Hon. Auwal Aranposu Ya bayyana hakan ne yayin da yake mika sakon barka da sallah ga daukacin Al’ummar jihar Kano.
Wanda ya bayyana cewa yin gudun wuce sa’a a lokacin da mutun ke tuki na taka rawa wajen haifar da haddura akan titunan jihar Kano, wanda kuma tuni mai girma Gwamna Alh. Abba Kabir ya gyara tituna.
Aranposu ya bukaci Al’umma jihar Kano da su kasance masu bin dokoki, duba da yadda suka baza jami’an hukumar domin tabbatar da an bi dokokin hanya a yayin da ake gudanar da bukuwan sallah a fadin jihar Kano.
Daga bisani ya godewa AL’ummar jihar Kano bisa hadin kan da suke bawa hukumar wajen bin dokoki kamar yadda ya kamata.