Ko kun san za ku iya samun kuɗi maƙudai da wayar hannun ku? 📱
Kasance mai bincike da ɗora (Content) a shafin ka ta hanyar tara mabiya wato (followers) domin samun rabo mai tsoka
Duk wani mai neman na kan sa sai ya hadu da qalu bale kala-kala, kama daga kan masu siyan kayan ka, masu yi maka aiki, ds
Wani lokacin ma sai kaji kamar ka haqura da sana’ar, to in ka haqura da ita kuma me za ka yi❓
Duk wata harkar nema cike take da qalubale.
Sau da yawa za ka dinga jin kalmomi kamar irin su AI, AR, VR, IOT, da dai sauran su, sai kaji kalmomin baqi kuma masu rudarwa.
Wadanne kalmomin IT ne suke rudar da kai/ke❓
Ina so mu saka a ran mu cewa babu wata nasara da za ka/ki samu a rayuwa ba tare da ka yi taking risk ba ⚠️
Idan har kana jin tsoron rashin nasara to fa ba za ka ci nasara ba, haka sunnar rayuwa take, a rashin gwaji ake barin dama.
Don haka mu dena jin tsoron gwada wani abu.
🌎Duniya kullum sai canjawa take yi, sababbin qirqire-qirqire 🦾🦿🤖sai fitowa su ke yi domin sauqaqa rayuwa.
Wane abu ne ka ke ta jira ku ga bature ya qirqira❓
Duk rintsi kar ka yarda ka zama mai alqalamin sharri ko qage, kar ka yarda ka yi rubutun da za kayi da na sani.
Watch what you post in social media for it shapes the world’s perception of you.
Haba Mallam mutane suna ta abin arziki amma kai kullum sai complain❓
Wannan complain din ka dakatar da shi, ka fara Sana’a komai kankantar ta, idan ba haka ba za ka wayi gari lokaci ⏱️ ya kure maka.
Allah ya raba mu da aikin da na sani🤲🏻
Hausawa suka ce wai Dama sau daya take zuwa a rayuwa. Amma wasu kam za ka ga suna ta samun damammaki da yawa sai dai kash❗️ haka damar za ta zo ta wuce ba tare da sun amfane ta ba⏱️
Ya Dan’uwa yi amfani da damar da ka samu a lokacin da ka same ta.
Wasu mutanen su dai Sun ji dadin su a rayuwa❗️ Sun zama katangar sukari, sun zama silar farin cikin wasu, sun zama indararon alheri, mutane suna alfahari da su wajen taimakon al’umma.
Wasu sun samar wa da wasu ayyukan yi, wasu sun bada jari ga matasa.
Wani lokacin sai kaga ba ka da ko sisi amma wani abu ya sa ka farin ciki da nishadi 😊 😃
Wani abu ne idan kana da shi kake jin dadi ko da baka da ko sisi❓
Za ka samu mutane da yawa suna da wani qudiri a cikin zuciyar su, amma sai kaji zuciya na raya musu cewa bari dai sai wani lokaci.
Lokacin na zuwa sai kaji kana cewa sai nan gaba, kafin ka yi aune sai kaji lokaci ya kure maka.
Ya kai Dan uwa kana da wani quduri da kake son cimma?