If you were given $1 million, or your best friend was given $20 million, which would you choose? 🤔
A. Take the $1 million for yourself 💰
B. Let your best friend receive $20 million
No explanations, just pick one. 👇
Tausayi da jinƙai 🥹💔
Helen, mai shekara 91, da mijinta George, mai shekara 88, sun yi shekara 65 suna zaman aure cikin ƙauna da aminci.
George yana fama da matsananciyar cutar zuciya, kuma rayuwarsa ta dogara ne da shan magunguna a kullum. Wata rana inshorar lafiyarsu ta ƙare, sai kuɗin magungunansa ya tashi daga $50 zuwa $940 a wata.
Helen ta fahimci cewa idan mijinta bai samu waɗannan magunguna ba, rayuwarsa na cikin haɗari. Cikin tsananin damuwa da rashin mafita, ta ɗauki magungunan daga kantin sayar da magani ba tare da ta biya kuɗinsu ba.
Ba don tana son sata ba.
Ba don tana neman abin duniya ba.
Sai don ta yi ƙoƙarin ceton rayuwar mutumin da ta shafe shekaru 65 tana rayuwa tare da shi cikin ƙauna.
An kama ta aka kai ta kotu. Bayan Alƙali ya saurari cikakken bayani, sai ya nuna tausayi, ya ba da umarnin a dakatar da shari'ar tare da tabbatar an taimaka wa ma'auratan domin George ya samu magungunan da yake buƙata.
Wasu lokuta abin da muke gani a matsayin kuskure yana iya kasancewa sakamakon tsananin wahala ko rashin mafita. Wannan ba yana nufin sata ta halatta ba, amma yana tunatar da mu muhimmancin tausayi, taimakon mabukata, da nuna jinƙai ga masu cikin ƙunci.
Hakika, mata da dama suna da tausayi da sadaukarwa ga iyalansu.
Allah Ya kare mana iyalanmu, Ya ba marasa lafiya lafiya, Ya sanya tausayi da rahama a zukatanmu. Amin. 🤲❤️
Shetteeman Goronyo