Even with all the populist rhetoric, fiery tweets, look at the abysmal turnout Atiku campaign got in Bauchi state.
I had to zoom in to make sure it wasn’t a councilorship candidate, Those making money off this man’s dreams should be sued 🤦🏽♂️ Haba!
How the self crowned “King of the North” Atiku Abubakar was received in Azare
No street credibility
Rejected online
Rejected by Federal high court.
Don’t waste your votes #ArewaForAsiwaju
“I hope FCT is not part of the Northern states you're counting for Atiku. Even the 13 states he's claiming for Atiku are totally not correct. FCT is for the APC”
Wike has been pressing their necks nonstop. Lokaci Alƙali 😂 #ArewaForAsiwaju
Uwargidar Gwamnan Jihar Kebbi ta samu isowa ɗakin taron tattaunawa da shawarwari da mata masu ruwa da tsaki, tare da ƙaddamar da kwamitin mata na yaƙin neman zaɓen 2027.
Uwargidar Gwamnan Jihar Kebbi, Mai Girma Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris (Kauran Gwandu), tare da tawagarta sun samu isowa ɗakin taro da ke masaukin Shugaban Ƙasa domin tattaunawa da manyan mata masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a faɗin Jihar Kebbi, tare da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓe na kakar zaɓen 2027.
Wannan taro zai ba wa mata masu ruwa da tsaki damar bayyana ra’ayoyinsu, tattauna ƙalubalen da suke fuskanta tare da bayar da shawarwari masu ma’ana domin bunƙasa ƙarfafa mata da ci gabansu a Jihar Kebbi.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
NEMA ta tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa 653 a Kebbi
A ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba kayan agaji da na tallafa wa sana’o’i ga gidaje 653 da ambaliyar ruwa ta shekarar 2025 ta shafa a Jihar Kebbi.
An raba kayan abinci da na amfanin gida, tare da kayan tallafa wa sana’o’i kamar injinan ɗinki, injinan niƙa da babura masu ɗaukar kaya, domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa su farfaɗo da sana’o’insu da hanyoyin samun abin dogaro.
A sabon rahoton da NEMA ta fitar, hukumar ta bayyana cewa jimillar waɗanda suka amfana da shirin a jihohin Kebbi, Sokoto da Zamfara ta kai mutum 1,930, inda Kebbi ke da 653, Sokoto 652, sannan Zamfara 625.
Wannan shiri na musamman na Gwamnatin Tarayya na da manufar taimaka wa iyalan da ambaliyar ta shafa wajen farfaɗo da rayuwarsu, dawo da hanyoyin samun abin dogaro da kuma ƙarfafa juriyar al’umma bayan aukuwar ibtila’i.
#ArewaforAsiwaju #A4A
An gudanar da gangamin A4A a Birnin Kebbi gabanin ziyarar Shugaba Tinubu
Ana gudanar da gangamin Arewa for Asiwaju (A4A) a Birnin Kebbi, gabanin gangamin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da za a gudanar a jihar gobe.
Daga cikin waɗanda suka halarci gangamin akwai fitaccen mawaki Rarara da sauran jaruman masana'antar Kannywood.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta bayyana a shafinta na Facebook cewa tana tara mata domin shirin tarbar Mai Girma Shugaban Ƙasa da Uwargidarsa, waɗanda za su ziyarci Kebbi ranar Talata.
Ta ce ta ji daɗin ganin mata da aka naɗa a muƙamai, kansiloli mata, da kuma matan tsofaffin ciyamomi da kwamishinoni waɗanda ta yi aiki da su a lokacin mulkin maigidanta.
Ta kuma yi addu’ar Allah Ya sa a yi lafiya, a gama cikin nasara.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
2027: "...Gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaro a Najeriya, kasancewar shi ne abu na farko da ta fi ba muhimmanci a cikin manufofinta..." in ji Abdul'aziz Abubakar Yari, Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa
#ArewaforAsiwaju#A4A
A4A ta gana da al’ummar Musulmi a Jos, ta nemi goyon bayan wa’adin mulkin Tinubu na biyu.
Shugabannin ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A) sun yi kira ga al’ummar Musulmi da ke Jos, Jihar Plateau, da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a yunƙurinsa na neman wa’adin mulki na biyu, tare da bayyana cewa gwamnatin tana ƙoƙarin magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Da yake jawabi ga wasu zaɓaɓɓun shugabannin al’umma daga ƙaramar hukumar Jos North, Darakta Janar na ƙungiyar A4A, Mai Girma Mohammed Badaru Abubakar, ya nuna matuƙar godiya ga al’ummar yankin bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar APC tsawon shekaru.
Badaru ya tuna da irin goyon bayan da al’ummar Jos North suka bai wa Shugaba Tinubu a zaɓen 2023, inda ya buƙace su da su sake nuna irin wannan goyon baya a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu.
Ya bayyana cewa duk da ƙalubalen da gwamnatin Tinubu ke fuskanta, tana ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da suka daɗe suna addabar ƙasar.
A nasa jawabin, tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Ahmed Wase, ya gode wa al’ummar Jos North bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar APC, tare da kira gare su da su fifita muradun al’umma gaba ɗaya a kan na kashin kai yayin yanke shawarar da ta shafi zaɓe mai zuwa.
Taron, wanda ya samu halartar manyan mutane, ya haɗa da shugabannin Babban Masallacin Jos, ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), Jos Development Association, Jama’atu Izalatul Bidi’a, Jos Renaissance Group da sauran ƙungiyoyi.
A nasu jawaban, shugaban al’ummar Hausawa da Fulani na Jos, Alhaji Sani Mudi, da Babban Limamin Jos, Sheikh Ghazali Ismail Adam, sun jaddada dangantakar da ke tsakanin al’ummar Jos da jam’iyyar APC tun lokacin da aka kafa ta.
Sun kuma yaba da ci gaban da aka samu wajen tabbatar da zaman lafiya da tattaunawa a jihar, inda suka danganta hakan da ƙoƙarin Shugaba Tinubu da Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Muftwang, na bunƙasa haɗin kai da zaman lafiya tsakanin al’umma.
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Lokacin da na zo Jihar Filato a baya, ban wuce filin jirgin sama ba. Ku yafe ni idan ba ku gan ni a cikin karkara ba, amma na ga irin ɓarnar da aka yi, na karɓi rahoto daga gwamna, na kuma ga firgicin da ke fuskokin jama'armu. Amma tun daga wancan lokaci, abubuwa sun sauya; muna ci gaba tare. Ina tabbatar wa waɗanda aka raba da muhallansu cewa za mu sake gina garuruwanku, mu kuma mayar da ku can.
Shugaba Tinubu ne ya faɗi haka a yau a gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a Jihar Filato
#ArewaforAsiwaju #A4A
PRESIDENT TINUBU HEALTH REFORMS RECORD GAINS AS 16.6 MILLION CHILDREN FULLY IMMUNISED, MALARIA PREVALENCE FALLS
- The Executive Director of the National Primary Health Care Development Agency (NPHCDA), Dr Muyi Aina, disclosed that 16.6 million children had been fully immunised, exceeding the project's target of 9.3 million.
- The proportion of fully immunised children aged 12–23 months increased from 31% to 39.7%, surpassing the project's 36% target.
- Malaria prevalence among children aged 6–59 months fell from 22% in 2021 to 15.2% in 2025, reflecting progress in prevention, diagnosis and treatment.
- Under-five mortality declined from 102 to 90 deaths per 1,000 live births, according to figures presented by NPHCDA.
- The project supported improvements to over 2,500 primary healthcare facilities across 30 states and the Federal Capital Territory, strengthening access to essential health services.