Original pure honey 🍯🍯 available for pickup and delivery nationwide
Price range: 2L 13k
1L 6500
Half litre 3500
Small container: 1000
Big container: 1500
Those that want 20L and 25L too it's available
Location: Mando kaduna
Kindly retweet for me jazakumullahu khair
Idan ka tashi Aure karkace kai lallai iya Genotype da HIV zaku yi, yanada kuyi duk wani pre-marital test wanda ya kamata. Wasu suna gujewa kashe kudi sai su ce a musu iya Genotype da HIV, yin hakan akwai matsala musamman ga Mace koda baida complete kudi a hannun shi yakamata ki cika masa domin kusan status dinku
Babbar barazanar rashin yin hakan akwai Blood Group a ciki, misali ka Aure Macen da Blood Group dinta 0-Negative kai kuma sai naka yazo 0+Positive baku sani ba. Wannan shine babban tashin hankalin da ake kira "Rhesus incompatibility"
Barazanar da zaku fara fuskanta itace lokacin da Matarka ta samu ciki, Mace mai Blood Group O-Negative idan ta Aure Miji mai Positive kamar O+, A+, B+, ko AB+, akwai yuwuwar jaririn dake cikintq ya kasance mai Positive kamar mahaifinsa
Inda matsalar take shine, ita Matarka Negative ce, idan yaron jinin shi ya zama Positive jikin uwarshi zai dauki jinin yaron a matsayin foreign object ma'ana bakon abu haka zai saka Anti-bodies din jikin Matarka su kaiwa jaririnta farmaki
Kunsan meye dalilin daya saka zaku ga wasu Matan suna yawan zubar da ciki, suna yawan bari, suna yawon haifan yaro a Mace, suna yawan haifan yara da cutar sanyi wanda ake kira da jaundice, ko a haifa yaron da zai dinga zama kusan ko wani lokaci da cutar karancin jini na Anemia?
Wannan dalilin ya saka idan Mace tana yawan fuskantar irin wannan matsalar inhar ba'a gano dalilin ba sai a dinga cewa Mayu ne suka Shane mata jini, ko ace mayu ne suke kashe mata yaron saboda yawan zubar da ciki da yawon haifan macaccen yaro ko yaro mai dauke da Anemia
Babban tashin hankalin na biyu a lokacin da Mace ta samu ciki shine, su mutane masu 0-Negative suna iya baiwa kowa jinin su amma su ba kowa bane yake iya basu jini sai mau irin nasu sai yasa ake kiransu da Universal Donors
A cikin mutane 100% kaso 7-8% ne kacal masu 0-Negative sai yasa samun jini mai Negative yake karanci musamman a lokacin gaggawa wanda hakan yake sanadiyar mutuwar mutane dayawa
Samun lafiyar Mace mai jini 0-Negative a lokacin da take da ciki shine a dinga yi mata Allurar Anti-D (Rhogam). Ita Anti-D ana yin ta ne saboda Anti-bodies din jikin Matarka kar su dinga kaiwa jaririn dake cikinta hari
Babban kalubale na uku shine tsadar Allurar Anti-D, kudinta yana iya kaiwa 100k, 150k ya danganta da Asibitin daka kai Matarka kuma ana yin Allurar sau biyu zuwa sau uku ya danganta da lafiyar Matarka. A lalace zaka ajiye 300k iya kudin Allura
Bawai rashin yarda da kaddara bane kaucewa fadawa cikin wannan hadarin, shi kanshi addini ya karantar da cewa ku kauracewa kanka fadawa cikin matsala ko masifa. Ubangiji Allah ya bamu lafiya da abinda lafiyar zata ci
~ Aliyu Naziru Officer ~
@NigeriaJFP Pls why does it take long before a fellow is been match to a host it's almost a month since I was approved but no organization has been assigned to for interviews yet