Top Tweets for #YaseenaTech
Juma’a Mubarak 🤲 $TAO tare da https://t.co/ym73EVvYIA dandalin da ke sauƙaƙa maka gano al amuran whales da wallet movement $TAO yana ci gaba da kafa matsayi a fannin AI + Blockchain kuma tare da @inspectxyz zaka iya Ilmi + Ladabtarwa Nasara a crypto
#TAO #ACC #Yaseenatech

Alhamdulillah 🙏
Yau Founder na ACC, @KB_CRIPTO ya yi min follow back Abin alfahari ne kuma zai ƙara min ƙwarin guiwa wajen yada ilimin Blockchain & Crypto a Hausa 🚀💚 @acc_community
Alkairi ce
#CryptoHausa #ACC #YaseenaTech

Juma’a Mubarak 🤲
$TAO da https://t.co/ym73EVvqT2 kayan aiki na masu crypto domin bincike da nazari kan kasuwa cikin sauƙi📊
🚀 $TAO yana ci gaba da jan hankali a kasuwar AI + Blockchain kuma @inspectxyz yana taimaka wa traders
#TAO #InspectXYZ #ACC #Yaseenatech #Blockchain

🚀 $TAO (Substrike) Price Update
Farashin $TAO yanzu ya kai $337 🔥 @inspectxyz
Network ɗin AI + Blockchain yana ci gaba da ƙarfafawa
📊 Ku kasance masu lura da motsin farashi damar shiga tana nan yanzu
#TAO #Substrike #CryptoHausa #Blockchain #ACC #Yaseenatech

Substrike yana ci gaba da jan hankali a kasuwar crypto tare da sabbin abubuwan da suke kawo wa ecosystem ɗin AI. 🔥
📊 Ku ci gaba da bibiyar farashi da al'amuran network ɗin domin samun damar shiga tun da wuri 🚀 $TAO @inspectxyz
#TAO #Substrike #Blockchain #ACC #Yaseenatech

📊 Idan kana son ci gaba da kasancewa a gaba a fagen crypto, https://t.co/ym73EVvqT2 na baka damar duba:
✅ Chart analysis mai sauƙi
✅ Whale alerts
✅ Trading signals da metrics
@inspectxyz
#YaseenaTech #Blockchain #TAO #InspectXYZ #ACC

Muna haɗa matasan Arewa domin koyon ilimin Crypto Blockchain cikin harshen Hausa
Tare da #ACC zaka samu
✅ Ilimin asali kan Blockchain
✅ Hanyoyin samun damar Crypto
✅ Koyon tsaro da fasaha na zamani
Ilmi shi ne ginshiƙin ci gaban al,umma muna tare da @inspectxyz #YaseenaTech

🕌 Juma’a Mubarak! 🌙
Allah ya albarkace rayuwarmu da rahama da nasara a duniya da lahira.
Mu ci gaba da neman ilimi da gaskiya a duk inda muka tsinci kanmu.
Kuma ka ce: Ya Ubangijina Ka ƙara mini ilimi.
#JumaMubarak #CryptoHausa #Blockchain #YaseenaTech #ACC
📸 @YaseenaTech

Happy Bitcoin Pizza Day
🍕A ranar 22 ga Mayu 2010 wani mutum ya sayi pizza guda 2 da 10,000 BTC
Wannan shine farkon amfani da Bitcoin a matsayin kudin kasuwanci
Yau muna tunawa da wannan tarihi daga pizza zuwa duniya mai cike da dama
#CryptoHausa #Blockchain #YaseenaTech #ACC

Kana da ilimi a crypto ko blockchain
Kada ka ɓoye
Rubuta a harshenka – Hausa ma tana da wurinta.
@GiveRep yana nan yana sauraronka.
Let’s educate. Let’s earn. Let’s @GiveRep
#CryptoHausa #YaseenaTech #ACC #GiveRep @acc_community

I’m proud to be part of the @GiveRep movement ⚡
Contributing in Hausa. Earning in Rep. Let’s empower creators
Let’s build for the people who engage
#GiveRep #YaseenaTech #CryptoHausa #ACC
Proudly repping @GiveRep

Hanyoyi Don Kaucewa Asarar Kuɗi a Crypto
@YaseenaTech | ACC
#CryptoHausa #YaseenaTech #ACC #BlockchainTips
1/7
A kasuwar crypto, mutane da yawa suna rasa kuɗi saboda rashin tsari da ilimi.
Ga muhimman hanyoyi da za su taimaka maka k kaucewa asara
📉❌💸
2/7 – Yi Karatu da Nazari
📚🔍
Kafin ka saka kuɗi a wani token ko project, ka yi bincike
Karanta whitepaper, duba website da community ɗin project ɗin
3/7 – Guji FOMO (Tsoron a bar ka a baya
🚫😱📈
Kar ka bi shaharar mutane kawai.
FOMO na janyo ka zuba kudi a wuraren da babu tushe.
4/7 – Yi Amfani da Stop-Loss
🛑📉
A trading, amfani da stop-loss yana taimaka maka ka rage asara idan farashin ya fadi kwatsam.
5/7 – Kada Ka Saka Dukkan Kuɗinka
💰⚖️
Ka saka abinda zaka iya rasawa ba tare da ya dame ka ba.
Kar ka zuba dukiya gaba ɗaya.
6/7 – Rike N Tsawon Lokaci (HODL)
⏳🚀
Idan ka zabi token mai kyau, rike shi.
Kada ka sayar da wuri saboda tsoro ko ƙarancin hakuri.
7/7 – Tabbatar da Tsaro
🔐🦊
Guji ajiye kuɗinka a exchange kaɗai.
Yi amfani da wallets masu zaman kansu kamar MetaMask ko Trust Wallet.
Follow @YaseenaTech @acc_community don ƙarin ilimi a blockchain cikin harshen Hausa
Let's @GiveRep
#CryptoHausa #YaseenaTech #ACC #BlockchainTips #FinancialLiteracy #Web3Hausa

Menene Blockchain da Me Yasa Yake Da Muhimmanci saboda #YaseenaTech #ACC
Blockchain ba kawai fasaha bace revolushin ne a tsarin amana da gaskiya
Ga wasu zurfin fahimta
1. Blockchain = Lissafin Tarihi Mai Gaskiya
Duk wani abu da aka rubuta a cikinsa ba za a iya gogewa ko canzawa ba.
2. Blocks + Chain = Tushen Tsari
Ana haɗa bayanai a cikin blocks sannan a ɗaure su da juna ta hanyar lamba ta musamman (hash).
3. Decentralized = Babu Shugaba Ɗaya
Babu wata hukuma guda da ke iko da bayanai. Ana raba iko tsakanin nodes daban-daban.
4. Transparency = Kowa na iya dubawa
Bayanai a blockchain a bude suke. Duk mai intanet na iya gani.
5. Consensus = Amincewa Tare
Kafin a ƙara sabbin bayanai, dole duk masu amfani su amince hakan yana hana yaudara.
A duniyar crypto, idan baka da tsaro, dukiyarka tana cikin haɗari. Ga wasu mahimman matakai da za ka dauka:
1. Kada ka taɓa ba kowa Private Key ko Recovery Phrase.
2. Yi amfani da 2FA a duk wallet da exchange ɗinka
3. Ka tabbata kana amfani da official apps kawai — kaucewa download daga shafukan da ba a yarda da su ba.
4. Kada ka yarda da DM ko reply da suna baka tallafi (support) yawanci scammers ne.
5. Yi amfani da hardware wallet idan kana da kudi masu yawa
Tambaya
Wanne daga cikin waɗannan ka fi fahimta Ko kana da tambaya a kai
Just us 😸 😊
@GiveRep
#CryptoEducation #Web3Africa #Blockchain101 #YaseenaTech #ArewaCryptoCommunity @Abdulhadi021 @acc_community @KB_CRIPTO #CryptoSecurity

Me Yasa $Sei Blockchain Ya Banbanta @SeiNetwork 🔴
#SeiNetwork #CryptoHausa #YaseenaTech #ACC
Shin ka san cewa $Sei blockchain yana da sauri fiye da yadda kake tunani
Ga dalilin da yasa $Sei ke ɗaukar hankalin duniya
⚡ Super Fast Finality – kasa da 500ms
🛡️ MEV Protection – Kare users daga cin hanci a blockchain
🔁 Parallel Execution – Ayyuka da dama suna tafiya lokaci ɗaya
$Sei yana da dama sosai ga devs da kuma non-devs masu son gina ko yin aiki a Web3.
Ka biyo mu don koyon yadda zaka ci gajiyar $Sei 🔴
#CryptoEducation #ACC #BlockchainNaHausa #Web3Africa #YaseenaTech #ArewaCryptoCommunity #SeiEcosystem @acc_community

Yadda Ake Tabbatar da Gaskiyar Bayanai a Blockchain
#CryptoHausa #Blockchain #YaseenaTech #ACC
A Blockchain, babu banki ko hukuma da ke tabbatar da gaskiya.
To, yaya ake sanin gaskiya
Ana amfani da Consensus Mechanism wanda ke tabbatar da
Duk nodes sun yarda da sabbin bayanai
An bi ƙa'ida kafin ƙara block
Ba za a iya canza tarihi ba
Misalai na Consensus:
1. Proof of Work
2. Proof of Stake
3. Delegated Proof of Stake
Consensus shine zuciyar amintaccen blockchain.
Babu shi, ba za a iya dogaro da bayanai ba follow @YaseenaTech
And @acc_community
#CryptoHausa #Blockchain #Consensus #YaseenaTech #ArewaCryptoCommunity #Web3Nigeria #CryptoEducation #BlockchainNaHausa #CryptoAfrica #SeiNetwork

Litinin mai albarka 💯🪙
Ka sani: A blockchain, kowace mu’amala ana adanata cikin tsarin da ba za a iya gogewa ko sauyawa ba. Wannan yana ƙara gaskiya da tsaro a harkokin mu na yau da kullum. Mu ci gaba da karatu domin mu zama kwararru 📌👌 #YaseenaTech #BlockchainHausa #CryptoHausa #Arewacrypto #MondayMotivation #ACC #CryptoEducation @KB_CRIPTO

COIN vs TOKEN a Duniya Crypto [Hausa Thread🧵
Assalamu Alaikum yan uwa
A yau zamu fahimci bambanci tsakanin COINS da TOKENS a cikin duniya Crypto
Ka karanta har ƙarshe domin karin fahimta
#CryptoHausa #Blockchain #YaseenaTech #ACC
1. Mecece COIN? ⚡
Coin crypto ce da ke da nata blockchain.
Ana amfani da Coins wajen:
Musayar kudi (Payments)
Adana daraja (Store of Value)
Lissafi da kididdiga (Unit of Account)
Misalai: Bitcoin (BTC) ₿, Ethereum (ETH) Ξ, Dogecoin (DOGE) Ð.
2. Yaya ake ƙirƙirar Coin? ⛏️
Ana mining ta hanyar kwamfutoci (solving puzzles).
Wannan yana sa blockchain ɗin su kasance:
🛡️ Mai tsaro
⚖️ Decentralized (ba wanda ya mallake su)
3. Nau'o'in Coins:
Native Coins: BTC, ETH, LTC
Forked Coins: BCH, ETC
Wrapped Coins: WBTC, WETH
Stablecoins: USDT, USDC
4. Mecece TOKEN? 🪙
Token crypto ce da bata da nata blockchain.
Ana ginawa akan blockchains irin su Ethereum, BNB Chain, Solana.
Misalai:
USDT (Tether)
UNI (Uniswap)
AAVE (Aave)
5. Amfanin Tokens: ⚙️
Biyan kudi (Payments)
Amfani a cikin dApps (decentralized applications)
Gudanarwa (Governance voting)
Samun damar shiga sabis (Access)
6. Nau'o'in Tokens:
Utility Tokens 🔧 (LINK, UNI)
Security Tokens 🏦 (Asset-backed tokens)
Governance Tokens 🗳️ (AAVE)
Stable Tokens ⚖️ (USDT, USDC)
7. Babban Bambanci a Saukake:
Coin ⚡
Yana da nashi blockchain
Mining/validation
Misali BTC, ETH DOGE
TOKEN 🪙
Bai da nashi blockchain smart contract creation
Misali USDT, UNI, AAVE
Kammalawa: ✨
> Coin = kamar gonar da kake da ita da kanka
Token = kamar shinkafar da ka noma a gonar wani
Idan ka koyi wani abu daga wannan thread, kayi commenting!
Kuma kada ka manta: Follow @YaseenaTech domin karin ilimi akan Crypto da Blockchain a harshen Hausa
#CryptoHausa #Blockchain #ACC #YaseenaTech @acc_community
@devameer0 @fuchaweb3 @KB_CRIPTO @S_M_Danpullo

$PAWS: Shin Wannan Airdrop Ya Yi Mana Adalci?
#CryptoHausa #Blockchain #ACC #YaseenaTech
1. A iya nazarin da nayi, gaskiya bana tunanin cewa $PAWS za su yi abinda ya dace nan gaba. Mun sha mining sosai, amma abubuwan da nake gani yanzu basu kwantar da hankali ba.
2. Idan muka duba irin tokens da muka yi mining a baya — kamar $NOT, $DOGS, da $CATI — sun nuna muhimmanci da kulawa da community. Sun tsara FDV yadda ya dace, hakan yasa muka amfana.
3. Amma $PAWS ba su nuna irin wannan kulawa ba. Farashin ya fara da ƙasa sosai, babu cikakken bayani a kan roadmap, team, ko vision ɗin su. Wannan abu ne mai tayar da hankali.
4. Community shine ginshiƙin kowane token mai makoma. Idan project bai girmama wanda suka yi mining ba, to me ya rage?
5. Darasi ga masu mining airdrops: Kada kawai mu karɓi duk wani token saboda yana kyauta. Mu duba:
Tokenomics
Project roadmap
FDV
Kula da community
6. Mu zama masu nazari, ba kawai masu jira ba. A crypto, ka iya mining kyauta, amma idan babu daraja, sai dai ka yi aikin banza.
@YaseenaTech @GOTPAWSED
#CryptoHausa #PAWS #ACC #Notcoin #Dogs #Mining #Blockchain @EngineerAdam123

YADDA NA SAMU $PAWS TOKEN TA MINI APP NA TELEGRAM – DA YADDA ZAI SHIGA KASUWA GOBE
#CryptoHausa #Blockchain #YaseenaTech #ACC
1. A kwanakin baya, na shiga wani sabon tsarin crypto a Telegram mai suna PAWS mini app, inda muka rika cika wasu ayyuka don samun maki. Wannan shine mining a web3 way
2. A bisa yawan maki da na tara, yau aka turo min token ɗin $PAWS guda 2,835 kai tsaye a cikin wallet ɗina na Bitget. Wannan yana nuni da cewa ka iya samun crypto ba tare da zuba kuɗi ba
3. Gobe Laraba, 16 Afrilu, za a fara kasuwancin $PAWS a manyan kasuwanni. Wannan yana nufin zan iya sayarwa ko riƙewa gwargwadon dabarata.
4. $PAWS yanzu yana kan Solana blockchain – wato ana samun sa da sauri, ba tare da biyan kudade masu yawa ba. Wannan babban ci gaba ne ga project ɗin.
5. Shawarata ga masu bibiyar crypto:
Ku koyi amfani da mini apps
Ku bude wallets kamar Phantom.
Ku shiga airdrops da tasks don fara crypto ba tare da jari ba.
6. Ni kuma, ina ci gaba da ilmantar da jama’a a harshen Hausa ta hanyar @YaseenaTech karkashin Arewa Crypto Community (ACC).
7. Idan kuna so ku koyi yadda crypto ke aiki cikin sauki da Hausa, kubi @acc_community yanzu. Wannan sabon zamani ne, kuma dole mu kasance a ciki!
#CryptoHausa #PAWS #Solana #Blockchain #YaseenaTech #ACC #Web3 #Bitget

Juma’a Mubarak
A yau, bari mu tuna: Blockchain ba hanya bace ta kudi kawai, hanya ce ta gaskiya da tsaro wajen mu’amala.
Yana taimaka wajen rage damfara da karfafa amana a duniya ta dijital. @acc_community
Mu ci gaba da koyon blockchain domin samun damar gobe
#YaseenaTech #ArewaCrypto #BlockchainHausa #CryptoHausa #Jumaat #ACC

Trends for you
Most Popular Users

Elon Musk 
@elonmusk
240.9M followers

Barack Obama 
@barackobama
118.8M followers

Cristiano Ronaldo 
@cristiano
114.5M followers

Donald J. Trump 
@realdonaldtrump
111.9M followers

Narendra Modi 
@narendramodi
107M followers

Rihanna 
@rihanna
98.7M followers

NASA 
@nasa
92.2M followers

Justin Bieber 
@justinbieber
91.8M followers

KATY PERRY 
@katyperry
90M followers

Taylor Swift 
@taylorswift13
84M followers

Lady Gaga 
@ladygaga
75.5M followers

Virat Kohli 
@imvkohli
73.4M followers

Kim Kardashian 
@kimkardashian
70.8M followers

YouTube 
@youtube
68.7M followers

Neymar Jr 
@neymarjr
66.4M followers

Bill Gates 
@billgates
65.2M followers

Selena Gomez 
@selenagomez
63.1M followers

The Ellen Show
@theellenshow
62.2M followers

CNN 
@cnn
61.7M followers

X 
@x
60.6M followers
