Jimillar buƙatu da shahidin jagoran mu ya bayyana, tare da abubuwan da na ambata a cikin saƙona na 7 ga Tir, 1405, su ne za su zama jagora wajen kawo sauyi, bunƙasa, da kuma kaiwa ga inda ake so a Bangaren Shari'a.
#Iran#MojtabaKhamenei#Khamenei
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai
Mai girma Hujjatul-Islam wal-Muslimin Alhaji Mohseni,
Ina miƙa godiyata bisa ƙoƙarinku masu amfani da kuma inganci. Ina sake naɗa ku a matsayin Shugaban Bangaren Shari'a.
#Iran#MojtabaKhamenei#Khamenei
Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a cikin wani hukunci da ya fitar, ya sake naɗa Hujjatul-Islam wal-Muslimin Mohseni Ejei a matsayin Shugaban Bangaren Shari'a.
#Iran#MojtabaKhamenei#Khamenei
📷An gudanar da taron ne a Makarantar Farhang da ke Tehran, tare da halartar Dr. Gholam-Ali Haddad Adel, iyalanta, da kuma wani adadi na abokan aikinta da ƙawayenta.
🏴#DoleMuTashiTsaye#ShahidKhamenei#Khamenei
📷 An gudanar da bikin bankwana da Malama Shahida Zahra Haddad Adel, mata kuma uwargida ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a daren jiya Laraba, 1 ga Yuli, 2026 .
🏴#DoleMuTashiTsaye#ShahidKhamenei#Khamenei
Hanyar isa ga adalci da yaki da zalunci da cin hanci da rashawa hanya ce mai wahala, wadda za ta sauƙaƙa ne ta hanyar himma da ƙuduri mai ƙarfi, ƙwazo da ƙarin ƙoƙari, jarumta da tsayawa tsayin daka,
Bincike da hukunta laifukan da aka aikata a kallafaffen Yaƙi na Biyu, da faɗaɗa wannan bincike zuwa Kallafaffen Yaƙi na Uku, tare da ci gaba da bibiyar lamarin har sai an kai ga yanke hukunci, sannan a mika aiwatar da hukuncin ga waɗanda suka cancanta…
Tabbas, furucin da wasu shugabannin makiya na Amurka da sahayoniya suka yi, da alfahari da suka nuna game da waɗannan laifuka, ana ɗaukarsa a matsayin shaidar aikata laifi kai tsaye, kuma yana zama ginshiƙi wajen samar da matakan ƙwato haƙƙin da aka tauye na al’ummar [Iran].
kowane ɗaya daga cikin waɗannan shari’a ne mai zaman kansa da kuma muhimmanci, waɗanda wajibi ne a bi diddiginsa da cikakken ƙwazo a kotunan cikin gida da na ƙasa da ƙasa.
Kisan jarirai masu kwanaki kaɗan har zuwa manyan tsofaffi masu daraja; kuma mafi girman su duka, shahadar wannan fitaccen mutum, lu’u-lu’u na musamman kuma wanda ba shi da tamka a zamaninsa, babban jagora, mujahidi —
Raunukan jiki da na ruhi da suka samu kowane ɗan ƙasar Iran sakamakon kallafaffen Yaƙi na Biyu da na Uku, kashe yara, laifukan yaƙi da aka aikata a Minab da Lamerd, har da hare-haren da aka kai kan cibiyoyin kiwon lafiya—
Daya daga cikin muhimman batutuwan shari'a da suka shafi daukacin al'ummar Iran a wannan lokaci shi ne bibiya da ƙwato haƙƙoƙin da aka tauye musu sakamakon laifuffukan da masu aikata manyan laifukan ƙasa da ƙasa, masu girman kai na Duniya,
Ya zama wajibi bangaren shari'a ya kai ga wani matsayi na tabbatar da adalci da duk wanda aka zalunta zai ɗauke shi a matsayin mafakarsa kuma wurin neman hakkinsa.