Every morning, millions of Nigerians leave their homes to earn a living. I know the burden of transport fares and how much less you have left for your family when you return home. It is a burden I am determined to ease.
We are already seeing encouraging results in at least ten states and the FCT. A journey from Enugu to Nsukka that once cost as high as N4,000 now costs N1,600 on participating CNG buses. There are N50 bus rides in Borno and free CNG bus services in Kaduna. More Nigerians deserve to experience this.
At my invitation, Yutong, the world’s largest bus manufacturer, is establishing a CNG bus assembly plant at the former Leyland automotive plant in Ibadan.
Under an agreement with our Presidential Initiative on CNG and Electric Vehicles (Pi-CNG & EV), Yutong will supply an initial 300 buses for our National Affordable CNG Transit Programme. The first 100 are expected as early as next month. Subsequent buses will be assembled in Ibadan through YP Automobiles, creating jobs for our engineers, technicians and other workers.
I am particularly encouraged by the number of state governments procuring CNG buses in recent weeks. Private investors are expanding our refuelling network, and my earlier directive for 1,000 additional CNG refuelling infrastructure units nationwide will further support this expansion.
In my Reforms to Prosperity Agenda for 2027–2031, I have committed to reducing transport fares by approximately 40% on participating routes. Preparations for delivering on that commitment are already underway.
Nigeria is blessed with abundant natural gas. We must put it to work for the woman going to the market, the young man going to work and the parent struggling with the cost of sending children to school.
We cannot afford to return to the days when fraudulent subsidy claims enriched middlemen while ordinary Nigerians struggled.
I know the sacrifices you have made since we began reforming our economy. I know that what matters to you now is how much better your life becomes.
I want you to spend less getting to work, earn a decent living and return home with enough to give your family a better life.
That is why we are doing this.
Bola Ahmed Tinubu, GCFR
Kowace safiya, miliyoyin 'yan Najeriya na fita daga gidajensu domin neman abin da za su ci. Na san irin nauyin da kuɗin sufuri ke ɗora muku, da yadda hakan ke rage kuɗin da kuke komawa gida da shi domin kula da iyalanku. Wannan nauyi ne da na ƙudiri aniyar sauƙaƙa muku.
Tuni mun fara ganin sakamako mai ƙarfafa gwiwa a aƙalla jihohi goma da Babban Birnin Tarayya, Abuja. A baya, tafiya daga Enugu zuwa Nsukka kan kai Naira 4,000, amma yanzu ana biyan Naira 1,600 kacal a motocin bas masu amfani da CNG da ke cikin shirin. A Borno, ana biyan Naira 50 kacal a wasu motocin bas, yayin da a Kaduna ake samun motocin bas na CNG da ake hawa kyauta. Ya kamata ƙarin 'yan Najeriya su ma su amfana da wannan shiri.
Bisa gayyatata, kamfanin Yutong, wanda shi ne mafi girma a duniya wajen ƙera motocin bas, yana kafa masana'antar haɗa motocin bas masu amfani da CNG a tsohuwar masana'antar motoci ta Leyland da ke Ibadan.
A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka ƙulla da Shirin Shugaban Ƙasa kan Motocin CNG da Lantarki (Pi-CNG & EV), Yutong zai samar da motocin bas 300 a matakin farko domin Shirin Ƙasa na Sufurin CNG Mai Rahusa. Ana sa ran motocin bas 100 na farko za su iso tun a watan Disamba. Sauran motocin kuma za a haɗa su a Ibadan ta hannun kamfanin YP Automobiles. Wannan zai samar da ayyukan yi ga injiniyoyi, ƙwararrun masu sana'o'i da sauran ma'aikata.
Abin da ya fi ƙarfafa min gwiwa shi ne yadda gwamnatocin jihohi da dama suka fara sayen motocin bas na CNG a 'yan makonnin nan. 'Yan kasuwa masu zuba jari kuma na ci gaba da buɗe ƙarin tashoshin cika gas. Umarnin da na bayar tun da farko na samar da ƙarin tashoshin cika gas na CNG guda 1,000 a faɗin ƙasar nan zai ƙara bunƙasa wannan shiri.
A cikin Ajandar Sauye-sauye Zuwa Wadata da na gabatar domin shekarun 2027 zuwa 2031, na yi alƙawarin rage kuɗin sufuri da kusan kashi 40 cikin 100 a hanyoyin da shirin ya shafa. Tuni an fara shirye-shiryen cika wannan alƙawari.
Najeriya tana da albarkatun iskar gas masu yawa. Dole ne mu yi amfani da su domin amfanin mata masu zuwa kasuwa, matasan da ke zuwa wuraren aiki da iyayen da ke kashe kuɗi wajen kai yaransu makaranta.
Ba za mu iya komawa zamanin da tallafin man fetur na bogi ke azurta dillalai ba, yayin da talakawan Najeriya ke shan wahala.
Na san irin sadaukarwar da kuka yi tun lokacin da muka fara gyaran tattalin arzikinmu. Na kuma san cewa abin da ya fi muhimmanci a gare ku yanzu shi ne ganin rayuwarku ta inganta.
Ina so ku rage kuɗin da kuke kashewa wajen zuwa aiki, ku samu abin dogaro da kai, sannan ku koma gida da isasshen abin da zai ba iyalanku damar rayuwa mai inganci.
Shi ya sa muke yin haka.
Bola Ahmed Tinubu, GCFR
#ArewaForAsiwaju
#A4A
You don’t need @hayateey1 to tell you APC will sweep the 2027 polls. The apparent available facts are more than enough for you, you can attest and testify by yourself.
#ArewaForAsiwaju#A4A
"Wannan Shugaban Ƙasa ya share mana hawaye. A baya, an manta da mu. A baya, ana raba muƙamai, amma yankin Kudu maso Gabas ba ya samun wani abin a zo a gani.
Bari in faɗa muku, kaso mai tsoka na ayyukan more rayuwa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa yana nan a Jihar Anambra. Don Allah mu yi wa Shugabanmu tafi!
Ku dubi shahararriyar babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha, wadda ake mayar da ita mai hannu biyu a tsawon kilomita 108 baki ɗaya. Kilomita 100 cif daga cikin wannan hanya ana gina su ne da siminti mai sandunan ƙarfe a kan kuɗi Naira biliyan 150, kuma tuni an kammala kashi 70 cikin 100 na wannan aiki. Sauran ɓangaren da ake yi da kwalta kuwa zai ci wa gwamnatin tarayya Naira biliyan 202. Gaba ɗaya, an kammala sama da kashi 85 cikin 100 na wannan aiki.
Ina batun hanyar kewaye ta Gadar Neja ta Biyu? Tana da tsawon kilomita 35 da gadoji da dama a nan Jihar Anambra, kuma kuɗin aikin ya kai Naira biliyan 175. Lokacin da Gadar Neja ta Farko ta fara ba mu matsala kuwa, nan take Shugaban Ƙasa ya shiga lamarin, cikin makonni biyu kuma aka gyara ta.
Ina batun ayyukan da aka amince da su kwanan nan domin al'ummar Anambra? Tuni an fara matakan bayar da kwangilar titin Oba zuwa Nnewi mai hannu biyu, mai tsawon kilomita 76."
Sanata Dave Umahi, Ministan Ayyuka
#ArewaForAsiwaju
#A4A
Improving rural roads, reducing travel time, boosting local businesses, and making life easier for communities. Real development that impacts lives!
#AbbaIsWorking
Improving rural roads, reducing travel time, boosting local businesses, and making life easier for communities. Real development that impacts lives!
#AbbaIsWorking
Improving rural roads, reducing travel time, boosting local businesses, and making life easier for communities. Real development that impacts lives!
#KanoFirst#AbbaIsWorking
🤍 Toni Rüdiger: “If I play the most matches of my career here at Real Madrid, then I can probably say it’s the club of my life”.
“My situation is good. I’m healthy. I get game time”, told @MarioCortegana on The Athletic.
A ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu, Najeriya ta samu nasara a wani gagarumin aikin ƙwato kadarori wanda hukumar ICPC ta jagoranta. An kai ziyara wurin a jiya.
#ArewaForAsiwaju#A4A
A iya sanina, tuni an riga an san wanda ya ci wannan zaɓe da wanda ya faɗi. Shugaba Tinubu ba ya buƙatar yin maguɗi a kowane zaɓe. A yau, a ko'ina a faɗin ƙasar nan, a kowace jiha ta Najeriya, fafatawa ce tsakanin Shugaba Tinubu da wata jam'iyya guda ɗaya, yayin da akwai wasu 'yan takara da ke da ƙarfi a wasu sassan ƙasar, amma a wasu sassan kuwa ba a ma san da zamansu ba.
Farfesa Charles Soludo, Gwamnan Jihar Anambra, a yau a wurin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a Jihar Anambra.
#ArewaforAsiwaju #A4A