SHIN KANA SON SAMUN LADAN AIKIN HAJJI DA UMRAH ???
Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Wanda ya yi Sallar Asubahi a cikin jamʼi, sannan ya zauna yana ambaton Allah har rana ta ɓullo, sannan ya sallaci raka'o'i guda biyu, za su kasance masa kamar ladan wanda ya yi aikin Hajji da Umrah cikakke, cikakke.”
~ Sunan Tirmizy, Hadith na 586, Albany ya inganta shi
Wannan garaɓasa ce maigirma ga waɗanda basu samu damar halartar Aikin Hajji da Umrah ba, kana daga cikin gidanka idan ka aikata abinda aka umurceka da aikatawa za ka samu wannan lada mai girma idan Allah ya yarda, kuma domin a tabbatar maka da samun wannan lada idan ka aikata Annabi (ﷺ) ya ce: Cikakke-cikakke, kenan ba tare da an tauye maka komai ba daga ladan da za a bawa Mai Aikin Hajji ko Umrah.
Don haka ga duk mai son wannan garaɓasar to sai ya lizimci Sallar Asubahi a lokacinta sannan ya ƙauracewa baccin safe, a lura cewa mafiya albarka na sauka ne a daidai irin wannan lokacin, shi yasa ma wasu suke ganin laifi ne yin baccin safe, a'a babu laifi amma duk mai buƙatar ire-iren waɗannan garaɓasa sai ya ƙauracewa baccin safe. Allah ya sa mu dace, Ameen!
- Dr Kabir Asgar
“Indeed, with hardship comes ease.”
— (Qur’an 94:6)
May this remind you today that every difficulty you face carries within it relief and blessing from Allah 🤲