🚀 Yadda 𝕏 (Twitter) Zai Canza Maka Rayuwa: Hanyar Samun Kuɗi! 💰
Kada ka tsaya kallon ruwa kawai, kaima zaka iya zama cikin waɗanda ake biya a kowane wata a kafar 𝕏. Idan kana son gina account mai daraja da kawo kudi, ga matakan da zaka bi:
🔹 1. Cika Sharuddan Monetization: Tabbatar kana da asusun 𝕏 Premium (Blue Tick), mabiya (Followers) akalla 500, da kuma samun kallo (Impressions) akalla miliyan 5 a cikin watanni 3.
🔹 2. Gina Ingantaccen Suna (Quality Content): Kar ka zama mai tura komai da ruwanka. Mayar da hankali kan abubuwa masu amfani, fadakarwa, ko nishadi a kullum.
🔹 3. Neman Mabiya na Kwarai: Ka mayar da hankali wajen samun Active Followers. Mu'amala da mutane (Engagement) ita ce sarki; tattaunawa da wasu yana sa account dinka girma.
🔹 4. Darajar Masu Blue Tick: Ka sani cewa engagement (kamar Like, Reply, da Repost) daga mutanen da suke da Verified Accounts shi ne ke sa a biya ka kudi mai tsoka.
Haske: Istiqama da jajircewa su ne sirrin nasara. 𝕏 ba hira ba ce kawai, sana'a ce!
Allah ya bada sa’a, Yasa muna da Rabo. 🤲🏽✨
#XMonetization #ArewaTech #HanyarKudi #XGuide