Kwararru a fannin kimiyyar sadarwa da kuma fannin lafiya sun karyata batun da ake yadawa cewa tsarin sadarwar salula mai saurin gaske ta 5G na haddasa cutar #coronavirus. #FACTCHECK#COVID19#Corona#CoronaVirusInNigeria https://t.co/dn9oegLNfF
Yayinda cutar #Coronavirus ke ci gaba da yaduwa, mutane da dama na ci gaba da yada bayanan karya kan cigar. Ga misali, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa Cizon sauro ba ya sanyawa a kamu da cutar Coronavirus kamar yadda wasu ke yadawa: https://t.co/Vv0QxXBzkx #Corona
Labaran boge da suka fi tayar da kura a 2019: Shekarar 2019 na sahun gaba a jerin shekarun da suka wahalar da masu fafutukar yaki da labaran karya musamman saboda wasu manyan abubuwa da suka faru a cikinta a ciki da wajen Najeriya.
https://t.co/ki4ruADe44 #fakenews#FactCheck
Kwararru a fannin yaki da labaran boge na ci gaba da yin karin haske kan yadda masu yada labaran karya ke kara bullo da sabbin dabaru, wanda suka hada da cakuda karya da gaskiya: https://t.co/sNYkQxkOHn #FakeNews#FactCheck#misinformation#karya
Kure-karya: Da gaske an kafa ‘Ma’ikatar biyan albashi da wuri’ a #Gombe? Daga dukkan alamu an sarrafa hoton ne ta hanyar amfani da daya daga cikin manhajojin sarrafa hotuna. Hakan ya tilasta wa gwamnatin jihar yin karin bayani game da lamarin: https://t.co/v4yN2GtkY1
Mutane da dama ne ke yada wani rahoto da ke cewa hukumomi a #Dubai na UAE na saka ido kan Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin Najeriya karkashin #PDP a zaben 2019, bisa zargin ta’addanci, sai dai binciken Bindiddigi ya gano rashin gaskiyar labarin: https://t.co/t8R3oFHRxM
Kure karya: Mutane da dama sun yada hoton wani dattijo a kan gadon marasa lafiya a asibiti, wanda suka yi ikirarin cewa gwamnan jihar Kano ne Abdullahi Umar Ganduje. https://t.co/04cGKcUG4I
Wata makala da aka yada sau sama da 3,000 a Facebook da Twitter ta yi ikirarin cewa Firaministan kasar Canada Justin Trudeau ya roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya tura ‘yan ci-rani miliyan daya daga Najeriya zuwa kasarsa. https://t.co/99AcP0xGxh
Dubban mutane ne suka yada wani bidiyo da ke dauke da hoton gwaman jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai yana maganar cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana da masaniya kan wadanda ke kai hara-hare a jihar Zamfara. https://t.co/IRIbFRZHum
Kure-karya: El-Rufai bai soki Buhari kan rikicin Zamfara ba? Dubban mutane ne suka yada wani bidiyon gwamna Nasir el-Rufai yana cewa Shugaba Buhari ya san masu kai hare-hare Zamfara. Sai dai bidiyon na shekarar 2013 ne kuma ba da Buhari @elrufai yake ba: https://t.co/m72xpY5n2i
Shin Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya fadi gaskiya kan saukar farashin taki zuwa 5,500?
Mun bi biddigin kalaman na Mataimakin shugaban Najeriya domin tabbatar da gaskiyarsu ko akasin haka: https://t.co/YmnrCsyIVY
Wasu hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta dauke da wasu sakonnin talla like a jikin manyan motocin bas a birnin Landan wadanda ke kira da a garkame Bukola Saraki a gidan yari ba na gaskiya ba ne: https://t.co/mqPz2IfdqA #FakeNews#FactCheck#NigeriaDecides#London
Bincike ya gano cewa, wani bidiyo ya bulla a Facebook kwanakin baya da ke nuna fasinjoji a cikin wani jirgin sama cikin firgici kuma sanye da takunkumin shakar iskar oxygen, ba na jirgin saman #Ethiopian Airlines samfurin 737 Max 8 da ya yi hatsari ba ne: https://t.co/GdKYdCO7EV
Shafin #Facebook na kamfanin jaridar Nigerian Tribune ya wallafa kanun labari cewa: “Da Dumi-dumi: Babban Bankin kasa #CBN ya haramta shigowa da atamfofi da yaduka”, sai dai binocike ya nuna labarin ba haka ba ne: https://t.co/kARyYZHa4a #FakeNews#FactCheck#Textiles#Nigeria
Wasu ma’abota shafukan sada zumunta musamman #Whatsapp na ci gaba da yada wani sakamakon zaben gwamnan jihar #Ogun na bogi wanda ya nuna cewa ya kamata zaben gwamna a jihar Ogun ya zama ba cikakke ba:https://t.co/ZqjAd7K4td #nigeriadecides#nigeria#INEC#Nigeria#inconclusive
Babu gaskiya a wasu labaran da aka yada cewa tsohon shugaban Najeriya Olusegun #Obasanjo ya arce daga kasar bayan hukumar zaben kasar #INEC ta sanar da cewa Shugaba Muhammadu #Buhari ne ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar: https://t.co/hn4QwOyqg0 #NigeriaDecides