga Iyalai da Yan'uwan Alh. Bishir Tuta Danja na rashinsa da muka yi.
Allah ya jikansa ya kai haske Kabarinsa, ya ba mu hakurin Rashin shi. Amin🙏
#GUGA2027#GUGA4REPS🇳🇬
#BAKORIDANJA2027
#ABDULJABBARSURAJOGUGA
#ADADEANYISAIGASKIYA
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
A madadin kaina, iyalaina da dukkan magoya bayana, muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga Shugaban Jam’iyyar PDP na Shiyyar Funtua Zone, Alh. Yahaya Dan-Uwa (Elder), bisa rasuwar ’yar uwarsa, Malam Jummai, wadda Allah ya yi wa rasuwa a yau, Talata 15 ga Satumba, 2026. Muna roƙon Allah ta’ala ya jiƙanta da rahama, ya gafarta mata kura-kuranta, ya sanya jinyar da ta yi ya zama kaffara ga zunubanta, Ya bai wa iyalanta da ’yan uwanta haƙurin jure wannan babban rashi amin.
Abduljabbar Surajo Guga
PDP House of Reps Candidate
Bakori-Danja Federal Constituency 🇳🇬
Sakon bangajiya da Fatan Alkhairi ga Yan'uwa Musulmi, mahalarta taron Maulidi na Matasa na Jihar Katsina da ya gabata a yau Asabar a Karamar Hukumar Danja. Ina yi ma kowa fatan ya koma gida lafiya, Allah ya kara hadin kan Musulmi da Musulunci baki daya.
...
We extend our warm wishes for the well-being of all Muslim youth and participants at the Maulidi event held today, Saturday, in Danja Local Government Area of Katsina State. May everyone return home safely. May Allah increase unity among Muslims and within Islam as a whole.
#GUGA2027
#VOTEGUGA2027
#VOTEGUGA4REPS
#BAKORIDANJA2027
#ABDULJABBARSURAJOGUGA
#ADADEANYISAIGASKIYA
Now it's up to us, WE the good people of Bakori da Danja! Allah Ya bamu nasara Kuma Ya bamu ikwon rike amanar juna. Allah Ya kara kawo mana zaman lafiya da kuma kawo cigaba mai albarka ga al ummar mu. 🙏✅️🗳🇳🇬✊️💯 #GUGA2027
Now it's up to us, WE the good people of Bakori da Danja! Allah Ya bamu nasara Kuma Ya bamu ikwon rike amanar juna. Allah Ya kara kawo mana zaman lafiya da kuma kawo cigaba mai albarka ga al ummar mu. 🙏✅️🗳🇳🇬✊️💯 #GUGA2027
Mun kai ziyara Guga, Kakumi, Kandarawa da Kabomo da wasu yankunan Jargaba domin jajanta wa al’ummar da hare-haren ’yan bindiga suka shafa tare da duba halin da suke ciki.
Abin da na gani ya taba zuciyata, musamman yadda wasu iyalai suka rasa matsugunansu, mata da ƙananan yara kuma suke gudun hijira. Duk da ƙalubalen tafiyar, na ji wajibi ne in je in jajanta musu.
Ina addu’ar Allah Ya kare al’ummarmu, Ya kubutar da waɗanda suke hannun ’yan bindiga, Ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya, Ya kuma kawo ƙarshen matsalar tsaro.
A Dade Ana Yi Sai Gaskiya.
#GUGA2027
#GUGA4REPS🇳🇬
#BAKORIDANJA2027
#ABDULJABBARSURAJOGUGA
#ADADEANYISAIGASKIYA