Ya tsaya a gaban wata Budurwa tana ɗiban ruwa a Rijiya a wani ƙauye, ya ce, baiwar Allah me ake nufi da KAIDIN mata..!?
Matar nan ta ƙwallo ihu da ƙarfi sosai, har mutanen ƙauyen nan suka jiyota. Suka nufo in d take ɗauke da makamai.
Cikin tsoro ya ce, baiwar Allah ya zaki yi haka, nifa tambaya kawai na yi...!!
Ta ce, so nake in suka ƙaraso su kashe ka, domin k zo da niyyar cutar da ni. Ya yi ta rantsuwa akan ba shi da niyyar cutar da ita..!
Sai ta ɗau ruwan Tulun ta jiƙe jikinta, shi ma ta jiƙa shi jalab. Ko da mutanen ƙauyen suka ƙaraso, sai ta ce, Rijiya na faɗa wannan mutumin ya kubutar d ni.
Mutanen ƙauyen nan suka rinƙa yi masa godiya, su ka karrama shi sosai, suka ba shi kyaututtuka..!
Ya tambayeta, menene hikimar abin da kika aikata?
Ta ce, haka KAIDIN MACE, in ka cutar da ita; sai ta mayar da rayuwarka kamar Jahannama. Idan kuma ka kyautata mata, haƙiƙa sai ta mayar da kai kamar ɗan Aljanna.
- Sukairaj Hafiz Imam
Choosing a partner is one of the most important decisions you’ll ever make. The right person brings peace, growth, and purpose. The wrong one can cost you your confidence, your dreams, and years you’ll never get back. Choose character over chemistry. Peace over pressure. Wisdom over emotions.
Aisha Ahmad Rufai secretary board of interior,wacce ta bawa matasa aiki,A kallah mutum 500 from 2018 to 2022, kama da immigrations,civil defense,fire service.Hakika Muna bukatar irinsu a cikin alummarmu.Allah ya jikanta da Rahmarshi Aamin.
Dr. Musbahu Mohammed Bashir, a Kano-based businessman received ₦451 million in dividends from JAIZ Bank.
He is the owner and founder of Althani Investment Limited, one of Jaiz Bank's largest shareholders.
MATAKIN DA ZAKA DAUKA TSAKANIN KA DA MAI YI MAKA HASSADA DA KIYAYYA:
1. Ka daina fallasa masa sirrin rayuwarka a fili. Ka zama mai wuyar ganewa da fuskanta a gareshi, rashin sanin takunka zai haukata tunanin sa ya dakile kullin sa a gareka .
2. In kun hadu ka nuna natsuwa da Rashin damuwana a aikin ka da harshen ka. In ta kama kana ce masa *"Babu damuwa ko kaɗan, ka kula da kanka."* Kana kamewa, Shirunka zai zame masa jidali ya wargaza masa masa lissafi ya kasa gane Ina ka dosa.. hakan zai barshi cikin damuwa yana nadamar nasarar ka
3. In abin nasa yayi yawa ko sau daya ka faɗi wannan jimlar, sannan ka ɓace ɓat "Ban tsammaci hakan daga gare ka ba. Amma na riga na ɗauki darasi." Wannan magana za ta dade a zuciyarsa, Kuma zata taka Masa burki kadan.
4. Kada kayi hayaniya ko fada dashi. Kada ka toshe shi a kafafen sada zumunta; ka bar shi yayi ta aiko da saƙoni kana gane irin tunanin sa akan ka. Kai dai in ya aiko sako ka karanta ka bar shi haka ba tare da ka ba da amsa ba.
5. Kana neman taimakon Allah akan ya tsare ka daga sharrin zuciyar sa, ya kareka daga makircin kiyayyar sa. Allah ya isar maka akan cutarwar da yake yi maka, Allah ya mayar masa da kaidin sa gareshi
- Shiekh Aliyu Said Gamawa